- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1010–970 BC
The Reign of David
David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Sama’ila 15:34kusan 1021 K.H.
Amma in ka koma birni, ka gaya wa Absalom, ‘Zan zama bawanka, ya sarki; dā ni bawan mahaifinka ne, amma yanzu zan zama bawanka,’ ta haka za ka watsar da shawarar Ahitofel.
- 2 Sama’ila 15:35kusan 1021 K.H.
Ba Zadok da Abiyatar firistocin nan suna nan tare da kai ba? Ka gaya musu duk abin da ka ji a fadan sarki.
- 2 Sama’ila 15:36kusan 1021 K.H.
’Ya’yansu biyu maza, Ahimawaz ɗan Zadok, da kuma Yonatan ɗan Abiyatar, suna can tare da su. Ka aike su wurina da duk abin da ka ji.”
- 2 Sama’ila 15:37kusan 1021 K.H.
Saboda haka Hushai abokin Dawuda ya isa Urushalima yayinda Absalom yake shigowa birnin.
- 2 Sama’ila 16:1kusan 1023 K.H.
Sa’ad da Dawuda ya yi ɗan nesa da ƙwanƙolin, sai ga Ziba mai hidimar Mefiboshet, yana jira yă tarye shi. Yana da jerin jakuna da sirdi suna ɗauke da dunƙulen burodi ɗari biyu, da ƙosai busasshen inabi ɗari ɗaya, da kosan ’ya’yan itace ɓaure guda ɗari, da salka ruwan inabi.
- 2 Sama’ila 16:2kusan 1023 K.H.
Sarki ya ce wa Ziba, “Me ya sa ka kawo waɗannan?” Ziba ya ce, “Jakuna domin iyalin gidan sarki su hau ne, burodi da ’ya’yan itace domin mutane su ci, ruwan inabi kuma domin waɗanda suka gaji a hamada.”
- 2 Sama’ila 16:3kusan 1023 K.H.
Sai sarki ya ce, “Ina jikar maigidanka?” Ziba ya ce, “Yana zaune a Urushalima gama yana tsammani cewa, ‘Yau gidan Isra’ila za su mayar mini da sarautar kakana.’ ”
- 2 Sama’ila 16:4kusan 1023 K.H.
Sai sarki ya ce wa Ziba, “Duk abin da yake na Mefiboshet, ya zama naka.” Ziba ya rusuna ya ce, “Bari in dinga samun tagomashi a gabanka ranka yă daɗe.”
- 2 Sama’ila 16:5kusan 1023 K.H.
Yayinda Sarki Dawuda ya kusato Bahurim, sai ga wani mutumin dangin Shawulu ya fito daga can, sunansa Shimeyi ɗan Gera. Ya fito yana ta la’anta yayinda yake fitowa.
- 2 Sama’ila 16:6kusan 1023 K.H.
Ya jajjefi Dawuda da dukan fadawan sarki da duwatsu, ko da yake sojoji da masu gadin sarki na musamman suna kewaye da sarki dama da hagu.
- 2 Sama’ila 16:7kusan 1023 K.H.
Yayinda yake la’antar, Shimeyi ya ce, “Tafi daga nan, tafi daga nan, mai kisankai, mutumin banza kawai!
- 2 Sama’ila 16:8kusan 1023 K.H.
Ubangiji ya kama ka saboda alhakin jinin gidan Shawulu, wanda kake sarauta a maimakonsa. Ubangiji ya ba da masarautar ga ɗanka Absalom. Hallaka ta zo maka domin kai mai kisankai ne!”
- 2 Sama’ila 16:9kusan 1023 K.H.
Sai Abishai ɗan Zeruhiya ya ce wa sarki, “Ranka yă daɗe, don me wannan mataccen kare yake la’antarka? Bari in je in datse kansa.”
- 2 Sama’ila 16:10kusan 1023 K.H.
Amma sarki ya ce, “Ba ruwana da ku, ku ’ya’yan Zeruhiya. Idan yana la’ana ne domin Ubangiji ya ce masa, ‘La’anci Dawuda,’ wa zai ce, ‘Don me kake haka?’ ”
- 2 Sama’ila 16:11kusan 1023 K.H.
Sa’an nan Dawuda ya ce wa Abishai da dukan fadawansa, “Ɗana, na cikina, yana ƙoƙari yă kashe ni. Balle wannan mutumin Benyamin! Ku ƙyale shi, yă yi ta zargi, Ubangiji ne ya ce masa yă yi haka.
- 2 Sama’ila 16:12kusan 1023 K.H.
Mai yiwuwa Ubangiji yă ga azabata, yă sāka mini da alheri saboda la’anar da nake sha a yau.”
- 2 Sama’ila 16:13kusan 1023 K.H.
Saboda haka Dawuda da mutanensa suka ci gaba da tafiyarsu yayinda Shimeyi yana tafiya ɗaura da shi a gefen tudu, yana zagi, yana jifansa da duwatsu, yana tayar masa da ƙura.
- 2 Sama’ila 16:14kusan 1023 K.H.
Sarki da dukan mutanen da suke tare da shi suka isa masauƙinsu a gajiye. A can fa ya huta.
- 2 Sama’ila 16:15kusan 1023 K.H.
Ana cikin haka, Absalom da dukan Isra’ila suka iso Urushalima, Ahitofel kuwa yana tare da shi.
- 2 Sama’ila 16:16kusan 1023 K.H.
Sai Hushai mutumin Arkitawa, abokin Dawuda ya je wurin Absalom ya ce masa, “Ran sarki yă daɗe! Ran sarki yă daɗe!”
- 2 Sama’ila 16:17kusan 1023 K.H.
Absalom ya ce wa Hushai, “Ƙaunar da kake nuna wa abokinka ke nan? Me ya sa ba ka tafi tare da abokinka ba?”
- 2 Sama’ila 16:18kusan 1023 K.H.
Hushai ya ce wa Absalom, “A’a, ai, wanda Ubangiji ya zaɓa ta wurin waɗannan mutane, da kuma ta wurin dukan mutane Isra’ila, shi zan zama nasa, zan kuma kasance tare da shi.
- 2 Sama’ila 16:19kusan 1023 K.H.
Ban da haka ma, wane ne zan bauta wa? Ashe, ba ɗan ne zan bauta wa ba? Kamar dai yadda na bauta wa mahaifinka, haka zan bauta maka.”
- 2 Sama’ila 16:20kusan 1023 K.H.
Absalom ya ce wa Ahitofel, “Ba mu shawararka. Me za mu yi?”
- 2 Sama’ila 16:21kusan 1023 K.H.
Ahitofel ya ce wa Absalom, “Je ka kwana da ƙwarƙwaran mahaifinka waɗanda ya bari su lura da fada. Ta haka dukan Isra’ila za su ji cewa ka mai da kanka abin wari a hancin mahaifinka, dukan hannuwan waɗanda suke tare da kai kuwa za su sami ƙarfi.”