- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1010–970 BC
The Reign of David
David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Sama’ila 14:17kusan 1027 K.H.
“Yanzu kuwa baiwarka tana cewa, ‘Bari magana ranka yă daɗe sarki yă ba ni hutu, gama ranka yă daɗe sarki yana kama da mala’ikan Allah cikin rarrabe nagarta da mugunta. Bari Ubangiji Allahnka yă kasance tare da kai.’ ”
- 2 Sama’ila 14:18kusan 1027 K.H.
Sai sarki ya ce wa matar, “Kada ki ɓoye mini kome daga abin da zan tambaye ki.” Matar ta ce, “Bari ranka yă daɗe sarki yă yi tambaya.”
- 2 Sama’ila 14:19kusan 1027 K.H.
Sarki ya ce, “Anya, babu hannun Yowab a cikin dukan wannan?” Matar ta ce, “Muddin kana a raye, ranka yă daɗe sarki, ba wanda zai juya dama ko hagu daga wani abin da ranka yă daɗe sarki ya faɗa. I, bawanka Yowab ne ya umarce ni in yi wannan, shi ne kuma ya sa kalmomin nan a bakin baiwarka.
- 2 Sama’ila 14:20kusan 1027 K.H.
Bawanka Yowab ne ya yi haka don yă daidaita al’amura. Ranka yă daɗe yana da hikima iri ta mala’ikan Allah, ya san dukan kome da yake faruwa a ƙasar.”
- 2 Sama’ila 14:21kusan 1027 K.H.
Sarki ya ce wa Yowab, “To, da kyau, zan yi haka. Je ka, ka dawo da saurayin nan Absalom.”
- 2 Sama’ila 14:22kusan 1027 K.H.
Yowab ya rusuna har ƙasa don bangirma, ya kuma yi wa sarki kyakkyawar fata. Yowab ya ce, “Yau, bawanka ya sani ya sami tagomashi a gare ka, ranka yă daɗe sarki, gama sarki ya ji roƙon bawansa.”
- 2 Sama’ila 14:23kusan 1027 K.H.
Sa’an nan Yowab ya tafi Geshur ya dawo da Absalom Urushalima.
- 2 Sama’ila 14:24kusan 1027 K.H.
Amma sarki ya ce, “Yă tafi gidansa; kada yă zo yă gan ni.” Saboda haka Absalom ya tafi gidansa, bai kuwa je ganin sarki ba.
- 2 Sama’ila 14:25kusan 1027 K.H.
A cikin dukan Isra’ila babu wanda ake yabon kyansa kamar Absalom. Tun daga kansa har zuwa tafin ƙafansa babu tabo a jikinsa.
- 2 Sama’ila 14:26kusan 1027 K.H.
A duk sa’ad da ya aske gashin kansa (yakan aske kansa lokaci-lokaci sa’ad da ya yi masa nauyi) yakan auna shi, nauyin gashin kuwa yakan kai wajen shekel ɗari biyu a ma’aunin da ake awo.
- 2 Sama’ila 14:27kusan 1027 K.H.
Aka haifa wa Absalom ’ya’ya uku maza da ’ya mace guda. Sunanta Tamar, ta kuwa zama kyakkyawan mace ƙwarai.
- 2 Sama’ila 14:28kusan 1027 K.H.
Absalom ya zauna a Urushalima shekara biyu amma ba tare da ganin fuskar sarki ba.
- 2 Sama’ila 14:29kusan 1027 K.H.
Sai Absalom ya aika a kira masa Yowab don yă aike shi wurin sarki, amma Yowab ya ƙi zuwa. Saboda haka ya sāke aika sau na biyu, amma ya ƙi yă zo.
- 2 Sama’ila 14:30kusan 1027 K.H.
Sai ya ce wa bayinsa, “Duba, gonar Yowab tana gab da tawa, kuma yana da sha’ir a can. Ku je ku sa mata wuta.” Sai bayin Absalom suka sa wa gonar wuta.
- 2 Sama’ila 14:31kusan 1027 K.H.
Sa’an nan Yowab ya tafi gidan Absalom ya ce masa, “Me ya sa bayinka suka sa wa gonata wuta?”
- 2 Sama’ila 14:32kusan 1027 K.H.
Absalom ya ce wa Yowab, “Kai, na aika, ‘Ka zo nan don in aike ka wurin sarki ka tambaya, “Me ya sa na dawo daga Geshur? Ai, ya fi mini a ce ina can har yanzu!” ’ Yanzu kuwa, ina so in ga sarki, kuma idan na yi wani laifi, to, yă kashe ni.”
- 2 Sama’ila 14:33kusan 1025 K.H.
Saboda haka Yowab ya tafi wurin sarki ya gaya masa wannan. Sai sarki ya aika aka zo da Absalom, ya kuma rusuna da fuskarsa har ƙasa a gaban sarki. Sarki kuwa ya sumbaci Absalom.
- 2 Sama’ila 15:1kusan 1024 K.H.
Ana nan sai Absalom ya samo wa kansa wata keken yaƙi da dawakai tare da mutum hamsin da za su sha gabansa.
- 2 Sama’ila 15:2kusan 1024 K.H.
Absalom yakan tashi da sassafe yă tsaya a gefen hanyar shigar ƙofar birni. Duk sa’ad da wani ya zo da ƙara don a kai gaban sarki yă yi shari’a, Absalom yakan kira shi yă ce, “Daga wane gari ka fito?” Sai mutumin yă amsa yă ce, “Bawanka ya fito a ɗaya daga cikin kabilan Isra’ila.”
- 2 Sama’ila 15:3kusan 1024 K.H.
Sai Absalom yă ce masa, “Ga shi, ƙararka daidai ne, tana kuma da gaskiya, sai dai ba wakilin sarkin da zai ji ka.”
- 2 Sama’ila 15:4kusan 1024 K.H.
Absalom kuwa yakan ƙara da cewa, “Da a ce an naɗa ni alƙali a ƙasar mana! Da duk mai ƙara, ko kuka wanda zai zo wurina, zan in tabbatar an yi masa adalci.”
- 2 Sama’ila 15:5kusan 1024 K.H.
Kuma duk sa’ad da wani ya zo wurin Absalom ya rusuna don yă gaishe shi, sai Absalom yă sa hannunsa yă ta da shi, yă kuma rungume shi.
- 2 Sama’ila 15:6kusan 1024 K.H.
Absalom ya yi ta yin haka ga dukan Isra’ilawan da suka zo wurin sarki don neman adalci, ta haka kuwa ya saci zukatan mutanen Isra’ila.
- 2 Sama’ila 15:7kusan 1021 K.H.
A ƙarshen shekara huɗu, Absalom ya ce wa sarki, “Bari in tafi Hebron in cika alkawarin da na yi wa Ubangiji.
- 2 Sama’ila 15:8kusan 1021 K.H.
Yayinda bawanka yake zama a Geshur, a Aram, na yi wannan alkawari, na ce, ‘In Ubangiji ya komo da ni Urushalima, zan yi wa Ubangiji sujada a Hebron.’ ”