Tsallake zuwa abun ciki

circa 1010–970 BC

The Reign of David

David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.

1,230 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 2 Sama’ila 13:6kusan 1032 K.H.

    Sai Amnon ya kwanta sai ka ce yana ciwo. Da sarki ya zo don ganinsa, sai Amnon ya ce, “Zan so ƙanuwata Tamar tă zo tă shirya mini abinci a gabana, don in ci daga hannunta.”

  2. 2 Sama’ila 13:7kusan 1032 K.H.

    Dawuda kuwa ya aika wa Tamar a fada, ya ce, “Ki je gidan Amnon ɗan’uwanki, ki yi masa abinci.”

  3. 2 Sama’ila 13:8kusan 1032 K.H.

    Saboda haka Tamar ta tafi gidan ɗan’uwanta Amnon, wanda yake kwance. Ta ɗauki fulawa, ta kwaɓa, ta yi burodi a gabansa ta toya shi.

  4. 2 Sama’ila 13:9kusan 1032 K.H.

    Sa’an nan ta juye a kasko ta ba shi burodin, amma ya ƙi ci. Amnon ya ce, “A sa kowa yă fita daga nan.” Saboda haka kowa ya fita ya bar shi.

  5. 2 Sama’ila 13:10kusan 1032 K.H.

    Sa’an nan Amnon ya ce wa Tamar, “Kawo abincin a nan a cikin ɗakin kwanciyata, don in ci daga hannunki.” Tamar kuwa ta ɗauki burodin da ta toya, ta kawo wa ɗan’uwanta Amnon a ciki ɗakin kwanciyarsa.

  6. 2 Sama’ila 13:11kusan 1032 K.H.

    Amma da ta kai masa don yă ci, sai ya cafke ta ya ce, “Zo in kwana da ke, ’yar’uwata.”

  7. 2 Sama’ila 13:12kusan 1032 K.H.

    Ta ce, “Kada ka yi wannan ɗan’uwana! Kada ka tilasta ni. Bai kamata a yi irin wannan abu a Isra’ila ba! Kada ka yi wannan mugun abu.

  8. 2 Sama’ila 13:13kusan 1032 K.H.

    Ni fa, ina zan sa kaina saboda kunya? Kai kuma za ka zama kamar wani mugun wawa a Isra’ila. Ina roƙonka ka yi wa sarki magana; ba zai hana ni aurenka ba.”

  9. 2 Sama’ila 13:14kusan 1032 K.H.

    Amma Amnon ya ƙi yă saurare ta, da yake ya fi ta ƙarfi, sai ya yi mata fyaɗe.

  10. 2 Sama’ila 13:15kusan 1032 K.H.

    Bayan ya yi lalata da ita sai Amnon ya ƙi ta da mummunan ƙiyayya. Zahiri ya ƙi ta fiye da ya ƙaunace ta. Sai Amnon ya ce mata, “Tashi, ki fita!”

  11. 2 Sama’ila 13:16kusan 1032 K.H.

    Ta ce, “A’a! Korina zai fi muni da abin da ka riga ka yi mini.” Amma ya ƙi yă saurare ta.

  12. 2 Sama’ila 13:17kusan 1032 K.H.

    Sai ya kira bawansa ya ce, “Fitar da matan nan daga nan, ka rufe ƙofa.”

  13. 2 Sama’ila 13:18kusan 1032 K.H.

    Saboda haka bawansa ya fitar da ita, ya kuma sa aka rufe ƙofa. Tana sanye da doguwar riga mai kayan ado masu tsada, gama wannan ne irin kayan da budurwai ’ya’yan sarki mata suke sawa.

  14. 2 Sama’ila 13:19kusan 1032 K.H.

    Sai Tamar ta zuba toka a kanta, ta kuma yayyage doguwar riga mai kayan adon da take sanye da shi. Ta sa hannunta a kai, ta tafi tana kuka da ƙarfi.

  15. 2 Sama’ila 13:20kusan 1032 K.H.

    Absalom ɗan’uwanta ya ce mata, “Amnon, ɗan’uwanki ya ɓata ki ko? To, ki yi shiru ’yar’uwata; ai, ɗan’uwanki ne. Kada wannan abu yă dame ki.” Tamar kuwa ta zauna a gidan ɗan’uwanta Absalom, zaman kaɗaici.

  16. 2 Sama’ila 13:21kusan 1032 K.H.

    Da Sarki Dawuda ya ji dukan abin da ya faru, sai ya husata ƙwarai.

  17. 2 Sama’ila 13:22kusan 1032 K.H.

    Absalom kuwa bai yi wa Amnon wata magana ta alheri ko ta mugunta ba; ya ƙi jinin Amnon domin ya ci mutuncin ƙanuwarsa Tamar.

  18. 2 Sama’ila 13:23kusan 1030 K.H.

    Bayan shekaru biyu, sa’ad da masu askin tumakin Absalom suna Ba’al-Hazor, kusa da iyakar Efraim, sai ya gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza a can.

  19. 2 Sama’ila 13:24kusan 1030 K.H.

    Sai Absalom ya je wurin sarki ya ce, “Bawanka ya sa masu askin tumaki sun zo. Ko sarki da fadawansa za su zo tare da ni?”

  20. 2 Sama’ila 13:25kusan 1030 K.H.

    Sarki ya ce, “A’a ɗana, bai kamata dukanmu mu tafi ba; don kada nauyi yă yi maka yawa.” Absalom dai ya dāge, duk da haka sarki ya ƙi yă je, sai dai ya albarkace shi.

  21. 2 Sama’ila 13:26kusan 1030 K.H.

    Sa’an nan Absalom ya ce, to, “In ba za ka ba, ina roƙonka bari Amnon ɗan’uwana yă zo tare da mu.” Sarki ya ce masa, “Don me zai tafi tare da kai?”

  22. 2 Sama’ila 13:27kusan 1030 K.H.

    Amma Absalom ya nace don sarki yă yarda, saboda haka sarki ya bar Amnon da sauran ’ya’yan sarki maza su tafi tare da shi.

  23. 2 Sama’ila 13:28kusan 1030 K.H.

    Absalom ya umarci mutanensa ya ce, “Ku saurara! Sa’ad da Amnon ya bugu sosai da giya na kuma ce muku, ‘Ku bugi Amnon,’ sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro. Ashe, ba ni ne na ba ku wannan umarni ba? Ku yi ƙarfin hali, ku kuma yi jaruntaka.”

  24. 2 Sama’ila 13:29kusan 1030 K.H.

    Saboda haka mutanen Absalom suka yi wa Amnon abin da Absalom ya umarta. Sai dukan sauran ’ya’yan sarki maza suka hau dawakansu suka gudu.

  25. 2 Sama’ila 13:30kusan 1030 K.H.

    Yayinda suke kan hanyarsu, sai labari ya kai kunnen Dawuda cewa, “Absalom ya kashe dukan ’ya’yan sarki maza; ko ɗayansu Absalom bai rage ba.”