- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1010–970 BC
The Reign of David
David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Sama’ila 11:14kusan 1035 K.H.
Da safe Dawuda ya rubuta wa Yowab wasiƙa ya ba wa Uriya.
- 2 Sama’ila 11:15kusan 1035 K.H.
A ciki wasiƙar ya rubuta, “Tura Uriya a gaba inda yaƙi ya fi zafi. Sa’an nan ka janye daga gare shi don a buge shi yă mutu.”
- 2 Sama’ila 11:16kusan 1035 K.H.
Saboda haka yayinda Yowab ya kai yaƙi kusa da birnin, sai tura Uriya a inda ya sani akwai jarumawan Ammon na gaske.
- 2 Sama’ila 11:17kusan 1035 K.H.
Sa’ad da mutanen garin suka fito suka yaƙi Yowab, sai waɗansu mutane daga sojojin Dawuda suka mutu; Uriya mutumin Hitti ma ya mutu.
- 2 Sama’ila 11:18kusan 1035 K.H.
Yowab ya aika wa Dawuda cikakken labari batun yaƙin.
- 2 Sama’ila 11:19kusan 1035 K.H.
Ya umarci manzon ya ce, “Da ka gama yin wa sarki wannan batun yaƙin,
- 2 Sama’ila 11:20kusan 1035 K.H.
wataƙila sarki yă husata, yă tambaye ka, ‘Me ya sa kuka je kusa da birnin don ku yi yaƙi? Ba ku san cewa za su yi harbi daga katanga ba?
- 2 Sama’ila 11:21kusan 1035 K.H.
Wane ne ya kashe Abimelek ɗan Yerub-Beshet? Ba mace ce ta jefa dutsen niƙa a kansa daga katanga, ta haka ya mutu a Tebez ba? Me ya sa kuka je kurkusa da katangar?’ In ya tambaye ka wannan, sai ka ce masa, ‘Har bawanka Uriya mutumin Hitti ma ya mutu.’ ”
- 2 Sama’ila 11:22kusan 1035 K.H.
Manzon ya tashi ya tafi, da ya iso kuwa sai ya gaya wa Dawuda dukan abin da Yowab ya aike shi yă faɗa.
- 2 Sama’ila 11:23kusan 1035 K.H.
Manzon ya ce wa Dawuda, “Mutanen sun sha kanmu suka fito suka yaƙe mu a fili, amma muka kore su har ƙofar birni.
- 2 Sama’ila 11:24kusan 1035 K.H.
Sa’an nan maharba suka yi ta harbi daga katanga har waɗansu mutanen sarki suka mutu. Ban da haka ma, Uriya mutumin Hitti bawan sarki ya mutu.”
- 2 Sama’ila 11:25kusan 1035 K.H.
Dawuda ya ce wa manzon, “Ka gaya wa Yowab, ‘Kada ka bar wannan yă dame ka; yadda takobi ya lamushe wannan, haka zai lamushe wancan ma. Ku ƙara matsa wa garin lamba, ku hallaka shi.’ Ka faɗa haka don ka ƙarfafa Yowab.”
- 2 Sama’ila 11:26kusan 1035 K.H.
Da matar Uriya ta ji cewa mijinta ya mutu, sai ta yi makoki saboda shi.
- 2 Sama’ila 11:27kusan 1035 K.H.
Bayan kwanakin makoki suka ƙare, Dawuda ya sa aka kawo ta gidansa, ta kuwa zama matarsa, ta kuma haifa masa ɗa. Sai dai abin da Dawuda ya yi bai gamshi Ubangiji ba.
- 2 Sama’ila 12:1kusan 1034 K.H.
Ubangiji ya aiki Natan wurin Dawuda. Da ya tafi wajensa, sai ya ce, “An yi waɗansu mutum biyu a wani gari, ɗaya mai arziki, ɗayan kuma matalauci.
- 2 Sama’ila 12:2kusan 1034 K.H.
Mai arzikin yana da babban garken tumaki, da kuma shanu,
- 2 Sama’ila 12:3kusan 1034 K.H.
amma matalauci ba shi da kome sai ’yar tunkiyar da ya sayo. Ya yi kiwonta, ta kuwa yi girma tare shi da yaransa. Takan ci tare da shi ta sha ruwa a kwaf nasa, har ma ta kwanta a ƙirjinsa. Ta ma zama kamar ’ya a gare shi.
- 2 Sama’ila 12:4kusan 1034 K.H.
“To, sai ga wani baƙo ya zo wurin mai arzikin nan, amma mai arzikin ya ƙi yă kama tunkiyarsa, ko saniyarsa yă yanka don yă shirya wa baƙon da ya zo abinci. A maimako, sai ya je ya kama ’yar tunkiyan nan ta matalaucin ya yanka ya shirya wa mutumin da ya zo masa.”
- 2 Sama’ila 12:5kusan 1034 K.H.
Dawuda ya husata ƙwarai da mutumin, ya ce wa Natan, “Muddin Ubangiji yana a raye, mutumin da ya yi wannan ya cancanci yă mutu!
- 2 Sama’ila 12:6kusan 1034 K.H.
Dole yă biya diyyar tunkiyan nan sau huɗu, domin ya aikata haka ba tausayi.”
- 2 Sama’ila 12:7kusan 1034 K.H.
Sai Natan ya ce wa Dawuda, “Kai ne mutumin! Ga abin da Ubangiji, Allah ya ce, ‘Na naɗa ka sarki bisa Isra’ila, na kuma cece ka daga hannun Shawulu.
- 2 Sama’ila 12:8kusan 1034 K.H.
Na ba ka gidan maigidanka, da matan maigidanka duka. Na ba ka gidan Isra’ila da Yahuda. Da a ce dukan waɗannan sun kāsa maka, ai, da na ƙara maka.
- 2 Sama’ila 12:9kusan 1034 K.H.
Me ya sa ka rena maganar Ubangiji ta wurin yin mugunta haka a idonsa? Ka kashe Uriya mutumin Hitti da takobi, ka kuma ɗauki matarsa tă zama matarka. Ka kashe shi da takobin Ammonawa.
- 2 Sama’ila 12:10kusan 1034 K.H.
To, fa, takobi ba zai taɓa rabu da gidanka ba, domin ka rena ni, ka kuma ƙwace matar Uriya mutumin Hitti ta zama matarka.’
- 2 Sama’ila 12:11kusan 1034 K.H.
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Daga cikin iyalinka zan kawo masifa a kanka. A idanunka zan ɗauki matanka in ba wa wani da yake kusa da kai, zai kuwa kwana da su da rana tsaka.