- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1010–970 BC
The Reign of David
David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Sama’ila 8:14kusan 1040 K.H.
Ya ajiye rundunar sojoji ko’ina a Edom, dukan mutanen Edom kuwa suka zama bayin Dawuda. Ubangiji ya ba wa Dawuda nasara a duk inda ya tafi.
- 2 Sama’ila 8:15kusan 1040 K.H.
Dawuda ya yi mulkin dukan ƙasar Isra’ila, yana yin wa dukan jama’arsa shari’ar gaskiya da adalci.
- 2 Sama’ila 8:16kusan 1040 K.H.
Yowab ɗan Zeruhiya ya zama shugaban sojoji; Yehoshafat ɗan Ahilud kuwa shi ne marubucin tarihi;
- 2 Sama’ila 8:17kusan 1040 K.H.
Zadok ɗan Ahitub da Ahimelek ɗan Abiyatar, su ne firistoci; Serahiya kuma sakatare;
- 2 Sama’ila 8:18kusan 1040 K.H.
Benahiya ɗan Yehohiyada ne shugaban Keretawa da Feletiyawa, wato, sojoji masu gadin Dawuda, sa’an nan ’ya’yan Dawuda maza su ne mashawartan sarki.
- 2 Sama’ila 9:1kusan 1040 K.H.
Wata rana Dawuda ya yi tambaya ya ce, “Akwai wani har yanzu da ya rage a gidan Shawulu wanda zan nuna masa alheri saboda Yonatan?”
- 2 Sama’ila 9:2kusan 1040 K.H.
To, akwai wani bawa na gidan Shawulu mai suna Ziba. Sai aka kira shi yă bayyana a gaban Dawuda, sarki ya ce masa, “Kai ne Ziba?” Sai ya ce, “I, ni ne, ranka yă daɗe.”
- 2 Sama’ila 9:3kusan 1040 K.H.
Sa’an nan sarki ya yi tambaya ya ce, “Babu wani har yanzu da ya rage a gidan Shawulu don in nuna masa alherin Allah?” Ziba ya ce wa sarki, “Har yanzu akwai ɗan Yonatan da ya rage, sai dai shi gurgu ne a dukan ƙafafu.”
- 2 Sama’ila 9:4kusan 1040 K.H.
Sarki ya ce, “Ina yake?” Ziba ya ce, “Yana a gidan Makir ɗan Ammiyel a Lo Debar.”
- 2 Sama’ila 9:5kusan 1040 K.H.
Saboda haka Sarki Dawuda ya umarta aka kawo shi daga gidan Makir ɗan Ammiyel, daga Lo Debar.
- 2 Sama’ila 9:6kusan 1040 K.H.
Sa’ad da Mefiboshet ɗan Yonatan, ɗan Shawulu, ya zo wurin Dawuda, sai ya rusuna har ƙasa ya yi gaisuwar bangirma. Dawuda ya ce, “Mefiboshet!” Shi kuwa ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, ga ni, bawanka.”
- 2 Sama’ila 9:7kusan 1040 K.H.
Dawuda ya ce, “Kada ka ji tsoro, gama tabbatacce zan nuna maka alheri saboda mahaifinka Yonatan. Zan mayar maka da dukan ƙasar da take ta kakanka Shawulu, kullum kuma za ka ci a teburina.”
- 2 Sama’ila 9:8kusan 1040 K.H.
Mefiboshet ya rusuna ya ce, “Ni ne wa har da za ka kula da ni? Ai! Ni bawanka ne da bai ma fi mataccen kare daraja ba.”
- 2 Sama’ila 9:9kusan 1040 K.H.
Sai sarki ya kira Ziba bawan Shawulu, ya ce masa, “Na ba wa jikan maigidanka kome da yake na Shawulu da iyalinsa
- 2 Sama’ila 9:10kusan 1040 K.H.
Kai da ’ya’yanka maza da bayinka za ku riƙa yin masa noma, ku kuma kawo hatsin, don jikan maigidanka yă sami abinci. Mefiboshet kuma, jikan maigidanka, zai riƙa ci a teburina.” (Ziba kuwa yana da ’ya’ya maza goma sha biyar da kuma bayi ashirin.)
- 2 Sama’ila 9:11kusan 1040 K.H.
Sai Ziba ya ce wa sarki, “Bawanka zai aikata dukan abin da ranka yă daɗe sarki, ya umarce shi.” Saboda haka Mefiboshet ya riƙa ci a teburin Dawuda kamar sauran ’ya’yan sarki.
- 2 Sama’ila 9:12kusan 1040 K.H.
Mefiboshet yana da wani ƙaramin ɗa sunansa Mika, dukan iyalin gidan Ziba kuwa bayin Mefiboshet ne.
- 2 Sama’ila 9:13kusan 1040 K.H.
Mefiboshet ya zauna a Urushalima, gama kullum yana ci a teburin sarki, shi kuwa gurgu ne a dukan ƙafafu.
- 2 Sama’ila 10:1kusan 1037 K.H.
Ana nan sai sarkin Ammonawa ya rasu, ɗansa Hanun kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.
- 2 Sama’ila 10:2kusan 1037 K.H.
Dawuda ya yi tunani a ransa ya ce, “Zan yi wa Hanun ɗan Nahash alheri kamar yadda mahaifinsa ya yi mini.” Saboda haka sai Dawuda ya aiki jakadu su yi masa ta’aziyyar mutuwar mahaifinsa. Sa’ad da mutanen Dawuda suka isa ƙasar Ammonawa,
- 2 Sama’ila 10:3kusan 1037 K.H.
sai manyan mutanen Ammonawa suka ce wa Hanun shugabansu, “Kana tsammani Dawuda yana girmama mahaifinka ne da ya aiko da jakadu su kawo maka ta’aziyya? Ai, wayo ya yi don yă ga asirin birninmu, yă san ƙarfinmu, yă kuma ci mu da yaƙi.”
- 2 Sama’ila 10:4kusan 1037 K.H.
Saboda haka Hanun ya kama mutanen Dawuda ya aske rabin gemun kowannensu, ya yayyage rigunarsu daidai ɗuwawu, sa’an nan ya sallame su.
- 2 Sama’ila 10:5kusan 1037 K.H.
Sa’ad da aka gaya wa Dawuda game da wannan, sai ya aiki manzanni su taryi waɗannan mutanen da aka ci mutuncinsu, gama an wulaƙanta su ƙwarai. Sai sarki ya ce musu, “Ku dakata a Yeriko har sai gemunku ya sāke girma, sa’an nan ku dawo.”
- 2 Sama’ila 10:6kusan 1037 K.H.
Da Ammonawa suka gane cewa Dawuda ya ji fushi da su sosai saboda abin da suka yi, sai suka yi hayar sojojin ƙasar Arameyawa dubu ashirin daga Bet Rehob da Aram-Zoba, suka kuma yi hayar sarkin Ma’aka tare da mutum dubu ɗaya, suka kuma yi hayar maza dubu goma sha biyu daga Tob.
- 2 Sama’ila 10:7kusan 1037 K.H.
Da jin haka, Dawuda ya tura Yowab da dukan sojojin yaƙi.