Tsallake zuwa abun ciki

circa 1010–970 BC

The Reign of David

David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.

1,230 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 2 Sama’ila 7:18kusan 1042 K.H.

    Sa’an nan Sarki Dawuda ya je ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Wane ne ni, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ko gidana, har da ka ɗaga mu zuwa wannan matsayi?

  2. 2 Sama’ila 7:19kusan 1042 K.H.

    Har ya zama kamar wannan bai isa ba a gabanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka kuma yi magana game da nan gaba na gidan bawanka. Haka ka saba yi da mutane, ya Ubangiji Mai Iko Duka?

  3. 2 Sama’ila 7:20kusan 1042 K.H.

    “Me kuma Dawuda zai ce maka? Gama ka san bawanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka.

  4. 2 Sama’ila 7:21kusan 1042 K.H.

    Gama saboda maganarka da kuma bisa ga nufinka, ka aikata wannan babban abu, ka kuma sanar da bawanka.

  5. 2 Sama’ila 7:22kusan 1042 K.H.

    “Kai mai girma ne, ya Ubangiji Mai Iko Duka! Babu wani kamar ka, babu kuma wani Allah sai kai; kamar yadda muka ji da kunnuwanmu.

  6. 2 Sama’ila 7:23kusan 1042 K.H.

    Wane ne kuma yake kamar da mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allah ya fita don yă kuɓutar wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa da kuma al’amuran banmamaki ta wurin korin al’ummai da allolinsu daga gaban mutanenka, waɗanda ka kuɓutar daga Masar?

  7. 2 Sama’ila 7:24kusan 1042 K.H.

    Ka kafa mutanenka Isra’ila kamar naka na kanka har abada, kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.

  8. 2 Sama’ila 7:25kusan 1042 K.H.

    “Yanzu kuwa, ya Ubangiji Allah, ka cika alkawarin da ka yi game da bawanka da gidansa. Ka yi kamar yadda ka alkawarta,

  9. 2 Sama’ila 7:26kusan 1042 K.H.

    domin sunanka yă kasance da girma har abada. Sa’an nan mutane za su ce, ‘Ubangiji Maɗaukaki, Allah ne a bisa Isra’ila!’ Kuma gidan bawanka Dawuda zai kahu a gabanka.

  10. 2 Sama’ila 7:27kusan 1042 K.H.

    “Ya Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, ka bayyana wa bawanka cewa, ‘Zan gina maka gida.’ Saboda haka bawanka ya sami ƙarfin hali yă miƙa maka wannan addu’a.

  11. 2 Sama’ila 7:28kusan 1042 K.H.

    Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai Allah ne! Maganarka da aminci take, ka kuma yi wa bawanka waɗannan abubuwa masu kyau.

  12. 2 Sama’ila 7:29kusan 1042 K.H.

    In ya gamshe ka, bari ka albarkaci gidan bawanka don yă dawwama a gabanka har abada; gama kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka riga ka yi magana, kuma saboda kai ka sa albarka ga gidan bawanka, lalle zai kasance da albarka har abada.”

  13. 2 Sama’ila 8:1kusan 1040 K.H.

    Ana nan, sai Dawuda ya ci Filistiyawa da yaƙi, ya kawo ƙarshen mulkinsu a ƙasar, ya kuma ƙwace ƙasar Meteg Amma daga hannun Filistiyawa.

  14. 2 Sama’ila 8:2kusan 1040 K.H.

    Haka kuma Dawuda ya ci Mowabawa. Ya sa suka kwanta a ƙasa, ya kuma auna su da igiya. Kowane awo biyu ya sa a kashe su, amma awo na uku sai yă sa a bar su da rai. Saboda haka Mowabawa suka zama bayin Dawuda, suka kuma kawo masa haraji.

  15. 2 Sama’ila 8:3kusan 1040 K.H.

    Ban da haka, Dawuda ya yaƙi Hadadezer ɗan Rehob, sarkin Zoba. Wannan ya faru a lokacin da Hadadezer yake kan hanyarsa zuwa Kogin Yuferites don yă sāke mai da wurin a ƙarƙashin ikonsa.

  16. 2 Sama’ila 8:4kusan 1040 K.H.

    Dawuda ya kame keken yaƙinsa guda dubu, mahayan keken yaƙinsa dubu bakwai, da sojojin ƙasa dubu ashirin. Ya yayyanke agaran dawakan duka amma ya bar dawakai kekunan yaƙi ɗari.

  17. 2 Sama’ila 8:5kusan 1040 K.H.

    Sa’ad da Arameyawan Damaskus suka zo don su taimaki Hadadezer sarkin Zoba, sai Dawuda ya karkashe dubu ashirin da biyunsu.

  18. 2 Sama’ila 8:6kusan 1040 K.H.

    Ya ajiye ƙungiyoyi sojoji a masarautar Arameyawan Damaskus, Arameyawa kuwa suka zama bayinsa, suka biya shi haraji. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a duk inda ya tafi.

  19. 2 Sama’ila 8:7kusan 1040 K.H.

    Dawuda ya kwashe garkuwoyin zinariya na shugabannin sojojin Hadadezer ya kawo Urushalima.

  20. 2 Sama’ila 8:8kusan 1040 K.H.

    Daga Teba da Berotai, garuruwan da suke ƙarƙashin Hadadezer, Sarki Dawuda ya kwashe tagulla masu yawan gaske.

  21. 2 Sama’ila 8:9kusan 1040 K.H.

    Da Towu sarkin Hamat ya ji cewa Dawuda ya ci dukan rundunar Hadadezer,

  22. 2 Sama’ila 8:10kusan 1040 K.H.

    sai ya aiki ɗansa Yoram wurin Sarki Dawuda yă gaishe, yă kuma yi masa barka saboda nasarar da ya yi a kan Hadadezer, gama Hadadezer nan ya hana Towu sakewa. Yoram ya tafi ɗauke da kayan azurfa, da na zinariya, da na tagulla.

  23. 2 Sama’ila 8:11kusan 1040 K.H.

    Sarki Dawuda kuwa ya keɓe waɗannan kayayyaki wa Ubangiji, yadda ya yi da zinariya, da kuma azurfa daga dukan al’umman da ya mallaka,

  24. 2 Sama’ila 8:12kusan 1040 K.H.

    wato, azurfa da zinariyan mutanen Edom, da na Mowabawa, da na Ammonawa, da na Filistiyawa, da na Amalekawa, da ganimar Hadadezer ɗan Rehob, sarkin Zoba.

  25. 2 Sama’ila 8:13kusan 1040 K.H.

    Dawuda kuwa ya ƙara zama shahararre bayan ya dawo daga kai wa ƙasar Aram hari, daga nan sai ya je ya karkashe mutanen Edom dubu goma sha takwas a Kwarin Gishiri.