Tsallake zuwa abun ciki

circa 1010–970 BC

The Reign of David

David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.

1,230 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 2 Sama’ila 16:22kusan 1023 K.H.

    Saboda haka suka kafa wa Absalom tenti a bisa rufin ɗaki, a can ya kwana da ƙwarƙwaran mahaifinsa a gaban dukan Isra’ila.

  2. 2 Sama’ila 16:23kusan 1023 K.H.

    To, a kwanakin nan shawarar da Ahitofel yakan bayar takan zama kamar wadda aka nemi daga Allah ne. Haka Dawuda da Absalom duk suke ɗaukan dukan shawarar Ahitofel.

  3. 2 Sama’ila 17:1kusan 1023 K.H.

    Ahitofel ya ce wa Absalom, “Zan zaɓi mutum dubu goma sha biyu su fita a daren nan in fafari Dawuda.

  4. 2 Sama’ila 17:2kusan 1023 K.H.

    Zan fāɗa masa sa’ad da yake cikin gajiya da karayar zuciya. Zan firgita shi, mutanen da suke tare da shi kuwa za su gudu. Sarki ne kaɗai zan kashe

  5. 2 Sama’ila 17:3kusan 1023 K.H.

    in dawo da dukan mutanen a gare ka. Mutuwar wanda kake nema zai zama dawowar duka; dukan mutanen ba za su cutu ba.”

  6. 2 Sama’ila 17:4kusan 1023 K.H.

    Wannan shawara ta gamshi Absalom da dukan dattawan Isra’ila.

  7. 2 Sama’ila 17:5kusan 1023 K.H.

    Amma Absalom ya ce, “A kira mini Hushai mutumin Arkitawan nan shi ma, mu ji abin da zai ce.”

  8. 2 Sama’ila 17:6kusan 1023 K.H.

    Da Hushai ya zo wurinsa, sai Absalom ya ce, “Ahitofel ya ba da wannan shawara. Mu yi abin da ya ce? In ba haka ba, sai ka ba mu ra’ayinka.”

  9. 2 Sama’ila 17:7kusan 1023 K.H.

    Hushai ya ce wa Absalom, “Shawarar da Ahitofel ya bayar a wannan lokaci kam, ba ta da kyau.

  10. 2 Sama’ila 17:8kusan 1023 K.H.

    Ka san mahaifinka da mutanensa mayaƙa ne, suna cikin fushi kamar mugun beyar da aka ƙwace mata ’ya’ya. Ban da haka ma, mahaifinka gogagge ne a yaƙi; ba zai kwana da rundunar ba.

  11. 2 Sama’ila 17:9kusan 1023 K.H.

    Kai, ko yanzu ma, ya riga ya ɓuya cikin kogo ko kuma a wani wuri. In har ya fara kai wa rundunarka hari duk wanda ya ji, zai ce, ‘An yi kaca-kaca da rundunar da suka bi Absalom.’

  12. 2 Sama’ila 17:10kusan 1023 K.H.

    Kai, ko jarumi mai zuciya kamar na zaki ma, zai narke don tsoro, gama dukan Isra’ila sun sani mahaifinka mayaƙi ne, sun kuma san cewa waɗanda suke tare da shi jarumawa ne.

  13. 2 Sama’ila 17:11kusan 1023 K.H.

    “Saboda haka ina ba ka shawara, bari a tara maka dukan Isra’ila, daga Dan zuwa Beyersheba da yawansu ya yi kamar yashin bakin teku, kai kanka ka jagorance su zuwa fagen fama.

  14. 2 Sama’ila 17:12kusan 1023 K.H.

    Sa’an nan za mu fāɗa masa duk inda yake, za mu fāɗa masa kamar yadda raɓa takan fāɗo a bisa ƙasa. Da shi da mutanensa babu ko ɗaya da za a bari da rai.

  15. 2 Sama’ila 17:13kusan 1023 K.H.

    In ma ya janye zuwa cikin birni, sai dukan Isra’ila su kawo igiyoyi wa wannan birni, su ja shi zuwa kwari yă wargaje, yadda ba za a bar wani dutse a kan wani ba.”

  16. 2 Sama’ila 17:14kusan 1023 K.H.

    Absalom da dukan mutanen Isra’ila suka ce, “Shawarar Hushai mutumin Arkitawa ta fi ta Ahitofel kyau.” Gama Ubangiji ya ƙudura yă wofinta kyakkyawar shawarar Ahitofel, don yă jawo wa Absalom masifa.

  17. 2 Sama’ila 17:15kusan 1023 K.H.

    Hushai ya ce wa Zadok da Abiyatar, firistoci, “Ahitofel ya ba wa Absalom da dattawan Isra’ila shawara su yi kaza da kaza, amma na ba su shawara su yi haka, su yi haka.

  18. 2 Sama’ila 17:16kusan 1023 K.H.

    Yanzu sai ku aika wa Dawuda saƙo nan da nan ku ce masa, ‘Kada ka kwana a mashigai cikin hamada; ka tabbata ka haye ba faci, in ba haka ba sarki da dukan mutanensa za su hallaka.’ ”

  19. 2 Sama’ila 17:17kusan 1023 K.H.

    Yonatan da Ahimawaz suna zaune a En Rogel. Wata baranya ce za tă je ta faɗa musu, su kuma su tafi su gaya wa Sarki Dawuda don suna tsoro kada a ga suna shiga birnin.

  20. 2 Sama’ila 17:18kusan 1023 K.H.

    Amma wani saurayi ya gan su, ya gaya wa Absalom. Sai dukansu biyu suka tashi da sauri suka shiga gidan wani mutum a Bahurim. Yana da rijiya a cikin gida, sai suka shiga cikinta.

  21. 2 Sama’ila 17:19kusan 1023 K.H.

    Matarsa mutumin kuwa ta kawo tabarma ta shimfiɗa a bakin rijiyar, sai ta kawo hatsi ta baza a kanta. Ba kuwa wanda ya san abin da ta yi.

  22. 2 Sama’ila 17:20kusan 1023 K.H.

    Da mutanen Absalom suka zo wurin matan a gidan, suka ce, “Ina Yonatan da Ahimawaz?” Matar ta ce, “Tuni, sun haye rafi.” Sai mutanen suka yi ta nemansu amma ba su ga kowa, sai suka koma Urushalima.

  23. 2 Sama’ila 17:21kusan 1023 K.H.

    Bayan mutanen suka tafi, sai su biyun suka fito daga rijiyar suka je suka gaya wa Sarki Dawuda. Suka ce masa, “Maza ka ƙetare kogi; Ahitofel ya ba wa Absalom shawara a yi maka kaza da kaza.”

  24. 2 Sama’ila 17:22kusan 1023 K.H.

    Saboda haka Dawuda da dukan mutanen da suke tare da shi suka tashi suka ƙetare Urdun. Kafin wayewar gari, babu wanda ya rage da bai haye ba.

  25. 2 Sama’ila 17:23kusan 1023 K.H.

    Da Ahitofel ya ga ba a bi shawararsa ba, sai ya hau jakinsa ya koma gidansa a garinsu. Ya kintsa gidansa sa’an nan ya rataye kansa. Ta haka ya mutu, aka kuma binne shi a kabarin mahaifinsa.