- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1010–970 BC
The Reign of David
David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Sama’ila 21:18kusan 1018 K.H.
Ana nan, sai aka sāke yin wani yaƙin da Filistiyawa, a Gob. A lokacin Sibbekai mutumin Husha ya kashe Saf, wani daga zuriyar Rafa.
- 2 Sama’ila 21:19kusan 1018 K.H.
Sai aka sāke yin wani yaƙin da Filistiyawa a Gob, Elhanan ɗan Ya’are-Oregim mutumin Betlehem ya kashe Goliyat mutumin Gat, wanda girmar sandan māshinsa ta yi kama da taɓarya.
- 2 Sama’ila 21:20kusan 1018 K.H.
Har wa yau a wani yaƙin da aka yi a Gat, akwai wani ƙaton mutum mai yatsotsi shida a kowane hannu, da kuma yatsotsi shida a kowane ƙafa, yatsotsi ashirin da huɗu ke nan. Shi ma daga zuriya Rafa ne.
- 2 Sama’ila 21:21kusan 1018 K.H.
Da ya yi wa Isra’ila reni, sai Yonatan ɗan Shimeya, ɗan’uwa Dawuda, ya kashe shi.
- 2 Sama’ila 21:22kusan 1018 K.H.
Waɗannan huɗu zuriyar Rafa ne a Gat, suka kuwa mutu ta hannu Dawuda da mutanensa.
- 2 Sama’ila 22:1kusan 1018 K.H.
Dawuda ya rera wannan waƙa ga Ubangiji, sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa, da kuma daga hannun Shawulu.
- 2 Sama’ila 22:2kusan 1018 K.H.
Ya ce, “Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona;
- 2 Sama’ila 22:3kusan 1018 K.H.
Allahna shi ne dutsena. A gare shi nake samun kāriya shi ne garkuwata da kuma ƙahon cetona. Shi ne mafakata, maɓuyata, da mai cetona. Daga mutane masu fitina, ka cece ni.
- 2 Sama’ila 22:4kusan 1018 K.H.
“Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo, na kuwa tsira daga abokan gābana.
- 2 Sama’ila 22:5kusan 1018 K.H.
Raƙumar ruwan mutuwa sun kewaye ni; raƙumar ruwan hallaka suna cin ƙarfina.
- 2 Sama’ila 22:6kusan 1018 K.H.
Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe ni; tarkuna kuma suka auka mini.
- 2 Sama’ila 22:7kusan 1018 K.H.
“A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; na yi kira ga Allahna. Daga cikin haikalinsa ya saurare muryata; kukata ta zo kunnensa.
- 2 Sama’ila 22:8kusan 1018 K.H.
Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza, harsashan sararin sama sun jijjigu; suka yi makyarkyata saboda yana fushi.
- 2 Sama’ila 22:9kusan 1018 K.H.
Hayaƙi ya taso daga kafaffen hancinsa; harshen wuta mai cinyewa daga bakinsa, garwashi mai ƙuna daga bakinsa.
- 2 Sama’ila 22:10kusan 1018 K.H.
Ya buɗe sararin sama, ya sauko ƙasa, girgije mai duhu suna ƙarƙashin ƙafafunsa.
- 2 Sama’ila 22:11kusan 1018 K.H.
Ya hau kerubobi, ya tashi sama; ya yi firiya a fikafikan iska.
- 2 Sama’ila 22:12kusan 1018 K.H.
Ya mai da duhu abin rufuwarsa gizagizai masu kauri cike da ruwa suka kewaye shi.
- 2 Sama’ila 22:13kusan 1018 K.H.
Daga cikin hasken gabansa garwashi wuta mai ci ya yi walƙiya.
- 2 Sama’ila 22:14kusan 1018 K.H.
Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama; aka ji muryar Mafi Ɗaukaka.
- 2 Sama’ila 22:15kusan 1018 K.H.
Ya harbe kibiyoyi, ya wartsar da abokan gāba, da walƙiya kuma ya sa suka gudu.
- 2 Sama’ila 22:16kusan 1018 K.H.
Aka bayyana kwarin teku, tushen duniya suka tonu. A tsawatawar Ubangiji, da numfashinsa mai ƙarfi daga hancinsa.
- 2 Sama’ila 22:17kusan 1018 K.H.
“Daga sama ya miƙo hannu ya ɗauke ni, ya tsamo ni daga zurfafa ruwaye.
- 2 Sama’ila 22:18kusan 1018 K.H.
Ya kuɓutar da ni daga hannun abokin gāba mai iko, daga maƙiyina da suka fi ƙarfina.
- 2 Sama’ila 22:19kusan 1018 K.H.
Suka auka mini cikin ranar masifata, amma Ubangiji ya kiyaye ni.
- 2 Sama’ila 22:20kusan 1018 K.H.
Ya fito da ni, ya kai ni wuri mafi fāɗi; ya kuɓutar da ni gama yana jin daɗina.