- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1010–970 BC
The Reign of David
David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Sama’ila 22:21kusan 1018 K.H.
“Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina; bisa ga tsabtar hannuwana ya sāka mini.
- 2 Sama’ila 22:22kusan 1018 K.H.
Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji; ban yi wani mugun abu da zai juyar da ni daga Allahna ba.
- 2 Sama’ila 22:23kusan 1018 K.H.
Dukan dokokinsa suna a gabana; ban ƙi ko ɗaya daga umarnansa ba.
- 2 Sama’ila 22:24kusan 1018 K.H.
Ba ni da laifi a gabansa na kiyaye kaina daga yin zunubi.
- 2 Sama’ila 22:25kusan 1018 K.H.
Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina bisa ga tsarkina a gabansa.
- 2 Sama’ila 22:26kusan 1018 K.H.
“Ga masu aminci, kakan nuna kanka mai aminci, ga marasa laifi, kakan nuna kanka marar laifi,
- 2 Sama’ila 22:27kusan 1018 K.H.
ga masu tsarki, kakan nuna musu tsarki. Amma ga masu karkataccen hali, kakan nuna kanka mai wayo.
- 2 Sama’ila 22:28kusan 1018 K.H.
Kakan ceci mai tawali’u, amma idanunka suna a kan masu girman kai don ka ƙasƙantar da su.
- 2 Sama’ila 22:29kusan 1018 K.H.
Ya Ubangiji kai ne fitilata; Ubangiji ya mai da duhuna haske.
- 2 Sama’ila 22:30kusan 1018 K.H.
Da taimakonka zan iya auka wa rundunar sojoji; tare da Allahna zan iya hawan katanga.
- 2 Sama’ila 22:31kusan 1018 K.H.
“Ga Allah dai, hanyarsa cikakkiya ce; maganar Ubangiji babu kuskure. Shi garkuwa ce ga waɗanda suka nemi mafaka a gare shi.
- 2 Sama’ila 22:32kusan 1018 K.H.
Gama wane ne Allah, in ba Ubangiji ba? Wane ne dutse kuma in ba Allahnmu ba?
- 2 Sama’ila 22:33kusan 1018 K.H.
Allah ne ya ba ni ƙarfi, ya kuma mai da hanyata cikakkiya.
- 2 Sama’ila 22:34kusan 1018 K.H.
Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa; ya sa na iya tsayawa a kan duwatsu.
- 2 Sama’ila 22:35kusan 1018 K.H.
Ya hori hannuwana don yaƙi, hannuwana za su iya tanƙware bakan tagulla.
- 2 Sama’ila 22:36kusan 1018 K.H.
Ka ba ni garkuwar nasararka; ka sauko don ka sa in sami girma.
- 2 Sama’ila 22:37kusan 1018 K.H.
Ka fadada hanya a ƙarƙashina domin kada idon ƙafana yă juya.
- 2 Sama’ila 22:38kusan 1018 K.H.
“Na fafari abokan gābana, na murƙushe su; ban kuwa juya ba sai da na hallaka su.
- 2 Sama’ila 22:39kusan 1018 K.H.
Na hallaka su ƙaƙaf, ba kuwa za su ƙara tashi ba, sun fāɗi a ƙarƙashin sawuna.
- 2 Sama’ila 22:40kusan 1018 K.H.
Ka ba ni ƙarfi don yaƙi; ka sa maƙiyina suka rusuna a ƙafafuna.
- 2 Sama’ila 22:41kusan 1018 K.H.
Ka sa abokan gābana suka juya a guje, na kuwa hallaka maƙiyina.
- 2 Sama’ila 22:42kusan 1018 K.H.
Suka nemi taimako, amma babu wanda zai cece su, suka yi kira ga Ubangiji, amma ba a amsa musu ba.
- 2 Sama’ila 22:43kusan 1018 K.H.
Na murƙushe su, suka yi laushi kamar ƙura; na daka na kuma tattake su kamar caɓi a kan tituna.
- 2 Sama’ila 22:44kusan 1018 K.H.
“Ka kuɓutar da ni daga harin mutanena; ka kiyaye ni kamar shugaban al’ummai. Mutanen da ban sansu ba za su kasance a ƙarƙashina,
- 2 Sama’ila 22:45kusan 1018 K.H.
baƙi kuma su na zuwa don su yi mini fadanci; da zarar sun ji ni, sukan yi mini biyayya.