circa 1010–970 BC
The Reign of David
David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Sama’ila 23:20kusan 1055 K.H.
Benahiya, ɗan Yehohiyada mutumin Kabzeyel shi ma jarumi ne sosai, ya yi nasarori masu yawa. Ya bugi ƙwararrun jarumawan Mowab guda biyu. Ya kuma shiga rami wata ranar da ake ƙanƙara, ya kashe zaki.
- 2 Sama’ila 23:21kusan 1055 K.H.
Ya kuma buge wani jibgaggen mutumin Masar. Duk da māshin da mutumin Masar yana riƙe a hannunsa, Benahiya ya kai masa hari da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannunsa, ya kuma kashe shi da māshin.
- 2 Sama’ila 23:22kusan 1055 K.H.
Irin nasarorin da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma jarumi ne sosai kamar jarumawan nan uku.
- 2 Sama’ila 23:23kusan 1055 K.H.
Aka fi ba shi girma fiye da talatin ɗin nan, amma ba ya cikin ukun. Dawuda ya sa shi yă zama ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.
- 2 Sama’ila 23:24kusan 1055 K.H.
Cikin talatin ɗin kuwa akwai, Asahel, ɗan’uwan Yowab, Elhanan, ɗan Dodo mutumin Betlehem,
- 2 Sama’ila 23:25kusan 1055 K.H.
Shamma, mutumin Harod, Elika, mutumin Harod,
- 2 Sama’ila 23:26kusan 1055 K.H.
Helez, mutumin Falti, Ira, ɗan Ikkesh mutumin Tekowa,
- 2 Sama’ila 23:27kusan 1055 K.H.
Abiyezer, mutumin Anatot, da Mebunnai, mutumin Husha,
- 2 Sama’ila 23:28kusan 1055 K.H.
Zalmon, mutumin Aho, da Maharai, mutumin Netofa,
- 2 Sama’ila 23:29kusan 1055 K.H.
Heleb, ɗan Ba’ana daga Netofa, Ittai, ɗan Ribai mutumin Gibeya a Benyamin,
- 2 Sama’ila 23:30kusan 1055 K.H.
Benahiya, mutumin Firaton, da Hiddai, daga rafuffukan Ga’ash,
- 2 Sama’ila 23:31kusan 1055 K.H.
Abi-Albon, mutumin Arba, da Azmawet, mutumin Bahurim,
- 2 Sama’ila 23:32kusan 1055 K.H.
Eliyaba, mutumin Sha’albo, ’Ya’yan Yashen, Yonatan,
- 2 Sama’ila 23:33kusan 1055 K.H.
ɗan Shamma mutumin Harar, da Ahiyam, ɗan Sharar mutumin Harod.
- 2 Sama’ila 23:34kusan 1055 K.H.
Elifelet, ɗan Ahasbai mutumin Ma’aka, Eliyam, ɗan Ahitofel mutumin Gilo,
- 2 Sama’ila 23:35kusan 1055 K.H.
Hezro, mutumin Karmel, Fa’arai, mutumin Arbi,
- 2 Sama’ila 23:36kusan 1055 K.H.
Igal, ɗan Natan mutumin Zoba, ɗan Hagiri,
- 2 Sama’ila 23:37kusan 1055 K.H.
Zelek, mutumin Ammon Naharai, mutumin Beyerot mai ɗaukan wa Yowab, ɗan Zeruhiya makamai,
- 2 Sama’ila 23:38kusan 1055 K.H.
Ira, mutumin Itra. Gareb, mutumin Itra,
- 2 Sama’ila 23:39kusan 1055 K.H.
da kuma Uriya, mutumin Hitti. Su talatin da bakwai ne duka.
- 2 Sama’ila 24:1kusan 1017 K.H.
Fushin Ubangiji ya sāke ƙuna a kan Isra’ila, sai ya zuga Dawuda, yana cewa, “Je ka ƙidaya Isra’ila da Yahuda.”
- 2 Sama’ila 24:2kusan 1017 K.H.
Saboda haka sarki ya ce wa Yowab da komandodin da suke tare da shi, “Tafi cikin dukan kabilan Isra’ila, daga Dan har zuwa Beyersheba, ku ƙidaya mayaƙa don in san yawansu.”
- 2 Sama’ila 24:3kusan 1017 K.H.
Amma Yowab ya ce wa sarki, “Ubangiji Allahnka ya sa mayaƙan su ƙaru sau ɗari fiye da yadda suke, har ranka yă daɗe, sarki yă gani da idonsa. Me ya sa ranka yă daɗe, sarki yake so yă yi abu haka?”
- 2 Sama’ila 24:4kusan 1017 K.H.
Duk da haka, maganar sarki ya rinjayi Yowab da komandodin soja, sai suka tashi daga gaban sarki, suka tafi su ƙirga mayaƙan Isra’ila.
- 2 Sama’ila 24:5kusan 1017 K.H.
Bayan suka ƙetare Urdun, sai suka yi sansani kusa da Arower, kudu da garin da yake cikin kwari, sa’an nan suka ratsa ta wajen Gad, suka ci gaba zuwa Yazer.