Tsallake zuwa abun ciki

circa 2100–1900 BC

Abraham: The Covenant

God calls Abram from Ur, establishes an everlasting covenant, and promises a son through whom all nations will be blessed.

394 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 13:6kusan 1918 K.H.

    Wannan ya sa har ƙasar ba tă ishe su yayinda suke zama tare ba, saboda mallakarsu ta yi yawa har ba za su iya zama tare ba.

  2. Farawa 13:7kusan 1918 K.H.

    Rikici kuma ya tashi tsakanin masu kiwon dabbobin Abram da na Lot. Mazaunan ƙasar, a lokacin kuwa Kan’aniyawa da Ferizziyawa ne.

  3. Farawa 13:8kusan 1918 K.H.

    Saboda haka Abram ya ce wa Lot, “Kada mu bar rikici yă shiga tsakaninmu, ko kuma tsakanin masu kiwon dabbobinka da nawa, gama mu ’yan’uwa ne.

  4. Farawa 13:9kusan 1918 K.H.

    Ba ga dukan ƙasar tana gabanka ba? Bari mu rabu. In ka yi hagu sai ni in yi dama. In ka yi dama, sai ni in yi hagu.”

  5. Farawa 13:10kusan 1918 K.H.

    Lot ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, sai ya ga kwarin yana da ciyawa mai kyau ƙwarai sai ka ce lambun Ubangiji, kamar ƙasar Masar, wajajen Zowar. (Wannan fa kafin Ubangiji yă hallaka Sodom da Gomorra.)

  6. Farawa 13:11kusan 1917 K.H.

    Saboda haka sai Lot ya zaɓar wa kansa dukan kwarin Urdun, ya tashi ya nufi wajen gabas. Haka fa suka rabu da juna.

  7. Farawa 13:12kusan 1917 K.H.

    Abram ya zauna a ƙasar Kan’ana, yayinda Lot ya zauna cikin biranen kwari, ya kafa tentunansa kusa da Sodom.

  8. Farawa 13:13kusan 1917 K.H.

    Mutanen Sodom kuwa mugaye ne, sun aikata zunubi ƙwarai ga Ubangiji.

  9. Farawa 13:14kusan 1917 K.H.

    Bayan Lot ya rabu da Abram, sai Ubangiji ya ce wa Abram, “Ɗaga idanunka daga inda kake, ka dubi arewa da kudu, gabas da yamma.

  10. Farawa 13:15kusan 1917 K.H.

    Dukan ƙasar da kake gani zan ba ka, kai da zuriyarka har abada.

  11. Farawa 13:16kusan 1917 K.H.

    Zan sa zuriyarka tă yi yawa kamar ƙurar ƙasa, har in wani yana iya ƙidaya ƙurar, to, za a iya ƙidaya zuriyarka.

  12. Farawa 13:17kusan 1917 K.H.

    Tafi, ka ratsa tsawo da fāɗin ƙasar, gama zan ba ka ita.”

  13. Farawa 13:18kusan 1917 K.H.

    Saboda haka Abram ya cire tentunansa, ya zo ya zauna kusa da manyan itatuwan Mamre a Hebron, inda ya gina bagade ga Ubangiji.

  14. Farawa 14:1kusan 1913 K.H.

    A zamanin Amrafel sarkin Shinar, shi da Ariyok sarkin Ellasar, Kedorlayomer sarkin Elam, da kuma Tidal sarkin Goyim

  15. Farawa 14:2kusan 1913 K.H.

    suka tafi don su yaƙi Bera sarkin Sodom, Birsha sarkin Gomorra, Shinab sarkin Adma, Shemeber sarkin Zeboyim, da kuma sarkin Bela (wato, Zowar).

  16. Farawa 14:3kusan 1913 K.H.

    Dukan waɗannan sarakuna na bayan nan suka haɗa kai a Kwarin Siddim (Teku Gishiri).

  17. Farawa 14:4kusan 1913 K.H.

    Shekara goma sha biyu suna bauta wa Kedorlayomer, amma a shekara ta sha uku sai suka yi tawaye.

  18. Farawa 14:5kusan 1913 K.H.

    A shekara ta goma sha huɗu, Kedorlayomer da sarakunan da suka haɗa kai da shi suka tafi suka cinye Refahiyawa a Ashterot Karnayim, Zuziyawa a Ham, Emawa a Shabe Kiriyatayim,

  19. Farawa 14:6kusan 1913 K.H.

    da Horiyawa a ƙasar tudun Seyir har zuwa El Faran kusa da hamada.

  20. Farawa 14:7kusan 1913 K.H.

    Sa’an nan suka juya suka tafi En Mishfat (wato, Kadesh), suka cinye dukan ƙasar Amalekawa, da kuma Amoriyawa waɗanda suke zaune a Hazazon Tamar.

  21. Farawa 14:8kusan 1913 K.H.

    Sai sarkin Sodom, sarkin Gomorra, sarkin Adma, sarkin Zeboyim da sarkin Bela (wato, Zowar), suka fita suka ja dāgā a Kwarin Siddim

  22. Farawa 14:9kusan 1913 K.H.

    gāba da Kedorlayomer sarkin Elam, Tidal sarkin Goyim, Amrafel sarkin Shinar da Ariyok sarkin Ellasar; sarakuna huɗu gāba da biyar.

  23. Farawa 14:10kusan 1913 K.H.

    Kwarin Siddim kuwa ya cika da ramummukan kwalta, sa’ad da sarakunan Sodom da Gomorra suka gudu kuwa, waɗansu mutane suka fāɗa cikin ramummukan kwaltan, sauran kuwa suka gudu zuwa tuddai.

  24. Farawa 14:11kusan 1913 K.H.

    Sarakunan nan huɗu suka washe dukan kayayyakin Sodom da Gomorra, da kuma dukan abincinsu, sa’an nan suka tafi.

  25. Farawa 14:12kusan 1913 K.H.

    Suka kuma kama Lot ɗan ɗan’uwan Abram, wanda yake zaune a Sodom, da kayayyakinsa, suka yi tafiyarsu.