Tsallake zuwa abun ciki

circa 2100–1900 BC

Abraham: The Covenant

God calls Abram from Ur, establishes an everlasting covenant, and promises a son through whom all nations will be blessed.

394 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 14:13kusan 1913 K.H.

    Sai wani wanda ya tsira, ya zo ya faɗa wa Abram mutumin Ibraniyawa. Abram kuwa yana zama kusa da manyan itatuwan Mamre, Mamre mutumin Amoriyawa ne ɗan’uwan Eshkol da Aner, su kuwa abokan Abram ne.

  2. Farawa 14:14kusan 1913 K.H.

    Da Abram ya ji cewa an kama danginsa, sai ya tara horarrun mutane 318, da aka haifa a gidansa, ya bi sawun sarakunan da suka tafi da Lot, har Dan.

  3. Farawa 14:15kusan 1913 K.H.

    Da dad dare, Abram ya rarraba mutanensa don su fāɗa wa sarakunan nan, ya ɗibge su, ya kore su har zuwa Hoba, arewa da Damaskus.

  4. Farawa 14:16kusan 1913 K.H.

    Ya washe su da kuma dukan kayayyakinsu, ya kuma dawo da Lot danginsa da mallakarsa, tare da mata da sauran mutane.

  5. Farawa 14:17kusan 1913 K.H.

    Bayan Abram ya dawo daga cin Kedorlayomer da sarakunan da suka haɗa kai da shi a yaƙi, sai sarkin Sodom ya fito don yă tarye Abram a Kwarin Shabe (wato, Kwarin Sarki).

  6. Farawa 14:18kusan 1913 K.H.

    Sai Melkizedek sarkin Salem ya kawo burodi da ruwan inabi. Shi firist ne na Allah Mafi Ɗaukaka,

  7. Farawa 14:19kusan 1913 K.H.

    ya albarkaci Abram yana cewa, “Allah Mafi Ɗaukaka Mahaliccin sama da ƙasa yă albarkace Abram.

  8. Farawa 14:20kusan 1913 K.H.

    Kuma albarka ta tabbata ga Allah Mafi Ɗaukaka wanda ya ba da maƙiyanka a hannunka.” Sa’an nan Abram ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na kome.

  9. Farawa 14:21kusan 1913 K.H.

    Sarkin Sodom ya ce wa Abram, “Ka ba ni mutanena da ka ƙwace daga hannun sarakunan nan kawai, ka riƙe kayayyakin don kanka.”

  10. Farawa 14:22kusan 1913 K.H.

    Amma Abram ya ce, wa sarkin Sodom, “Na ɗaga hannu ga Ubangiji Allah Mafi Ɗaukaka, Mahaliccin sama da ƙasa, na riga na rantse

  11. Farawa 14:23kusan 1913 K.H.

    cewa ba zan karɓi kome da yake naka ba, ko zare ko maɗaurin takalma, don kada ka ce, ‘Na azurta Abram.’

  12. Farawa 14:24kusan 1913 K.H.

    Ba zan karɓi kome ba, sai dai abin da mutanena suka ci da kuma rabon mutanen da suka tafi tare da ni, ga Aner, Eshkol, da Mamre. Bari su ɗauki rabonsu.”

  13. Farawa 15:1kusan 1911 K.H.

    Bayan wannan, maganar Ubangiji ta zo wa Abram cikin mafarki cewa, “Kada ka ji tsoro, Abram. Ni ne garkuwarka, kuma ladanka zai zama mai girma.”

  14. Farawa 15:2kusan 1911 K.H.

    Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mene ne za ka ba ni, ganin cewa ba na haihuwa, wanda kuma zai gāji gādon gidana shi ne Eliyezer mutumin Damaskus?”

  15. Farawa 15:3kusan 1911 K.H.

    Abram ya kuma ce, “Ga shi ba ka ba ni ɗa ba, don haka bawan da aka haifa a gidana ne zai zama magājina.”

  16. Farawa 15:4kusan 1911 K.H.

    Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo gare shi cewa, “Wannan mutum ba zai zama magājinka ba, ɗa da yake zuwa daga jikinka ne zai zama magājinka.”

  17. Farawa 15:5kusan 1911 K.H.

    Sai Ubangiji ya fito da kai shi waje ya ce, “Ka dubi sammai ka kuma ƙirga taurari, in har za ka iya ƙirga su.” Sa’an nan ya ce masa, “Haka zuriyarka za tă zama.”

  18. Farawa 15:6kusan 1911 K.H.

    Abram ya gaskata, Ubangiji kuma ya lasafta shi adalci ga Abram.

  19. Farawa 15:7kusan 1911 K.H.

    Ubangiji ya kuma ce wa Abram, “Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da kai daga Ur na Kaldiyawa, domin in ba ka wannan ƙasa ka mallake ta.”

  20. Farawa 15:8kusan 1911 K.H.

    Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, yaya zan san cewa zan mallake ta?”

  21. Farawa 15:9kusan 1911 K.H.

    Saboda haka Allah ya ce masa, “Kawo mini karsana, akuya, da kuma rago kowanne yă kasance shi shekara uku ne, da kurciya da kuma ɗan tattabara.”

  22. Farawa 15:10kusan 1911 K.H.

    Abram ya kawo waɗannan duka a gaban Allah, ya raba kowannensu a tsakiya, ya ajiye su gab da juna, amma bai tsaga tsuntsayen a tsaka ba.

  23. Farawa 15:11kusan 1911 K.H.

    Sai tsuntsaye masu cin nama suka sauko a kan gawawwakin, amma Abram ya kore su.

  24. Farawa 15:12kusan 1911 K.H.

    Yayinda rana tana fāɗuwa, sai Abram ya yi barci mai zurfi, sai wani duhu mai kauri mai kuma bantsoro ya rufe shi.

  25. Farawa 15:13kusan 1911 K.H.

    Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka sani tabbatacce cewa shekaru ɗari huɗu, zuriyarka za tă zama baƙi a ƙasar da ba tasu ba, za a mai da su bayi, a kuma wulaƙanta su.