Tsallake zuwa abun ciki

circa 2100–1900 BC

Abraham: The Covenant

God calls Abram from Ur, establishes an everlasting covenant, and promises a son through whom all nations will be blessed.

394 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 22:2kusan 1872 K.H.

    Sai Allah ya ce, “Ka ɗauki ɗanka, makaɗaicin ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi yankin Moriya, ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa a can a kan ɗaya daga cikin duwatsun da zan nuna maka.”

  2. Farawa 22:3kusan 1872 K.H.

    Kashegari da sassafe, Ibrahim ya tashi ya ɗaura wa jakinsa sirdi. Ya ɗauki bayinsa biyu, da ɗansa Ishaku. Bayan ya faskare isashen itace saboda hadaya ta ƙonawa sai ya kama hanya zuwa wurin da Allah ya faɗa masa.

  3. Farawa 22:4kusan 1872 K.H.

    A rana ta uku Ibrahim ya ɗaga ido sai ya ga wurin daga nesa.

  4. Farawa 22:5kusan 1872 K.H.

    Ibrahim ya ce wa bayinsa, “Ku tsaya a nan da jakin, ni da yaron kuwa mu haura can. Za mu yi sujada sa’an nan mu komo wurinku.”

  5. Farawa 22:6kusan 1872 K.H.

    Ibrahim ya ɗauki itace saboda hadaya ta ƙonawa ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuwa ya riƙe wuƙa da wutar. Yayinda su biyun suke tafiya,

  6. Farawa 22:7kusan 1872 K.H.

    sai Ishaku ya yi tambaya, ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba?” Ibrahim ya ce masa, “Na’am ɗana!” Ishaku ya ce, “Ga dai wuta, ga kuma itace, amma ina ɗan ragon hadaya ta ƙonawa?”

  7. Farawa 22:8kusan 1872 K.H.

    Ibrahim ya amsa ya ce, “Ɗana, Allah kansa zai tanada ɗan ragon hadayar ƙonawa.” Sai su biyu suka ci gaba da tafiya.

  8. Farawa 22:9kusan 1872 K.H.

    Sa’ad da suka isa wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya kuma shisshirya itacen a kai. Ya ɗaura ɗansa Ishaku, ya kwantar da shi a kan itacen, a bisa bagaden.

  9. Farawa 22:10kusan 1872 K.H.

    Sa’an nan Ibrahim ya miƙa hannunsa ya ɗauki wuƙar don yă yanka ɗansa.

  10. Farawa 22:11kusan 1872 K.H.

    Amma mala’ikan Ubangiji ya kira shi daga sama ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!” Sai Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.”

  11. Farawa 22:12kusan 1872 K.H.

    Mala’ikan ya ce, “Kada ka yi wa yaron nan rauni. Kada kuma ka ji masa ciwo. Yanzu na san cewa kana tsoron Allah, gama ba ka hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba.”

  12. Farawa 22:13kusan 1872 K.H.

    Ibrahim ya ɗaga ido, ya duba, sai ya ga rago da ƙahoninsa a kafe a wani ɗan kurmi. Sai Ibrahim ya tafi ya kamo ragon ya miƙa shi hadaya ta ƙonawa a maimakon ɗansa.

  13. Farawa 22:14kusan 1872 K.H.

    Ibrahim kuwa ya ba wa wurin suna, Ubangiji Zai Tanada. Gama kamar yadda ake ce har yă zuwa yau, “A bisan dutsen Ubangiji, za a tanada.”

  14. Farawa 22:15kusan 1872 K.H.

    Mala’ikan Ubangiji ya kira Ibrahim daga sama sau na biyu

  15. Farawa 22:16kusan 1872 K.H.

    ya ce, “Na rantse da kaina, in ji Ubangiji, domin ka yi wannan, ba ka kuwa hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba,

  16. Farawa 22:17kusan 1872 K.H.

    tabbatacce zan albarkace ka, zan kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar taurari a sararin sama, kamar kuma yashi a bakin teku. Zuriyarka za su mallaki biranen abokan gābansu,

  17. Farawa 22:18kusan 1872 K.H.

    ta wurin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka, domin ka yi mini biyayya.”

  18. Farawa 22:19kusan 1872 K.H.

    Sa’an nan Ibrahim ya koma wurin bayinsa, suka kuma kama hanya tare zuwa Beyersheba. Ibrahim kuwa ya yi zamansa a Beyersheba.

  19. Farawa 22:20kusan 1862 K.H.

    Bayan wani ɗan lokaci, sai aka faɗa wa Ibrahim cewa, “Ga shi, Milka ita ma ta haifa wa Nahor ɗan’uwanka, ’ya’ya maza;

  20. Farawa 22:21kusan 1862 K.H.

    ɗan fari shi ne Uz, ɗan’uwansa kuma Buz, Kemuwel (shi ne mahaifin Aram),

  21. Farawa 22:22kusan 1862 K.H.

    Kesed, Hazo, Fildash; Yidlaf, da kuma Betuwel.”

  22. Farawa 22:23kusan 1862 K.H.

    Betuwel ya haifi Rebeka. Milka ta haifa wa Nahor ɗan’uwan Ibrahim waɗannan ’ya’ya maza takwas.

  23. Farawa 22:24kusan 1862 K.H.

    Ban da haka ma, ƙwarƙwararsa, mai suna Reyuma, ta haifa masa ’ya’ya maza, Teba, Gaham, Tahash da kuma Ma’aka.

  24. Farawa 23:1kusan 1860 K.H.

    Saratu ta yi shekara ɗari da ashirin da bakwai a duniya.

  25. Farawa 23:2kusan 1860 K.H.

    Ta rasu a Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar Kan’ana, Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makokin Saratu, yana kuka saboda ita.