- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 2100–1900 BC
Abraham: The Covenant
God calls Abram from Ur, establishes an everlasting covenant, and promises a son through whom all nations will be blessed.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Farawa 21:11kusan 1893 K.H.
Al’amarin ya ɓata wa Ibrahim rai sosai domin zancen ya shafi ɗansa.
- Farawa 21:12kusan 1893 K.H.
Amma Allah ya ce wa Ibrahim, “Kada hankalinka yă tashi game da yaron nan da kuma baiwarka. Ka saurari duk abin da Saratu ta faɗa maka, saboda ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.
- Farawa 21:13kusan 1893 K.H.
Zan ba ɗan baiwan nan al’umma shi ma, domin shi zuriyarka ne.”
- Farawa 21:14kusan 1892 K.H.
Kashegari da sassafe sai Ibrahim ya ɗauki abinci da salkar ruwa, ya ba wa Hagar. Ya ɗora su a kafaɗunta, sa’an nan ya sallame ta da yaron. Ta kama hanyarta ta kuma yi ta yawo a cikin jejin Beyersheba.
- Farawa 21:15kusan 1892 K.H.
Sa’ad da ruwan da yake cikin salkan ya ƙare, sai ta ajiye yaron a ƙarƙashin wani ƙaramin itace.
- Farawa 21:16kusan 1892 K.H.
Sai ta tafi, ta zauna ɗan nesa da yaron, misalin nisan harbin baka, gama ta yi tunani ta ce, “Ba zan iya kallon yaron yana mutuwa ba.” Da ta zauna nesa da yaron, sai ta fara kuka.
- Farawa 21:17kusan 1892 K.H.
Allah kuwa ya ji yaron yana kuka, sai mala’ikan Allah ya kira Hagar daga sama ya ce mata, “Mene ne damuwarki, Hagar? Kada ki ji tsoro, Allah ya ji yaron yana kuka yayinda yake kwance a can.
- Farawa 21:18kusan 1892 K.H.
Ki ɗaga yaron ki riƙe shi a hannu, gama zan mai da shi al’umma mai girma.”
- Farawa 21:19kusan 1892 K.H.
Sa’an nan Allah ya buɗe idanunta ta ga wata rijiyar ruwa. Don haka sai ta tafi ta cika salkan da ruwa, ta kuma ba wa yaron ruwa ya sha.
- Farawa 21:20kusan 1892 K.H.
Allah ya kasance da yaron, yayinda yake girma. Ya yi zama a jeji, ya kuma zama maharbi.
- Farawa 21:21kusan 1892 K.H.
Yayinda yake zama a Jejin Faran, sai mahaifiyarsa ta samo masa mata daga Masar.
- Farawa 21:22kusan 1886 K.H.
A lokacin nan Abimelek da Fikol, komandan rundunoninsa suka zo suka ce wa Ibrahim, “Allah yana tare da kai a ko mene ne kake yi.
- Farawa 21:23kusan 1886 K.H.
Yanzu ka rantse mini a nan a gaban Allah cewa, ba za ka yaudare ni ko ’ya’yana ko kuma zuriyata ba. Ka nuna mini alheri, kai da ƙasar da kake zama baƙunci kamar yadda na nuna maka.”
- Farawa 21:24kusan 1886 K.H.
Ibrahim ya ce, “Na rantse.”
- Farawa 21:25kusan 1886 K.H.
Sa’an nan Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek game da rijiyar ruwan da bayin Abimelek suka ƙwace.
- Farawa 21:26kusan 1886 K.H.
Sai Abimelek ya ce, “Ban san wanda ya yi wannan ba. Ba ka faɗa mini ba, ban kuwa taɓa ji ba, sai yau.”
- Farawa 21:27kusan 1886 K.H.
Sai Ibrahim ya kawo tumaki da shanu ya ba wa Abimelek, sai su biyun suka yi yarjejjeniya.
- Farawa 21:28kusan 1886 K.H.
Ibrahim ya ware ’yan raguna bakwai daga cikin garke,
- Farawa 21:29kusan 1886 K.H.
sai Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Mene ne ma’anar ’yan raguna bakwai da ka keɓe?”
- Farawa 21:30kusan 1886 K.H.
Ibrahim ya amsa ya ce, “Ka karɓi waɗannan ’yan tumaki bakwai daga hannuna a matsayin shaida cewa ni ne na haƙa wannan rijiya.”
- Farawa 21:31kusan 1886 K.H.
Saboda haka aka kira wurin Beyersheba, domin a nan ne su biyun suka yi rantsuwa.
- Farawa 21:32kusan 1886 K.H.
Bayan da aka yi yarjejjeniya a Beyersheba, sai Abimelek da Fikol, komandan rundunoninsa suka koma ƙasar Filistiyawa.
- Farawa 21:33kusan 1886 K.H.
Sai Ibrahim ya shuka itacen tsamiya a Beyersheba, a can kuma ya kira bisa sunan Ubangiji, Allah Madawwami.
- Farawa 21:34kusan 1886 K.H.
Ibrahim kuwa ya zauna a ƙasar Filistiyawa na dogon lokaci.
- Farawa 22:1kusan 1872 K.H.
Bayan abubuwan nan suka faru, sai Allah ya gwada Ibrahim. Ya ce masa, “Ibrahim!” Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.”