- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 2100–1900 BC
Abraham: The Covenant
God calls Abram from Ur, establishes an everlasting covenant, and promises a son through whom all nations will be blessed.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Farawa 20:4kusan 1897 K.H.
Abimelek dai bai riga ya kusace ta ba tukuna, saboda haka ya ce, “Ya Ubangiji za ka hallaka al’umma marar laifi?
- Farawa 20:5kusan 1897 K.H.
Ba shi ne ya ce mini, ‘Ita ’yar’uwata ba ce,’ ita ma ba tă ce, ‘Shi ɗan’uwana ba ne’? Na yi haka da kyakkyawan nufi da hannuwa masu tsabta.”
- Farawa 20:6kusan 1897 K.H.
Sai Allah ya ce masa a cikin mafarki “I, na san ka yi wannan da kyakkyawan nufi, saboda haka ne na kiyaye ka daga yin mini zunubi. Shi ya sa ban bar ka ka taɓa ta ba.
- Farawa 20:7kusan 1897 K.H.
Yanzu ka komar da matar mutumin, gama shi annabi ne, zai kuma yi maka addu’a, za ka kuwa rayu. In ba ka komar da ita ba fa, ka sani tabbatacce kai da dukan abin da yake naka za ku mutu.”
- Farawa 20:8kusan 1897 K.H.
Kashegari da sassafe, sai Abimelek ya tara dukan fadawansa, ya faɗa musu duk abin da ya faru, suka ji tsoro ƙwarai da gaske.
- Farawa 20:9kusan 1897 K.H.
Sa’an nan Abimelek ya kira Ibrahim ciki ya ce, “Me ke nan ka yi mana? Ta wace hanya ce na yi maka laifi har da ka kawo irin wannan babban laifi a kaina da kuma masarautata? Ka yi mini abubuwan da bai kamata a yi ba.”
- Farawa 20:10kusan 1897 K.H.
Abimelek ya kuma ce wa Ibrahim, “Me ya sa ka yi wannan?”
- Farawa 20:11kusan 1897 K.H.
Ibrahim ya ce, “Na ce a raina, ‘Tabbatacce babu tsoron Allah a wannan wuri, za su kuwa kashe ni saboda matata.’
- Farawa 20:12kusan 1897 K.H.
Ban da haka, tabbatacce ita ’yar’uwata ce, ’yar mahaifina, ko da yake ba daga uwata ba, ta kuma zama matata.
- Farawa 20:13kusan 1897 K.H.
Sa’ad da Allah ya sa na tashi daga gidan mahaifina na ce mata, ‘Wannan shi ne yadda za ki nuna mini ƙaunarki. Duk inda muka tafi, ki ce game da ni, “Shi ɗan’uwana ne.” ’ ”
- Farawa 20:14kusan 1897 K.H.
Sai Abimelek ya kawo awaki da shanu da bayi maza da mata, ya ba wa Ibrahim, ya kuma komar da Saratu matarsa gare shi.
- Farawa 20:15kusan 1897 K.H.
Abimelek ya kuma ce, “Ƙasata tana gabanka, ka zauna a duk inda kake so.”
- Farawa 20:16kusan 1897 K.H.
Ga Saratu kuwa ya ce, “Ina ba wa ɗan’uwanki shekel dubu na azurfa, shaida ce ta tabbatarwa a idanun dukan waɗanda suke tare da ke, da kuma a gaban kowa cewa ba ki da laifi.”
- Farawa 20:17kusan 1897 K.H.
Sai Ibrahim ya yi addu’a ga Allah, Allah kuma ya warkar da Abimelek, da matarsa da bayinsa mata domin su haihu,
- Farawa 20:18kusan 1897 K.H.
gama Ubangiji ya rufe kowace mahaifa a gidan Abimelek saboda Saratu, matar Ibrahim.
Ana nan sai Ubangiji ya nuna wa Saratu alheri kamar yadda ya ce, Ubangiji kuma ya yi wa Saratu abin da ya yi alkawari.
Saratu ta yi ciki, ta kuma haifa wa Ibrahim ɗa a tsufansa; a daidai lokacin da Allah ya yi masa alkawari.
Ibrahim ya sa wa ɗan da Saratu ta haifa masa suna Ishaku.
Sa’ad da ɗansa Ishaku ya kai kwana takwas da haihuwa, sai Ibrahim ya yi masa kaciya, kamar yadda Allah ya umarce shi.
Ibrahim yana da shekara ɗari, sa’ad da aka haifa masa ɗansa Ishaku.
Saratu ta ce, “Allah ya sa na yi dariya, kuma duk wanda ya ji game da wannan, zai yi dariya tare da ni.”
Ta kuma ƙara da cewa, “Dā, wa zai iya ce wa Ibrahim, Saratu za tă yi renon yara? Duk da haka na haifar masa ɗa cikin tsufansa.”
- Farawa 21:8kusan 1893 K.H.
Yaron ya yi girma, aka kuma yaye shi, a ranar da aka yaye shi kuwa, Ibrahim ya yi babban biki.
- Farawa 21:9kusan 1893 K.H.
Amma Saratu ta ga cewa yaron da Hagar, mutuniyar Masar ta haifa wa Ibrahim yana wa ɗanta Ishaku gori,
- Farawa 21:10kusan 1893 K.H.
sai ta ce wa Ibrahim, “Ka kori baiwan nan tare da ɗanta, saboda ɗan baiwan nan ba zai taɓa raba gādo da ɗana Ishaku ba.”