Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Temptation

346 ayoyi · 52 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Na lulluɓe gadona da lili masu launi dabam-dabam daga Masar.

  2. Na yayyafa turare a gadona da mur, aloyes da kuma kirfa.

  3. Zo, mu sha zurfin ƙauna har safe; bari mu ji wa ranmu daɗi da ƙauna!

  4. Mijina ba ya gida; ya yi tafiya mai nisa.

  5. Ya ɗauki jakarsa cike da kuɗi ba zai kuwa dawo gida ba sai tsakiyar wata.”

  6. Da kalmomin rarrashi ta sa ya kauce; ta ɗauki hankalinsa da sulɓin maganarta.

  7. Nan take, ya bi ta kamar saniyar da za a kai mayanka, kamar wawa zuwa wurin da za a ba shi horo

  8. sai da kibiya ta soki hantarsa, kamar tsuntsun da ya ruga cikin tarko, ba tare da sani zai zama sanadin ransa ba.

  9. tana kira ga masu wucewa, waɗanda suke tafiya kai tsaye a hanyarsu.

  10. “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo cikin nan!” Tana ce wa marasa hankali.

  11. “Ruwan da aka sata ya fi daɗi; abincin da aka ci a ɓoye ya fi daɗi!”

  12. Adali yakan yi hankali a abokantaka, amma hanyar mugaye kan kai su ga kaucewa.

  13. Koyarwar mai hikima maɓulɓulan rai ne, mai juyar da mutum daga tarkon mutuwa.

  14. Tsoron Ubangiji shi ne maɓulɓular rai yakan juye mutum daga tarkon mutuwa.

  15. Mutum mai tā-da-na-zaune-tsaye yakan ruɗi maƙwabcinsa ya kai shi a hanyar da ba ta da kyau.

  16. In ka daina jin umarni, ɗana, za ka kuwa kauce daga kalmomin sani.

  17. Duk wanda ya jagorance masu aikata gaskiya a hanyar mugunta zai fāɗa cikin tarkonsa amma marasa abin zargi za su sami gādo mai kyau.

  18. Mutum mai aminci zai cika da albarka, amma duk mai son yin arziki dare ɗaya zai sha hukunci.

  19. In ba haka ba, zan wadace in ƙi ka har in ce, ‘Wane ne Ubangiji?’ Ko kuwa in zama matalauci in yi sata ta haka in kunyata sunan Allahna.

  20. Sai na iske wani abin da ya fi mutuwa ɗaci mace wadda take tarko ne, wadda zuciyarta tarko ne wadda kuma hannuwanta sarƙa ne. Mutumin da ya gamshi Allah zai tsere mata, amma za tă kama mai zunubi.

  21. Shi da yake tafiya cikin adalci yana kuma magana abin da yake daidai, wanda yake ƙin riba daga cuta yana kuma kiyaye hannunsa daga karɓan cin hanci, wanda yake hana kunnuwansa daga ƙulla kisa ya kuma rufe idanunsa a kan tunanin aikata mugunta,

  22. shi ne mutumin da zai zauna a bisa, wanda mafakarsa za tă zama kagarar dutse. Za a tanada abincinsa, kuma ruwa ba zai kāsa masa ba.

  23. kamar jakar jejin da ta saba da hamada, mai busar iska cikin son barbaranta sa’ad da take son barbara wa zai iya hana ta? Jakin da yake nemanta, ba ya bukatar wahalar da kansa; a lokacin barbara za a same ta.

  24. Kada ka yi gudu har ƙafafunka su zama ba takalma maƙogwaronka kuma ya bushe. Amma sai ka ce, ‘Ba amfani! Ina ƙaunar baƙin alloli kuma dole in bi su.’

  25. Sai na ajiye ƙwarya cike da ruwan inabi da waɗansu kwaf a gaban iyalin Rekabawan na kuma ce musu, “Ku sha ruwan inabin.”