Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Temptation

346 ayoyi · 52 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ka bishe ni da shawararka, bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka.

  2. Wa nake da shi a sama in ba kai ba? Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai.

  3. Jikina da zuciyata za su iya raunana, amma Allah ne ƙarfin zuciyata da kuma rabona har abada.

  4. Da ba don Ubangiji ya yi mini taimako ba, da tuni na zauna shiru a wurin mutuwa.

  5. Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,” ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni.

  6. Na kiyaye ƙafafuna daga kowace muguwar hanya domin in yi biyayya da maganarka.

  7. Mugaye sun kafa mini tarko, amma ban kauce daga farillanka ba.

  8. Waɗanda suke ƙaunar dokarka suna da babban salama, kuma babu abin da zai sa su yi tuntuɓe.

  9. Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka, kada ka yarda.

  10. In suka ce, “Zo mu tafi; mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe, mu fāɗa wa marasa laifi;

  11. mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami;

  12. za mu sami dukiya masu daraja iri-iri, mu kuma cika gidajenmu da ganima;

  13. ka haɗa kai da mu, za mu kuwa raba abin da muka sato”

  14. ɗana, kada ka tafi tare da su, kada ka taka ƙafarka a hanyarsu;

  15. gama ƙafafunsu kan yi sauri ga yin zunubi, suna saurin yin kisankai.

  16. Ba shi da amfani a kafa tarko a idanun dukan tsuntsaye!

  17. Gama hikima za tă shiga cikin zuciyarka, sani kuma zai faranta maka rai.

  18. Tsinkaya za tă tsare ka, ganewa kuma za tă yi maka jagora.

  19. Hikima za tă cece ka daga hanyoyin mugayen mutane, daga kalmomin mutane masu ɓatanci,

  20. Zai kiyaye ku kuma daga mazinaciya, daga mace mai lalata, mai ƙoƙarin kama ka da daɗin bakinta,

  21. Kada ka sa ƙafa a kan hanyar mugaye kada ka bi gurbin mugaye.

  22. Ka guji mugunta, kada ka yi tafiya a kanta; juya daga gare ta ka yi tafiyarka.

  23. Ba ta wani tunanin rayuwa; hanyoyinta karkatacce ne, amma ba tă sani ba.

  24. Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; kada ku juye daga abin da nake faɗa.

  25. Ku yi nesa da hanyarta, kana ku je kusa da ƙofar gidanta,