Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Temptation: General references

224 ayoyi · 52 fannoni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”

  2. Macen ta ce wa macijin, “Za mu iya ci daga ’ya’ya itatuwa a lambun,

  3. amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ”

  4. Maciji ya ce wa macen, “Tabbatacce ba za ku mutu ba.

  5. Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.”

  6. Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci.

  7. Sa’an nan idanun dukansu biyu suka buɗe, suka kuma gane tsirara suke; saboda haka suka ɗinɗinka ganyayen ɓaure suka yi wa kansu sutura.

  8. Da mutumin da matarsa suka ji motsin Ubangiji Allah yana takawa a lambun a sanyin yini, sai suka ɓuya daga Ubangiji Allah a cikin itatuwan lambu.

  9. Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin ya ce, “Ina kake?”

  10. Ya ce, “Na ji ka a cikin lambu, na kuwa ji tsoro gama ina tsirara, saboda haka na ɓuya.”

  11. Sai ya ce, “Wa ya faɗa maka cewa kana tsirara? Ko dai ka ci daga itacen da na umarce ka kada ka ci ne?”

  12. Mutumin ya ce, “Macen da ka sa a nan tare da ni, ita ta ba ni waɗansu ’ya’ya daga itacen, na kuwa ci.”

  13. Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?” Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.”

  14. Sai Allah ya ce masa a cikin mafarki “I, na san ka yi wannan da kyakkyawan nufi, saboda haka ne na kiyaye ka daga yin mini zunubi. Shi ya sa ban bar ka ka taɓa ta ba.

  15. Ku kula, kada ku yi yarjejjeniya da waɗanda suke zaune a ƙasar da za ku tafi, in ba haka ba, za su zama muku tarko.

  16. Ku rurrushe bagadansu, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu, ku sassare ginshiƙan Asheransu.

  17. Kada ku bauta wa wani allah, gama Ubangiji, wanda sunansa Kishi, Allah ne mai kishi.

  18. “Ku kula, kada ku yi yarjejjeniya da mazaunan wannan ƙasa, don kada sa’ad da suke yi wa allolinsu sujada, suna miƙa musu hadaya, su gayyace ku, ku ci hadayar da suka miƙa wa allolinsu.

  19. Kada ku auro wa ’ya’yanku maza ’yan matansu, waɗanda suke yi wa alloli sujada, har su sa ’ya’yanku su bi allolinsu.

  20. Ku ƙone siffar allolinsu da wuta. Kada ku yi ƙyashin azurfa ko zinariyar da aka rufe allolin da ita, Kada ku kwashe su, don kada su zamar muku tarko, gama abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku.

  21. Ku yi hankali cewa ba ku manta da Ubangiji Allahnku, har ku kāsa kiyaye umarnansa, dokokinsa da ƙa’idodinsa da nake ba ku a wannan rana ba.

  22. To, sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sa’ad da kuka gina gidaje masu kyau, kuka zauna,

  23. sa’ad da kuma garkunanku na shanu da na tumaki suka ƙaru, azurfanku da zinariyarku kuma suka ƙaru, sa’an nan dukan abin da kuke da shi ya haɓaka,

  24. to, sai ku lura, kada ku ɗaukaka kanku, har ku manta da Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta kuma.

  25. Wataƙila ku ce wa kanku, “Ikona da ƙarfin hannuwana ne suka ba ni da wannan arziki.”