Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Temptation: Blessedness of those who meet and overcome
Ayoyi game da Blessedness of those who meet and overcome
Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku,
domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa.
Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba.
Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.