Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sin

210 ayoyi · 120 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Suna yin rayuwarsu cikin arziki kuma su mutu cikin salama.

  2. Duk da haka suna ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu.’ Ba ma so mu san hanyoyinka.

  3. Wane ne Maɗaukaki har da za mu bauta masa? Wace riba za mu samu ta wurin yin addu’a gare shi?

  4. Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah? Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki?

  5. in na ɓoye zunubina yadda mutane suke yi, ta wurin ɓoye laifina a cikin zuciyata,

  6. Sa’an nan sai ya zo wurin, wurin mutane ya ce, ‘Na yi zunubi, na kauce wa abin da yake daidai, amma ban samu abin da ya kamata in samu ba.

  7. Ka koya mini abin da ba zan iya gani ba; in na yi ba daidai ba, ba zan sāke yi ba.’

  8. Saboda haka na rena kaina na kuma tuba cikin ƙura da toka.”

  9. Cikin fushinku kada ku yi zunubi; sa’ad da kuke kan gadajenku, ku bincike zukatanku ku kuma yi shiru. Sela

  10. Yakan yi taƙama da ƙulle-ƙullen zuciyarsa; yana albarkaci mai haɗama yana kuma ƙin Ubangiji.

  11. Yakan ce wa kansa, “Ai, Allah ya manta; ya rufe fuskarsa ba ya gani.”

  12. Game da ayyukan mutane kuwa, ta wurin maganar leɓunanka na kiyaye kaina daga hanyoyin tashin hankali.

  13. Ka kiyaye bawanka daga zunubin ganganci; kada ka bari su yi mulki a kaina. Ta haka zan zama marar laifi; marar laifi na babban tawaye.

  14. Juyo daga mugunta ku yi alheri; nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.

  15. Saboda hasalarka babu lafiya a jikina; ƙasusuwana ba lafiya saboda zunubina.

  16. Na furta laifina; na damu da zunubina.

  17. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zabura ta Dawuda. Na ce, “Zan lura da hanyoyina zan kuma kiyaye harshena daga zunubi; zan sa linzami a bakina muddin mugaye suna a gabana.”

  18. Kun yi waɗannan abubuwa na kuwa yi shiru; kun ɗauka gaba ɗaya ni kamar ku ne. Amma zan tsawata muku in kuma zarge ku a fuskarku.

  19. Ka wanke dukan kurakuraina ka tsarkake ni daga zunubina.

  20. Tabbatacce ni mai zunubi ne tun haihuwa mai zunubi daga lokacin da mahaifiyata ta yi cikina.

  21. Sukan ƙarfafa juna a mugayen ƙulle-ƙullensu, sukan yi magana yadda za su ɓoye tarkunansu; su ce, “Wa zai gan su?”

  22. Da a ce na ji daɗin zunubi a zuciyata, da Ubangiji ba zai saurara ba;

  23. Ka tuna da yadda abokin gāba ya yi maka ba’a, ya Ubangiji, yadda wawaye suka ɓata sunanka.

  24. Amma suka ci gaba da yin masa zunubi, suna tayarwa a cikin hamada a kan Mafi Ɗaukaka.

  25. Ka ajiye laifinmu a gabanka, asirin zunubanmu a hasken kasancewarka.