Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sin

210 ayoyi · 120 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. In muka ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da shi maƙaryaci ke nan, maganarsa kuwa ba ta da wuri a cikinmu.

  2. Duk mai yin zunubi yana karya doka ne; tabbatacce, zunubi, karya doka ne.

  3. Sai dai kun san cewa Kiristi ya bayyana ne domin yă ɗauke zunubanmu. A cikinsa kuwa babu zunubi.

  4. Duk mai aikata abin da yake zunubi shi na Iblis ne, domin Iblis mai aikata zunubi ne tun farko. Dalilin da ya sa Ɗan Allah ya bayyana kuwa shi ne don yă rushe aikin Iblis.

  5. Babu haifaffe na Allah da zai ci gaba da yin zunubi, domin iri na Allah yana a cikinsa; ba zai iya ci gaba da yin zunubi ba, domin haifaffe ne na Allah.

  6. Duk rashin adalci, zunubi ne, amma akwai waɗansu zunuban da ba sa kai ga mutuwa.

  7. Mun san cewa kowane haifaffe na Allah ba ya cin gaba da yin zunubi; kasancewarsa haifaffe na Allah ita takan kāre shi, mugun kuwa ba zai iya cuce shi ba.

  8. gama zunubanta sun yi tsororuwa sun kai sama. Allah kuma ya tuna da laifofinta.

  9. Ku sāka mata kamar yadda ta sāka muku; ku sāka mata sau biyu na abin da ta yi. Ku dama mata sau biyu na abin da yake cikin kwaf nata.

  10. Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon.