Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sin: Tempt others to

8 ayoyi · 120 fannoni

Ayoyi game da Tempt others to

  1. Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci.

  2. “Na ɗaga ka daga ƙura na mai da kai shugaban mutanena Isra’ila, amma ka yi tafiya a hanyoyin Yerobowam, ka kuma sa mutanena Isra’ila suka yi zunubi, ka tsokane ni na yi fushi ta wurin zunubansu.

  3. (Babu wani mutum kamar Ahab, wanda ya ba da kansa ga aikata mugunta a gaban Ubangiji. Yezebel matarsa ce ta zuga shi.

  4. Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka, kada ka yarda.

  5. In suka ce, “Zo mu tafi; mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe, mu fāɗa wa marasa laifi;

  6. mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami;

  7. za mu sami dukiya masu daraja iri-iri, mu kuma cika gidajenmu da ganima;

  8. ka haɗa kai da mu, za mu kuwa raba abin da muka sato”