Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sin

210 ayoyi · 120 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Haka ku ma, ku ɗauke kanku matattu ne ga ikon zunubi amma rayayyu cikin tarayya da Allah cikin Kiristi Yesu.

  2. Ba ku sani ba cewa sa’ad da kuka miƙa kanku ga wani don ku yi masa biyayya a matsayin bayi, ko ku bayi ne ga zunubi, wanda yake kai ga mutuwa, ko kuwa ga biyayya, wadda take kai ga adalci, ashe, ba kun zama bayi ga wannan da kuke yi wa biyayya ba ke nan?

  3. An ’yanta ku daga zunubi, kun kuma zama bayi ga aikin adalci.

  4. Wace riba ce kuka samu a lokacin, daga abubuwan nan da yanzu suka zama muku abin kunya? Ƙarshen irin abubuwan nan dai, mutuwa ne!

  5. Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  6. Gama sa’ad da halin mutuntaka yake mulkinmu, sha’awace-sha’awacen zunubi waɗanda dokar ta zuga sun yi ta aiki a jikunanmu, don mu ba da amfani wa mutuwa.

  7. Me za mu ce ke nan? Dokar zunubi ce? Sam, ko kaɗan! Tabbatacce ai, da ban san mene ne zunubi ba in ba ta wurin doka ba. Gama da ban san mene ne ƙyashi yake ba tabbatacce in ba don doka ta ce, “Kada ka yi ƙyashi ba.”

  8. Amma zunubi, da ya sami dama ta wurin umarnin nan, ya haifar a cikina kowane halin ƙyashi iri-iri. Gama in babu doka, zunubi matacce ne.

  9. Gama zunubi, da ya sami dama ta wurin umarni, sai ya ruɗe ni, kuma ta wurin umarnin kuwa ya kashe ni.

  10. Abin nan da yana mai kyau, zai kawo mini mutuwa? Ko kaɗan! Amma domin zunubi ya bayyana kansa a matsayin zunubi, sai ya haifar da mutuwa a cikina ta wurin abin da yake mai kyau, domin ta wurin umarnin nan zunubi ya fito da matuƙar muninsa.

  11. Kamar dai yadda yake, ba ni kaina nake yinsa ba, sai dai zunubin da yake zaune a cikina ne.

  12. amma ina ganin wata doka tana aiki a gaɓoɓin jikina, tana yaƙi da dokar hankalina, tana kuma sa in zama ɗaurarren dokar zunubin da take aiki a gaɓoɓin jikina.

  13. Gama in kuna rayuwa bisa ga mutuntaka, za ku mutu; amma in ta wurin Ruhu kuka kashe ayyukan jikin nan, za ku rayu.

  14. Dole ƙauna tă zama ta gaskiya. Ku ƙi duk abin da yake mugu; ku manne wa abin da yake nagari.

  15. Amma wanda yake da shakka yakan jawo wa kansa hukunci ne in ya ci, domin yana ci ne ba bisa ga bangaskiya ba; kuma duk abin da bai zo daga bangaskiya ba zunubi ne.

  16. Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu,

  17. ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah.

  18. Zunubi ne yake ba wa mutuwa dafi, Doka kuma take ba wa zunubi iko.

  19. Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi kamar hadayar zunubi saboda mu, domin mu sami adalcin Allah ta wurinsa.

  20. Dukan waɗanda suka dogara ga kiyaye Doka la’anannu ne, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda bai ci gaba da yi dukan abubuwan da aka rubuta a Littafin Doka ba.”

  21. Amma Nassi ya kulle kome a ƙarƙashin ikon zunubi, domin abin da aka yi alkawarin nan, da ake bayar ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi, a ba da shi ga waɗanda suka gaskata.

  22. Gama mutuntaka yana son abin da Ruhu yake ƙi, Ruhu kuma yana son abin da mutuntaka yake ƙi. Waɗannan biyu kuwa gāba suke da juna, har ku kāsa yin abin da kuke so.

  23. Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata;

  24. bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya,

  25. da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.