- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jacob
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Sa’ad da ’yan’uwansa suka ga cewa mahaifinsu ya fi ƙaunarsa fiye da kowanne daga cikinsu, sai suka ƙi jininsa, ba sa kuma maganar alheri da shi.
Sai Yusuf ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa ’yan’uwansa. Ya ce, “Ku saurara, na sāke yin wani mafarki, a wannan lokaci, na ga rana da wata da taurari goma sha ɗaya suna rusuna mini.”
Sa’ad da ya faɗa wa mahaifinsa da kuma ’yan’uwansa, sai mahaifinsa ya kwaɓe shi ya ce, “Wanne irin mafarki ne haka da ka yi? Kana nufin ni da mahaifiyarka da ’yan’uwanka za mu zo gabanka mu rusuna maka?”
’Yan’uwansa suka yi kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe batun nan a zuciya.
Sa’an nan Yaƙub ya kyakkece tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya kuma yi makoki domin ɗansa kwanaki masu yawa.
Dukan ’ya’yansa maza da mata, suka zo don su ta’azantar da shi, amma ya ƙi yă ta’azantu. Ya ce, “A’a, cikin makoki zan gangara zuwa kabari wurin ɗana.” Saboda haka, mahaifin Yusuf ya yi kuka saboda shi.
Sa’ad da Yaƙub ya sami labari cewa akwai hatsi a Masar, sai ya ce wa ’ya’yansa maza, “Don me kuke duban juna kawai?”
Ya ci gaba, “Na ji cewa akwai hatsi a Masar. Ku gangara can ku sayo mana, domin mu rayu kada mu mutu.”
A yanzu, yunwa ta yi tsanani a ƙasar.
Saboda haka sa’ad da suka cinye dukan hatsin da suka kawo daga Masar, mahaifinsu ya ce musu, “Ku koma, ku sayo mana ƙarin abinci.”
Amma Yahuda ya ce masa, “Mutumin ya gargaɗe mu sosai cewa, ‘Ba za ku sāke ganin fuskata ba sai in ɗan’uwanku yana tare da ku.’
In za ka aika da ɗan’uwanmu tare da mu, za mu gangara mu sayo maka abinci.
Amma in ba za ka aika da shi ba, ba za mu gangara ba, gama mutumin ya ce mana, ‘Ba za ku sāke ganin fuskata ba sai ko in ɗan’uwanku yana tare da ku.’ ”
Isra’ila ya yi tambaya, “Me ya sa kuka kawo wannan damuwa a kaina ta wurin faɗa wa mutumin cewa kuna da wani ɗan’uwa?”
Suka amsa, “Mutumin ya yi mana tambaya sosai game da kanmu da iyalinmu. Ya tambaye mu, ‘Mahaifinku yana da rai har yanzu? Kuna da wani ɗan’uwa?’ Mu dai mun amsa tambayoyinsa ne. Ta yaya za mu sani zai ce, ‘Ku kawo ɗan’uwanku a nan’?”
Sa’an nan Yahuda ya ce wa Isra’ila mahaifinsa, “Ka aika saurayin tare da ni za mu kuwa tafi nan da nan, saboda mu da ’ya’yanmu mu rayu, kada mu mutu.
Ni kaina zan tabbatar da lafiyarsa; na ɗauki lamuninsa, a hannuna za ka neme shi. In ban dawo da shi gare ka, in sa shi nan a gabanka ba, zan ɗauki laifin a gabanka dukan kwanakina.
Ai, da ba mun jinkirta ba, da mun komo har sau biyu.”
Sa’an nan mahaifinsu Isra’ila ya ce musu, “In dole ne a yi haka, to, sai ku yi. Ku sa waɗansu amfani mafi kyau na ƙasar a buhunanku, ku ɗauka zuwa wurin mutumin a matsayin kyauta, da ɗan man ƙanshi na shafawa, da kuma ’yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta da kuma almon.
Ku ɗauki ninki biyu na yawan azurfa tare da ku, gama dole ku mayar da azurfan da aka sa a cikin bakunan buhunanku. Mai yiwuwa an yi haka a kuskure ne.
Ku ɗauki ɗan’uwanku kuma ku koma wurin mutumin nan da nan.
Bari Allah Maɗaukaki yă nuna muku alheri a gaban mutumin saboda yă bar ɗan’uwanku da Benyamin su dawo tare da ku. Ni kuwa, in na yi rashi, na yi rashi.”
Suka faɗa masa, “Yusuf yana da rai! Gaskiya, shi ne mai mulkin dukan Masar.” Gaban Yaƙub ya fāɗi, domin bai gaskata su ba.
Amma sa’ad da suka faɗa masa kome da Yusuf ya faɗa musu, da kuma sa’ad da ya ga wagonun da Yusuf ya aika don a ɗauke shi a kai da shi can, sai ya farfaɗo, ya dawo cikin hankalinsa.
Sai Yaƙub ya ce, “Na yarda! Ɗana Yusuf yana da rai har yanzu. Zan tafi in gan shi kafin in mutu.”