Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jacob: Esau seeks to slay, escapes to Padan-Aram

11 ayoyi · 49 fannoni

Ayoyi game da Esau seeks to slay, escapes to Padan-Aram

  1. Isuwa ya riƙe Yaƙub a zuciya saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Ya ce wa kansa, “Kwanakin mutuwar mahaifina sun yi kusa; sa’an nan zan kashe ɗan’uwana Yaƙub.”

  2. Sa’ad da aka faɗa wa Rebeka abin da babban ɗanta Isuwa ya faɗa, sai ta kira ɗanta Yaƙub ta ce masa, “Ɗan’uwanka Isuwa yana ta’azantar da kansa da tunanin kashe ka.

  3. To, fa, ɗana, yi abin da na ce; gudu nan take zuwa wurin ɗan’uwana Laban a Haran.

  4. Zauna tare da shi na ɗan lokaci sai ɗan’uwanka ya huce.

  5. Sa’ad da ɗan’uwanka ya daina fushi da kai, ya kuma manta da abin da ka yi masa, zan aika don ka dawo daga can. Don me zan rasa ku biyu a rana guda?”

  6. Sa’an nan Rebeka ta ce wa Ishaku, “Ni fa na gaji da matan Hittiyawan nan. In Yaƙub ya auri mata daga cikin matan ƙasan nan, wato, daga matan Hittiyawa irin waɗannan, rayuwata ba za tă daɗa mini kome ba.”

  7. Saboda haka Ishaku ya kira Yaƙub, ya kuma albarkace shi, sa’an nan ya umarce shi ya ce, “Kada ka auri mace daga Kan’ana.

  8. Tashi nan da nan ka tafi Faddan Aram, zuwa gidan mahaifin mahaifiyarka Betuwel. Ka ɗauko wa kanka mata a can daga cikin ’ya’ya matan Laban ɗan’uwan mahaifiyarka.

  9. Bari Allah Maɗaukaki yă albarkace ka, yă kuma sa ka yi ta haihuwa ka riɓaɓɓanya har ka zama ƙungiyar jama’o’i.

  10. Bari Allah yă ba ka da kuma zuriyarka albarkar da ya ba wa Ibrahim, don ka amshi ƙasar da kake baƙunci, ƙasar da Allah ya ba wa Ibrahim.”

  11. Sa’an nan Ishaku ya sallami Yaƙub, ya kuwa tafi Faddan Aram, zuwa wurin Laban ɗan Betuwel mutumin Aram. Laban ne ɗan’uwan Rebeka, wadda take mahaifiyar Yaƙub da Isuwa.