Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jacob: Prophecies concerning himself and descendants

15 ayoyi · 49 fannoni

Ayoyi game da Prophecies concerning himself and descendants

  1. Allah yă ba ka daga raɓar sama da kuma yalwar ƙasa, yalwar hatsi da sabon ruwan inabi.

  2. Bari al’ummai su bauta maka mutane kuma su rusuna maka. Ka zama shugaba a kan ’yan’uwanka bari kuma ’ya’yan mahaifiyarka su rusuna maka. Bari waɗanda suka la’anta ka, su la’antu; waɗanda kuma suka sa maka albarka, su sami albarka.”

  3. Yaƙub ya bar Beyersheba ya kama hanyar Haran.

  4. Sa’ad da ya kai wani wuri, sai ya dakata domin yă kwana, gama rana ta riga ta fāɗi. Ya ɗauki dutse daga cikin duwatsun wurin, ya sa shi ya zama matashin kansa, sa’an nan ya kwanta don yă yi barci.

  5. Ya yi mafarki inda ya ga wata matakalar hawa, tsaye a ƙasa, kanta ta kai sama, mala’ikun Allah kuwa suna hawa, suna sauka a kanta.

  6. A can bisantaUbangiji ya tsaya, ya kuma ce, “Ni ne Ubangiji Allah na mahaifinka Ibrahim da kuma Allah na Ishaku. Zan ba ka, kai da kuma zuriyarka, ƙasar da kake kwance a kai.

  7. Zuriyarka za tă zama kamar ƙurar ƙasa, za ka kuma bazu zuwa yamma da kuma gabas, zuwa arewa da kuma kudu. Dukan mutanen duniya za su sami albarka ta wurinka da kuma ta wurin ’ya’yanka.

  8. Ina tare da kai, zan lura da kai duk inda ka tafi, zan kuma dawo da kai zuwa wannan ƙasa. Ba zan rabu da kai ba sai na cika abin da na yi maka alkawari.”

  9. Bayan Yaƙub ya komo daga Faddan Aram, sai Allah ya bayyana gare shi, ya kuma albarkace shi.

  10. Allah ya ce masa, “Sunanka Yaƙub ne, amma ba za a ƙara kira ka Yaƙub ba; sunanka zai zama Isra’ila.” Saboda haka ya ba shi suna Isra’ila.

  11. Sai Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka yi ta haihuwa, ka kuma riɓaɓɓanya. Al’umma da tarin al’ummai za su fito daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga jikinka.

  12. Ƙasar da na ba wa Ibrahim da Ishaku, zan kuma ba ka, zan kuma ba da wannan ƙasa ga zuriyarka a bayanka.”

  13. Sa’an nan Allah ya tashi sama daga gare shi a wurin da ya yi magana da shi.

  14. Ya tabbatar da shi ga Yaƙub a matsayin ƙa’ida, Isra’ila a matsayin madawwamin alkawari,

  15. “Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana a matsayin rabo za ka yi gādo.”