Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jacob

285 ayoyi · 49 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai Liyatu ta ce, “Allah ya sāka mini saboda na ba da mai hidimata ga mijina.” Saboda haka ta ba shi suna Issakar.

  2. Liyatu ta sāke yin ciki ta kuma haifa wa Yaƙub ɗa na shida.

  3. Sai Liyatu ta ce, “Allah ya ba ni kyauta mai daraja. A wannan lokaci mijina zai darajarta ni, domin na haifa masa ’ya’ya maza shida.” Saboda haka ta ba shi suna Zebulun.

  4. Daga baya ta haifi ’ya ta kuwa ba ta suna Dina.

  5. Sai Allah ya tuna da Rahila; ya saurare ta ya kuma buɗe mahaifarta.

  6. Sai ta yi ciki ta kuma haifi ɗa ta ce, “Allah ya ɗauke mini kunyata.”

  7. Ta ba shi suna Yusuf, ta kuma ce, “Bari Ubangiji yă ƙara mini wani ɗa.”

  8. Bari in ratsa cikin dukan garkunanka yau in fid da masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki daga ciki, waɗannan ne za su zama ladana.

  9. Gaskiyata kuwa za tă zama mini shaida nan gaba, duk sa’ad da ka bincika a kan albashin da ka biya ni. Duk akuyar da take tawa da ba dabbare-dabbare ko babare-babare, ko ɗan ragon da ba baƙi ba, zai kasance sata na yi.”

  10. Sai Laban ya ce, “Na yarda. Bari yă zama yadda ka faɗa.”

  11. A wannan rana ya ware dukan bunsurai da suke dabbare-dabbare da masu zāne-zāne, da dukan awakin da suke dabbare-dabbare (duka da suke da fari-fari a jikinsu), da dukan baƙaƙen tumaki, ya sa su a hannun ’ya’yansa maza.

  12. Sa’an nan ya sa nisan tafiya kwana uku tsakaninsa da Yaƙub, yayinda Yaƙub ya ci gaba da lura da sauran garkunan Laban Yaƙub.

  13. Yaƙub ya samo ɗanyen reshen itatuwan aduruku, da na katambiri, da na durumi, ya ɓare ya bar fararen cikin katakon rassan.

  14. Sa’an nan ya zuba ɓararre rassan cikin dukan kwamame na banruwa saboda su kasance a gaban garkunan sa’ad da suka zo shan ruwa. A sa’ad da garkunan suke barbara suka kuma zo shan ruwa,

  15. sai su yi barbara a gaban rassan. Sai kuwa su haifi ƙanana masu zāne dabbare-dabbare, ko babare-babare ko masu zāne-zāne.

  16. Sai Yaƙub yă ware ƙananan garken dabam, amma sai yă sa sauran su fuskanci dabbobin da suke dabbare-dabbare da kuma baƙaƙe da suke na Laban. Ta haka ya ware garkuna dabam domin kansa bai kuwa haɗa su da dabbobin Laban ba.

  17. A duk sa’ad da ƙarfafa dabbobi mata suke barbara, Yaƙub yakan zuba rassan a kwamame a gaban dabbobin saboda su yi barbara kusa da rassan,

  18. amma in dabbobin raunana ne, ba ya sa su a can. Saboda haka raunanan dabbobi suka zama na Laban, ƙarfafan kuma suka zama na Yaƙub.

  19. Ta haka mutumin ya zama riƙaƙƙe mai arziki, ya kasance mai manya-manyan garkuna, da bayi mata da maza, da raƙuma da kuma jakuna.

  20. Yaƙub shi ma ya kama hanyarsa, sai mala’ikun Allah suka sadu da shi.

  21. Sa’ad da Yaƙub ya gan su sai ya ce, “Wannan sansanin Allah ne!” Saboda haka ya kira wannan wuri Mahanayim.

  22. Bayan Yaƙub ya zo daga Faddan Aram, ya iso lafiya a birnin Shekem a Kan’ana, ya kuma kafa sansani a ƙofar birni.

  23. Ya sayi fili daga ’ya’yan Hamor maza, mahaifin Shekem inda ya kafa tentinsa, a bakin azurfa ɗari.

  24. A can ya kafa bagade ya kuma kira shi El Elohe Isra’ila.

  25. Sa’an nan Allah ya ce wa Yaƙub, “Haura zuwa Betel ka yi zama a can, ka kuma gina bagade a can wa Allah wanda ya bayyana gare ka sa’ad da kake gudu daga ɗan’uwanka Isuwa.”