Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Afflictions

106 ayoyi · 21 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Mutane suka buɗe baki suka yi mini riyar reni; suka yi mini ba’a suka haɗu suka tayar mini.

  2. Allah ya bashe ni ga mugayen mutane, ya jefa ni hannun mugaye.

  3. Dā ina zamana lafiya kome yana tafiya daidai; amma ya ragargaza ni; ya shaƙe ni a wuya; ya murƙushe ni na zama abin barata gare shi;

  4. maharbansa sun kewaye ni. Ba tausayi, ya soke ni a ƙodata har jini ya zuba a ƙasa.

  5. Ya ji mini rauni a kai a kai ya auko mini kamar mai yaƙi.

  6. “Ina makoki saye da tsummoki na ɓoye fuskata a cikin ƙura.

  7. Fuskata ta yi ja don kuka idanuna sun kukumbura;

  8. Jin ƙarfi da ya cika ƙasusuwansa zai kwantar da shi a cikin ƙura.

  9. Gama fushinsa na ɗan lokaci ne amma alherinsa har matuƙa ne; mai yiwuwa a yi kuka da dare amma farin ciki kan zo da safe.

  10. Zurfi kan kira zurfi cikin rurin matsirgar ruwanka; dukan raƙuma da igiyoyi sun sha kaina.

  11. Ka kawo mu cikin kurkuku ka kuma jibga kaya masu nauyi a bayanmu.

  12. Ka bar mutane suka hau a kawunanmu; mun bi ta wuta da ruwa, amma ka kawo mu zuwa wurin yalwa.

  13. Duk da haka ya kasance mai jinƙai; ya gafarta laifofinsu bai kuwa hallaka su ba. Sau da sau ya janye fushinsa bai kuwa sa fushinsa yă ƙuna ba.

  14. Ya tuna cewa su naman jiki ne kawai, iska mai wucewa da ba ta dawowa.

  15. Ka ciyar da su da burodin hawaye; ka sa suka sha hawaye ta cikakken kwaf.

  16. “In ’ya’yansa maza suka yashe dokata ba su kuwa bi ƙa’idodina ba,

  17. in suka take ƙa’idodina suka kuma kāsa kiyaye umarnaina,

  18. zan hukunta zunubinsu da sanda, laifinsu da bulala;

  19. Ba zai yi ta zargi ba ba kuwa zai yi ta jin fushi har abada ba;

  20. ba ya yin da mu gwargwadon zunubanmu ko yă sāka mana bisa ga laifofinmu.

  21. Sau da yawa ya cece su, amma sun nace su yi tawaye suka kuma lalace cikin zunubinsu.

  22. Amma ya lura da wahalarsu sa’ad da ya ji kukansu;

  23. saboda su ya tuna da alkawarinsa kuma daga yawan ƙaunarsa ya ji tausayi.

  24. Ya sa aka ji tausayinsu a wurin dukan waɗanda suka kame su.

  25. Ya Ubangiji na sani, cewa dokokinka masu adalci ne, kuma cikin aminci ka hore ni.