Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Afflictions: Of saints, end in joy and blessedness

7 ayoyi · 21 fannoni

Ayoyi game da Of saints, end in joy and blessedness

  1. Waɗanda suka yi shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.

  2. Shi da ya fita yana kuka, riƙe da iri don shuki, zai dawo da waƙoƙin farin ciki, ɗauke da dammuna.

  3. don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu, don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki,

  4. in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona, in maido musu rawani mai kyau a maimako na toka, man murna a maimako na makoki, da kuma rigar yabo a maimako na ruhun fid da zuciya. Za a ce da su itatuwan oak na adalci, shukin Ubangiji don bayyana darajarsa.

  5. Masu albarka ne waɗanda suke makoki, gama za a yi musu ta’aziyya.

  6. Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa.

  7. In an zage ku saboda sunan Kiristi, ku masu albarka ne, gama Ruhun ɗaukaka da kuma na Allah yana bisanku.