Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Afflictions: Often severe

14 ayoyi · 21 fannoni

Ayoyi game da Often severe

  1. Ba shakka ya Allah ka gajiyar da ni; ka ɓata gidana gaba ɗaya.

  2. Ka daure ni, ya kuma zama shaida; yadda na rame sai ƙasusuwa, wannan ya sa ake gani kamar don ni mai zunubi ne shi ya sa.

  3. Allah ya kai mini hari ya yi kaca-kaca da ni cikin fushinsa yana cizon haƙoransa don fushin da yake yi da ni; ya zura mini ido.

  4. Mutane suka buɗe baki suka yi mini riyar reni; suka yi mini ba’a suka haɗu suka tayar mini.

  5. Allah ya bashe ni ga mugayen mutane, ya jefa ni hannun mugaye.

  6. Dā ina zamana lafiya kome yana tafiya daidai; amma ya ragargaza ni; ya shaƙe ni a wuya; ya murƙushe ni na zama abin barata gare shi;

  7. maharbansa sun kewaye ni. Ba tausayi, ya soke ni a ƙodata har jini ya zuba a ƙasa.

  8. Ya ji mini rauni a kai a kai ya auko mini kamar mai yaƙi.

  9. “Ina makoki saye da tsummoki na ɓoye fuskata a cikin ƙura.

  10. Fuskata ta yi ja don kuka idanuna sun kukumbura;

  11. Zurfi kan kira zurfi cikin rurin matsirgar ruwanka; dukan raƙuma da igiyoyi sun sha kaina.

  12. Ka bar mutane suka hau a kawunanmu; mun bi ta wuta da ruwa, amma ka kawo mu zuwa wurin yalwa.

  13. Cikin tashin hankali, ka jefa ni cikin zurfafa, a tsakiyar teku, ka kuma jujjuya ni a cikin ruwa; dukan raƙuman ruwanka da ambaliyarka sun bi ta kaina.

  14. Na amsa na ce, “Ranka yă daɗe, kai ka sani.” Sai ya ce, “Waɗannan su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala; sun wanke tufafinsu suka kuma mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan.