Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Afflictions

106 ayoyi · 21 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Waɗanda suka yi shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.

  2. Shi da ya fita yana kuka, riƙe da iri don shuki, zai dawo da waƙoƙin farin ciki, ɗauke da dammuna.

  3. za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.

  4. domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi.

  5. Duk da haka, babu sauran baƙin ciki ga waɗanda suke shan azaba. Dā ya ƙasƙantar da ƙasar kabilan Zebulun da ƙasar Naftali, amma nan gaba zai girmama Galili na Al’ummai, ta hanyar teku wadda take ta Urdun.

  6. Gatari ya taɓa fin wanda yake amfani da shi girma, ko zarto yă yi wa wanda yake amfani da shi taƙama? Sanda za tă girgiza mutumin da yake riƙe da ita, ko kuwa kulki yă jijjiga mutumin da yake riƙe da katako!

  7. Ba da daɗewa ba fushina a kanku zai zo ga ƙarshe hasalata kuma za tă koma ga hallakarsu.”

  8. Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri; ya tashi don yă nuna muku jinƙai. Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya. Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!

  9. Ya mutanen Sihiyona, waɗanda suke zama a Urushalima, ba za ku ƙara kuka ba. Zai zama mai alheri sa’ad da kuka yi kukan neman taimako! Da zarar ya ji, zai amsa muku.

  10. Ko da yake Ubangiji yakan ba da abincin azaba da ruwan wahala, ba za a ƙara ɓoye malamanku ba; da idanunku za ku gan su.

  11. Ko kun juye dama ko hagu, kunnuwanku za su ji murya a bayanku tana cewa, “Ga hanya; ku yi tafiya a kai.”

  12. Ni ne na siffanta haske na kuma halicci duhu, ni ne nake ba da nasara in kuma jawo bala’i; ni, Ubangiji ne ke aikata dukan waɗannan abubuwa.

  13. “Gama a ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke, amma da ƙauna mai zurfi zan sāke dawo da ke.

  14. Cikin fushi mai zafi na ɓoye fuskata daga gare ki na ɗan lokaci, amma da madawwamin alheri zan ji tausayinki,” in ji Ubangiji Mai Fansarki.

  15. Na yi fushi saboda kwaɗayin zunubinsa; na yi masa horo, na kuma ɓoye fuskata saboda fushi, duk da haka ya ci gaba da ayyukan zunubinsa.

  16. don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu, don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki,

  17. in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona, in maido musu rawani mai kyau a maimako na toka, man murna a maimako na makoki, da kuma rigar yabo a maimako na ruhun fid da zuciya. Za a ce da su itatuwan oak na adalci, shukin Ubangiji don bayyana darajarsa.

  18. “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kamar ’ya’yan ɓauren nan masu kyau, haka zan kula da mutanen Yahuda waɗanda aka kwaso waɗanda na fisshe su daga wannan wuri zuwa ƙasar Babiloniyawa

  19. Idanuna za su kula da su don kyautatawarsu, zan kuma komo da su wannan ƙasa. Zan gina su ba zan rushe su ba; zan dasa su ba kuwa zan tumɓuke su ba.

  20. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sa’ad da shekaru saba’in suka cika a Babilon, zan zo muku in cika alkawarin alherina don in komo da ku zuwa wannan wuri.

  21. Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana, gama ina tare da kai,” in ji Ubangiji. “Ko da na hallaka dukan al’ummai sarai inda na kora ka, ba zan hallaka ka sarai ba. Zan hore ka amma da adalci kaɗai; ba zan bar ka ba hukunci ba.”

  22. Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai, ƙaunarsa tana da yawa.

  23. Gama ba haka kawai yake kawo wahala ko ɓacin rai ga ’yan adam ba.

  24. Zan lura da ku yayinda kuke wucewa ƙarƙashin sanda, zan kuma kawo ku cikin daurin alkawari.

  25. Idan aka busa ƙaho a ciki birni mutane ba sa yin rawar jiki? Sa’ad da bala’i ya auko wa birni, ba Ubangiji ne ya sa a kawo shi ba?