- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 930–586 BC
The Divided Kingdom
The kingdom splits into Israel and Judah; prophets warn of judgment as both nations slowly drift into idolatry and exile.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Sarakuna 15:28kusan 954 K.H.
Ba’asha ya kashe Nadab a shekara ta uku ta Asa sarkin Yahuda, ya kuma gāje shi a matsayin sarki.
- 1 Sarakuna 15:29kusan 954 K.H.
Nan da nan da ya fara mulki, sai ya kashe dukan iyalin Yerobowam. Bai bar wa Yerobowam wani da rai ba, amma ya hallaka su duka, bisa ga maganar Ubangiji da ya ba wa bawansa Ahiya, mutumin Shilo.
- 1 Sarakuna 15:30kusan 954 K.H.
Wannan abu ya faru saboda zunuban da Yerobowam ya yi, ya kuma sa Isra’ila ya yi, kuma saboda ya tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya yi fushi.
- 1 Sarakuna 15:31kusan 954 K.H.
Game da sauran ayyukan mulkin Nadab da kuma dukan abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
- 1 Sarakuna 15:32kusan 953 K.H.
Aka yi yaƙi tsakanin Asa da Ba’asha sarkin Isra’ila dukan kwanakin mulkinsu.
- 1 Sarakuna 15:33kusan 953 K.H.
A shekara ta uku ta Asa sarkin Yahuda, Ba’asha ɗan Ahiya ya zama sarkin dukan Isra’ila a Tirza, ya kuma yi sarauta shekara ashirin da huɗu.
- 1 Sarakuna 15:34kusan 953 K.H.
Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yana tafiya a hanyoyin Yerobowam da kuma cikin zunubinsa, wanda ya sa Isra’ila suka yi.
- 1 Sarakuna 16:1kusan 931 K.H.
Sai maganar Ubangiji ta zo wa Yehu ɗan Hanani game da Ba’asha,
- 1 Sarakuna 16:2kusan 931 K.H.
“Na ɗaga ka daga ƙura na mai da kai shugaban mutanena Isra’ila, amma ka yi tafiya a hanyoyin Yerobowam, ka kuma sa mutanena Isra’ila suka yi zunubi, ka tsokane ni na yi fushi ta wurin zunubansu.
- 1 Sarakuna 16:3kusan 931 K.H.
Saboda haka ina gab da cinye Ba’asha da gidansa, zan kuma mai da gidanka kamar na Yerobowam ɗan Nebat.
- 1 Sarakuna 16:4kusan 931 K.H.
Karnuka za su cinye waɗanda suke na Ba’asha da suka mutu a birni, tsuntsaye kuma za su cinye waɗanda suka mutu a jeji.”
- 1 Sarakuna 16:5kusan 953 K.H.
Game da sauran ayyukan mulkin Ba’asha, abin da ya yi, da kuma nasarorinsa, an rubuta su cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
- 1 Sarakuna 16:6kusan 930 K.H.
Ba’asha ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Tirza. Sai Ela ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
- 1 Sarakuna 16:7kusan 930 K.H.
Ban da haka, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Yehu ɗan Hanani wa Ba’asha da gidansa, saboda dukan muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, ya tsokane shi yă yi fushi ta wurin abubuwan da ya yi, da kuma zama kamar gidan Yerobowam, da kuma domin ya hallaka gidan Yerobowam.
- 1 Sarakuna 16:8kusan 929 K.H.
A shekara ta ashirin da shida ta Asa sarkin Yahuda, Ela ɗan Ba’asha ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki a Tirza shekaru biyu.
- 1 Sarakuna 16:9kusan 929 K.H.
Zimri, ɗaya daga cikin shugabanni, wanda ya shugabanci rabin kekunan yaƙin Ela, ya yi maƙarƙashiya a kansa. Ela yana a Tirza a lokacin, ya bugu a gidan Arza, sarkin fada a Tirza.
- 1 Sarakuna 16:10kusan 929 K.H.
Zimri ya shiga, ya buge shi ya kashe a shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda. Sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki.
- 1 Sarakuna 16:11kusan 929 K.H.
Nan da nan sai ya fara mulki ya kuwa zauna a kujerar sarauta, ya kashe dukan iyalin Ba’asha. Bai bar namiji guda ɗaya ba, ko dangi, ko aboki.
- 1 Sarakuna 16:12kusan 929 K.H.
Ta haka Zimri ya hallaka dukan iyalin Ba’asha, bisa ga maganar da Ubangiji ya yi game da Ba’asha ta wurin annabi Yehu.
- 1 Sarakuna 16:13kusan 929 K.H.
Wannan ya faru saboda dukan zunuban Ba’asha da waɗanda ɗansa Ela ya yi, da ya sa Isra’ila suka yi, har suka tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila, yă yi fushi ta wurin gumakansu marasa amfani.
- 1 Sarakuna 16:14kusan 929 K.H.
Game da sauran ayyukan mulkin Ela, da dukan abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
- 1 Sarakuna 16:15kusan 929 K.H.
A shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda, Zimri ya yi mulki a Tirza kwana bakwai. Mayaƙa suka yi sansani kusa da Gibbeton, wani garin Filistiyawa.
- 1 Sarakuna 16:16kusan 929 K.H.
Sa’ad da Isra’ilawa a cikin sansani suka ji cewa Zimri ya yi maƙarƙashiya a kan sarki, ya kuma kashe shi, sai suka yi shela, suka naɗa Omri, shugaban mayaƙa ya zama sarki a bisa Isra’ila, a wannan rana a cikin sansani.
- 1 Sarakuna 16:17kusan 929 K.H.
Sai Omri da dukan Isra’ilawa suka janye daga Gibbeton, suka yi wa Tirza kwanto.
- 1 Sarakuna 16:18kusan 929 K.H.
Da Zimri ya ga cewa an kame birnin, sai ya je ya shiga hasumiya fadan sarki ya sa wa fadan wuta wutar kuwa ta ƙone shi ya mutu.