Tsallake zuwa abun ciki

circa 930–586 BC

The Divided Kingdom

The kingdom splits into Israel and Judah; prophets warn of judgment as both nations slowly drift into idolatry and exile.

1,722 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 1 Sarakuna 16:19kusan 929 K.H.

    Wannan ya faru saboda zunuban da ya yi, ya yi mugunta a gaban Ubangiji ya kuma yi tafiya a hanyoyin Yerobowam da kuma cikin zunubin da Yerobowam ya yi da ya sa Isra’ila suka yi.

  2. 1 Sarakuna 16:20kusan 929 K.H.

    Game da sauran ayyukan mulkin Zimri, da tawayen da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

  3. 1 Sarakuna 16:21kusan 929 K.H.

    Sai mutanen Isra’ila suka rabu kashi biyu; rabi guda sun goyi bayan Tibni ɗan Ginat yă zama sarki, ɗayan rabin kuma sun goyi bayan Omri.

  4. 1 Sarakuna 16:22kusan 929 K.H.

    Amma mabiyan Omri suka nuna sun fi na Tibni ɗan Ginat ƙarfi. Sai Tibni ya mutu, Omri kuwa ya zama sarki.

  5. 1 Sarakuna 16:23kusan 925 K.H.

    A shekara ta talatin da ɗaya na Asa sarkin Yahuda, Omri ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki shekara goma sha biyu, shekaru shida a Tirza.

  6. 1 Sarakuna 16:24kusan 925 K.H.

    Ya saya tudun Samariya daga Shemer, a bakin talentin biyu na azurfa, ya kuma gina birni a kan tudun, ya kira shi Samariya, bayan Shemer, sunan mai tudun a dā.

  7. 1 Sarakuna 16:25kusan 925 K.H.

    Amma Omri ya yi mugunta a gaban Ubangiji, ya kuma yi zunubi fiye da dukan waɗanda suka kasance kafin shi.

  8. 1 Sarakuna 16:26kusan 925 K.H.

    Ya yi tafiya a dukan hanyoyin Yerobowam ɗan Nebat da kuma cikin zunubinsa wanda ya sa Isra’ila suka yi, har suka tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila yă yi fushi ta wurin gumakansu marasa amfani.

  9. 1 Sarakuna 16:27kusan 925 K.H.

    Game da sauran ayyukan mulkin Omri, abin da ya yi, da kuma abubuwan da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

  10. 1 Sarakuna 16:28kusan 925 K.H.

    Omri ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Samariya. Sai Ahab ya gāje shi a matsayin sarki.

  11. 1 Sarakuna 16:29kusan 918 K.H.

    A shekara ta talatin da takwas ta Asa sarkin Yahuda, Ahab ɗan Omri ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki a Samariya a kan Isra’ila, shekara ashirin da biyu.

  12. 1 Sarakuna 16:30kusan 918 K.H.

    Ahab ɗan Omri ya yi mugunta sosai a gaban Ubangiji fiye da wani daga cikin waɗanda suka riga shi.

  13. 1 Sarakuna 16:31kusan 918 K.H.

    Bai zama masa wani abu mai wuya ba, yă yi zunuban Yerobowam ɗan Nebat, har ma ya auri Yezebel ’yar Etba’al sarkin Sidoniyawa, ya kuma fara bauta wa Ba’al, ya yi masa sujada.

  14. 1 Sarakuna 16:32kusan 918 K.H.

    Ya kafa bagade domin Ba’al a haikalin Ba’al da ya gina a Samariya.

  15. 1 Sarakuna 16:33kusan 918 K.H.

    Ahab ya gina ginshiƙin Ashera, ya kuma aikata abubuwa masu yawa don yă tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila yă yi fushi fiye da dukan sarakunan Isra’ila da suka riga shi.

  16. 1 Sarakuna 16:34kusan 918 K.H.

    A lokaci Ahab ne, Hiyel mutumin Betel ya sāke gina Yeriko. Ya kafa tushensa a bakin ran ɗan farinsa Abiram, ya kuma kafa ƙofofinsa a bakin ran autansa Segub, bisa ga maganar Ubangiji da ya yi ta wurin Yoshuwa ɗan Nun.

  17. 1 Sarakuna 17:1kusan 910 K.H.

    To, Iliya mutumin Tishbe, daga Tishbe a Gileyad, ya ce wa Ahab, “Muddin Ubangiji, Allah na Isra’ila wanda nake bauta wa yana a raye, ba za a yi raɓa ko ruwan sama a ’yan shekaru masu zuwa ba, sai ko na faɗa haka.”

  18. 1 Sarakuna 17:2kusan 910 K.H.

    Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya, ta ce,

  19. 1 Sarakuna 17:3kusan 910 K.H.

    “Ka bar nan, ka nufi wajajen gabas, ka ɓuya a Rafin Kerit, gabas da Urdun.

  20. 1 Sarakuna 17:4kusan 910 K.H.

    Za ka sha daga rafin, zan kuma umarci hankaki su ciyar da kai a can.”

  21. 1 Sarakuna 17:5kusan 910 K.H.

    Saboda haka sai Iliya ya yi abin da Ubangiji ya faɗa masa. Ya tafi Rafin Kerit, gabas da Urdun, ya zauna a can.

  22. 1 Sarakuna 17:6kusan 910 K.H.

    Hankaki suka riƙa kawo masa abinci da nama, safe da yamma, ya kuma sha daga rafin.

  23. 1 Sarakuna 17:7kusan 909 K.H.

    Ana nan sai rafin ya bushe saboda ba a yi ruwan sama a ƙasar ba.

  24. 1 Sarakuna 17:8kusan 909 K.H.

    Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya cewa,

  25. 1 Sarakuna 17:9kusan 909 K.H.

    “Je ka, nan take, zuwa Zarefat na Sidon, ka zauna a can. Na umarci wata gwauruwa a can tă ciyar da kai.”