- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 930–586 BC
The Divided Kingdom
The kingdom splits into Israel and Judah; prophets warn of judgment as both nations slowly drift into idolatry and exile.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Sarakuna 18:11kusan 906 K.H.
Amma yanzu kana faɗa mini in tafi wurin mai girma in ce, ‘Iliya yana a nan.’
- 1 Sarakuna 18:12kusan 906 K.H.
Ban san inda Ruhun Ubangiji zai kai ka sa’ad da na bar ka ba. In na tafi na faɗa wa Ahab bai kuma same ka a nan ba, zai sa a kashe ni. Tuna fa, ni bawanka, na yi wa Ubangiji sujada tun ina saurayi.
- 1 Sarakuna 18:13kusan 906 K.H.
Ranka yă daɗe, ashe, ba a faɗa maka abin da na yi lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Ubangiji ba? Yadda na ɓoye annabawa ɗari, na sa su hamsin-hamsin a kogwanni biyu, na yi ta ba su abinci da ruwa.
- 1 Sarakuna 18:14kusan 906 K.H.
Yanzu fa, kana ce in tafi wurin mai girma sarki, in ce, ‘Iliya yana a nan.’ Ai, zai kashe ni!”
- 1 Sarakuna 18:15kusan 906 K.H.
Iliya ya ce, “Na rantse da Ubangiji Maɗaukaki, wanda nake bauta wa, tabbatacce zan gabatar da kaina ga Ahab a yau.”
- 1 Sarakuna 18:16kusan 906 K.H.
Saboda haka sai Obadiya ya tafi wurin Ahab ya faɗa masa, Ahab kuwa ya tafi wurin Iliya.
- 1 Sarakuna 18:17kusan 906 K.H.
Sa’ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Kai ne wannan, kai mai tā-da-na-zaune-tsaye a Isra’ila?”
- 1 Sarakuna 18:18kusan 906 K.H.
Iliya ya amsa, ya ce, “Ban tā-da-na-zaune-tsaye a Isra’ila ba. Amma kai da iyalin mahaifinka, ku kuka tā-da-na-zaune-tsaye. Ka ƙyale umarnai Ubangiji, ka bi Ba’al.
- 1 Sarakuna 18:19kusan 906 K.H.
Yanzu ka tara mutane daga dukan Isra’ila su sadu da ni a kan Dutsen Karmel. Ka kuma kawo annabawa ɗari huɗu da hamsin na Ba’al, da kuma annabawa ɗari huɗu na Ashera, waɗanda suke ci a teburin Yezebel.”
- 1 Sarakuna 18:20kusan 906 K.H.
Sai Ahab ya aika a duk fāɗin Isra’ila, ya kuma tattara annabawan a kan Dutsen Karmel.
- 1 Sarakuna 18:21kusan 906 K.H.
Iliya ya je gaban mutane ya ce, “Har yaushe za ku yi ta yawo tsakanin ra’ayoyi biyu? In Ubangiji ne Allah, ku bi shi; amma in Ba’al Allah ne, ku bi shi.” Mutane dai ba su ce uffam ba.
- 1 Sarakuna 18:22kusan 906 K.H.
Sai Iliya ya ce musu, “Ni ne kaɗai annabin Ubangiji da ya rage, amma Ba’al yana da annabawa ɗari huɗu da hamsin.
- 1 Sarakuna 18:23kusan 906 K.H.
Ku samo mana bijimai biyu. Bari su zaɓa ɗaya wa kansu, bari kuma su yanka shi kucu-kucu su sa a itace, sai dai, kada su sa wuta a kansa. Ni kuwa zan shirya ɗaya bijimin in sa a kan itace, ni ma, ba zan sa wuta a kansa ba.
- 1 Sarakuna 18:24kusan 906 K.H.
Sa’an nan ku kira bisa sunan allahnku, ni kuwa zan kira bisa sunan Ubangiji. Duk allahn da ya amsa ta wurin wuta, shi ne Allah.” Sai dukan jama’a suka ce, “Abin nan da faɗa yana da kyau.”
- 1 Sarakuna 18:25kusan 906 K.H.
Iliya ya ce wa annabawan Ba’al, “Ku ku fara zaɓi bijimi ɗaya, ku shirya, da yake kuna da yawa. Ku kira a bisa sunan allahnku, amma kada ku ƙuna wuta.”
- 1 Sarakuna 18:26kusan 906 K.H.
Sai suka ɗauki bijimin da aka ba su suka shirya shi. Sa’an nan suka kira bisa sunan Ba’al daga safe har tsakar rana. Suna ihu, “Ya Ba’al, ka amsa mana!” Amma babu wata amsa, babu wani da ya amsa. Suka yi ta rawa kewaye da bagaden da suka yi.
- 1 Sarakuna 18:27kusan 906 K.H.
Da tsakar rana, Iliya ya fara yin musu ba’a. Ya ce, “Ku yi ihu da ƙarfi, tabbatacce shi allah ne! Mai yiwuwa yana cikin zurfin tunani, ko dai aiki ya yi masa yawa, ko ya yi tafiya. Mai yiwuwa yana barci ne, dole a tashe shi.”
- 1 Sarakuna 18:28kusan 906 K.H.
Sai suka yi ta ihu da ƙarfi suna tsattsaga kansu da takuba da māsu, yadda al’adarsu take, sai da jininsu ya yi ta zuba.
- 1 Sarakuna 18:29kusan 906 K.H.
Tsakar rana ta wuce, suka ci gaba da ƙoƙari, suna annabci har lokacin miƙa hadayar yamma ya yi. Amma babu wani da ya tanƙa, babu wani da ya amsa, babu wanda ya kula.
- 1 Sarakuna 18:30kusan 906 K.H.
Sa’an nan Iliya ya ce wa dukan mutane, “Ku zo nan wurina.” Suka zo wurinsa, ya kuma shirya bagaden Ubangiji, da ya riga ya zama kufai.
- 1 Sarakuna 18:31kusan 906 K.H.
Iliya ya ɗauki duwatsu goma sha biyu, ɗaya don kowace kabila zuriyar Yaƙub, wanda maganar Ubangiji ta zo masa, cewa, “Sunanka zai zama Isra’ila.”
- 1 Sarakuna 18:32kusan 906 K.H.
Da waɗannan duwatsun ya gina bagade cikin sunan Ubangiji, ya kuma haƙa wuriya kewaye da shi, isashe da zai ci garwa biyu na irin ƙwayar gyada.
- 1 Sarakuna 18:33kusan 906 K.H.
Ya shirya itace, ya yayyanka bijimin kucu-kucu, ya shimfiɗa shi a itacen. Sa’an nan ya ce musu, “Ku cika manyan tuluna da ruwa, ku zuba a kan hadayar da kuma a kan itacen.” Suka zuba.
- 1 Sarakuna 18:34kusan 906 K.H.
Ya ce, “Ku sāke yin haka,” sai suka sāke yin haka. Ya umarta, “Ku yi haka sau na uku,” suka kuma yi haka sau na uku.
- 1 Sarakuna 18:35kusan 906 K.H.
Ruwan ya gangara kewaye da bagaden har ma ya cika wuriyar.