Tsallake zuwa abun ciki

circa 930–586 BC

The Divided Kingdom

The kingdom splits into Israel and Judah; prophets warn of judgment as both nations slowly drift into idolatry and exile.

1,722 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 1 Sarakuna 19:15kusan 906 K.H.

    Sai Ubangiji ya ce masa, “Ka koma ta hanyar da ka zo, ka tafi Hamadan Damaskus. Sa’ad da ka kai can, ka shafe Hazayel yă zama sarki bisa Aram.

  2. 1 Sarakuna 19:16kusan 906 K.H.

    Ka kuma shafe Yehu ɗan Nimshi yă zama sarkin Isra’ila, ka shafe Elisha ɗan Shafat daga Abel-Mehola yă gāje ka a matsayin annabi.

  3. 1 Sarakuna 19:17kusan 906 K.H.

    Yehu zai kashe duk wani wanda ya tsere wa takobin Hazayel, Elisha kuwa zai kashe duk wani wanda ya tsere wa takobin Yehu.

  4. 1 Sarakuna 19:18kusan 906 K.H.

    Duk da haka zan bar mutane dubu bakwai na Isra’ila waɗanda ba su rusuna da gwiwansu wa Ba’al ba, ba su kuma sumbace shi da bakinsu ba.”

  5. 1 Sarakuna 19:19kusan 906 K.H.

    Sai Iliya ya tafi daga can ya sami Elisha ɗan Shafat, yana noma da shanu goma sha biyu masu garman noma, shi kansa yana jan na goma sha biyun. Iliya ya tafi wurinsa ya jefa mayafinsa a kan Elisha.

  6. 1 Sarakuna 19:20kusan 906 K.H.

    Sai Elisha ya bar shanun, ya ruga ya bi Iliya. Ya ce, “Bari in sumbace mahaifina da mahaifiyata, in yi musu bankwana, sa’an nan in zo in bi ka.” Iliya ya ce, “Koma! Me na yi maka?”

  7. 1 Sarakuna 19:21kusan 906 K.H.

    Sai Elisha ya bar shi, ya koma, ya ɗauki shanunsa ya yayyanka. Ya ƙone kayan garman noman don yă dafa naman, ya kuma ba wa mutane naman, suka kuwa ci. Sa’an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya kuma zama mai hidimarsa.

  8. 1 Sarakuna 20:1kusan 901 K.H.

    Ben-Hadad sarkin Aram kuwa ya tattara mayaƙansa gaba ɗaya. Sarakuna talatin da biyu suka tafi tare da shi haɗe da dawakansu da kekunan yaƙinsu. Ya haura ya yi wa Samariya kwanto, ya kuma yaƙe ta.

  9. 1 Sarakuna 20:2kusan 901 K.H.

    Ya aika da ’yan aika zuwa cikin birnin wurin Ahab sarkin Isra’ila yana cewa, “Ga abin da Ben-Hadad ya ce,

  10. 1 Sarakuna 20:3kusan 901 K.H.

    ‘Azurfarka da zinariyarka nawa ne. Mafi kyau cikin matanka da ’ya’yanka nawa ne.’ ”

  11. 1 Sarakuna 20:4kusan 901 K.H.

    Sarkin Isra’ila ya amsa, ya ce, “Kamar dai yadda ka faɗa, ranka yă daɗe, sarki. Ni da dukan abin da nake da shi, naka ne.”

  12. 1 Sarakuna 20:5kusan 901 K.H.

    Sai ’yan aikan suka sāke dawo suka ce, “Ga abin da Ben-Hadad ya ce, ‘Na aika ka ba da azurfarka da zinariyarka, matanka da kuma ’ya’yanka.

  13. 1 Sarakuna 20:6kusan 901 K.H.

    Amma war haka gobe zan aika shugabannina su bincika fadanka da kuma gidajen shugabanninka. Za su kwashe dukan abubuwan da kake ganin darajarsu su tafi.’ ”

  14. 1 Sarakuna 20:7kusan 901 K.H.

    Sarkin Isra’ila ya tattara dukan dattawan ƙasar, ya ce musu, “Ku duba fa, wannan mutum yana neman tsokana! Sa’ad da ya aika in ba shi matana da ’ya’yana, azurfana da zinariyana, ban hana masa ba.”

  15. 1 Sarakuna 20:8kusan 901 K.H.

    Dattawa da dukan mutane suka amsa, suka ce, “Kada ka saurare shi ko ka yarda da abin da yake bukata.”

  16. 1 Sarakuna 20:9kusan 901 K.H.

    Saboda haka ya ba wa ’yan aikan Ben-Hadad amsa, ya ce, “Ku faɗa wa ranka yă daɗe, sarki, ‘Bawanka zai yi dukan abin da ka bukaci da farko, amma wannan na ƙarshe ba zan iya yin ba.’ ” Suka tafi suka kai amsar wa Ben-Hadad.

  17. 1 Sarakuna 20:10kusan 901 K.H.

    Sai Ben-Hadad ya aika da wani saƙo wa Ahab, ya ce, “Bari alloli su yi da ni yadda suke so, su kuma yi haka da tsanani, in isashen ƙura ta rage a Samariya da za a iya ba wa mutanena a tafin hannu.”

  18. 1 Sarakuna 20:11kusan 901 K.H.

    Sarki Isra’ila ya amsa, ya ce, “Ku faɗa masa, ‘Wanda ya sa kayan yaƙinsa bai kamata yă yi fariya ba sai ya tuɓe su.’ ”

  19. 1 Sarakuna 20:12kusan 901 K.H.

    Ben-Hadad ya ji wannan saƙo yayinda shi da sarakunan suke sha a cikin tentunansu, sai ya umarce mutanensa, ya ce, “Ku shirya don yaƙi.” Saboda haka suka shirya don su yaƙi birnin.

  20. 1 Sarakuna 20:13kusan 901 K.H.

    Ana cikin haka sai wani annabi ya zo wurin Ahab sarkin Isra’ila ya sanar masa cewa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka ga wannan ɗumbun mayaƙa? Zan ba da su cikin hannunka a yau, sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

  21. 1 Sarakuna 20:14kusan 901 K.H.

    Ahab ya ce, “Amma wa zai yi haka?” Annabin ya amsa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Sojoji matasa na shugabannin yankuna za su yi haka.’ ” Ya tambaya, “Wa kuma zai fara yaƙin?” Annabin ya amsa, “Kai za ka fara.”

  22. 1 Sarakuna 20:15kusan 901 K.H.

    Saboda haka Ahab ya kira sojoji matasa na shugabannin yankuna, mutum 232. Sa’an nan ya tattara sauran Isra’ilawa su 7,000 gaba ɗaya.

  23. 1 Sarakuna 20:16kusan 901 K.H.

    Suka fita da tsakar rana yayinda Ben-Hadad tare da sarakuna 32 masu goyon bayansa suke cikin tentunansu suna sha, suna buguwa.

  24. 1 Sarakuna 20:17kusan 901 K.H.

    Sojojin nan matasa na shugabannin yankuna suka fara fita. Ben-Hadad kuwa ya riga ya aiki ’yan leƙen asiri, waɗanda suka ce, “Mutane suna zuwa daga Samariya.”

  25. 1 Sarakuna 20:18kusan 901 K.H.

    Ya ce, “In sun fito don salama, ku kamo su da rai; in sun fito yaƙi ne, ku kamo su da rai.”