- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 930–586 BC
The Divided Kingdom
The kingdom splits into Israel and Judah; prophets warn of judgment as both nations slowly drift into idolatry and exile.
Ayoyi daga wannan lokacin
Shi ma ya aikata dukan irin zunubai da tsohonsa ya yi. Zuciyarsa ba tă bi Ubangiji Allahnsa, kamar yadda zuciyar Dawuda kakansa ta yi ba.
Duk da haka, saboda Dawuda Ubangiji Allahnsa ya ba shi fitila a Urushalima ta wurin ta da wani da ya gāje shi, ta wurinsa kuma Urushalima ta yi ƙarfi.
Gama Dawuda ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, bai kuma fasa kiyaye wani daga umarnan Ubangiji ba dukan kwanakinsa, sai dai a batun Uriya mutumin Hitti.
Aka yi yaƙi tsakanin Rehobowam da Yerobowam a duk kwanakin Abiya.
Game da sauran ayyukan mulkin Abiyam kuwa, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Aka yi yaƙi tsakanin Abiyam da Yerobowam.
- 1 Sarakuna 15:8kusan 955 K.H.
Sai Abiyam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Asa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.
- 1 Sarakuna 15:9kusan 955 K.H.
A shekara ta ashirin ta Yerobowam sarkin Isra’ila, Asa ya zama sarkin Yahuda,
- 1 Sarakuna 15:10kusan 955 K.H.
ya yi mulki a Urushalima shekara arba’in da ɗaya. Sunan mahaifiya mahaifiyarsa, Ma’aka ne ’yar Abisalom.
- 1 Sarakuna 15:11kusan 955 K.H.
Asa ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar yadda kakansa Dawuda ya yi.
- 1 Sarakuna 15:12kusan 955 K.H.
Ya kori dukan maza karuwai na masujadai daga ƙasar, ya kuma yi waje da dukan gumakan da mahaifinsa ya yi.
- 1 Sarakuna 15:13kusan 955 K.H.
Ya tuɓe mahaifiya mahaifiyarsa Ma’aka daga matsayinta na mahaifiyar sarauniya, gama ta gina ƙazantaccen ginshiƙin Ashera. Asa ya yanke ginshiƙin, ya kuma ƙone shi a Kwarin Kidron.
- 1 Sarakuna 15:14kusan 955 K.H.
Ko da yake bai cire masujadai da suke kan tuddai ba, zuciyar Asa ta kasance da aminci ɗungum ga Ubangiji dukan kwanakinsa.
- 1 Sarakuna 15:15kusan 955 K.H.
Ya kawo azurfa da zinariya da kayayyakin da shi da mahaifinsa suka keɓe a haikalin Ubangiji.
- 1 Sarakuna 15:16kusan 955 K.H.
Aka yi yaƙi tsakanin Asa da Ba’asha sarkin Isra’ila dukan kwanakin mulkinsu.
- 1 Sarakuna 15:17kusan 930 K.H.
Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura, ya yi yaƙi da Yahuda, ya kuma gina Rama don yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa, sarkin Yahuda.
- 1 Sarakuna 15:18kusan 930 K.H.
Sai Asa ya ɗauki dukan azurfa da kuma zinariyar da suka rage a ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma nasa fadan, ya ba da su ga wani shugabansa, ya kuma aika da su zuwa ga Ben-Hadad ɗan Tabrimmon, ɗan Heziyon, sarkin Aram, wanda yake mulki a Damaskus.
- 1 Sarakuna 15:19kusan 930 K.H.
Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakanina da kai, kamar yadda ta kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Duba, ina aika maka kyautai na azurfa da na zinariya. Yanzu fa sai ka janye yarjejjeniyarka da Ba’asha sarkin Isra’ila, don yă janye daga gare ni.”
- 1 Sarakuna 15:20kusan 930 K.H.
Ben-Hadad ya yarda da maganar Sarki Asa, ya kuma aika shugabannin sojojin mayaƙansa ya yi yaƙi da garuruwan Isra’ila. Ya kame Iyon, Dan, Abel-Bet-Ma’aka da dukan Kinneret, haɗe da Naftali.
- 1 Sarakuna 15:21kusan 930 K.H.
Da Ba’asha ya ji haka, sai ya daina ginin Rama, ya janye zuwa Tirza.
- 1 Sarakuna 15:22kusan 930 K.H.
Sai Sarki Asa ya ba da umarni ga dukan Yahuda, kuma babu wanda aka ware, kowa yă taimaka a kwashe duwatsu da katakan da Ba’asha yake amfani da su daga Rama. Da duwatsu da katakan ne Sarki Asa ya gina Geba a Benyamin da kuma Mizfa.
- 1 Sarakuna 15:23kusan 930 K.H.
Game da sauran ayyukan mulkin Asa, dukan nasarorinsa, dukan abin da ya yi, da kuma biranen da ya gina, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. A tsufansa, sai ƙafafunsa suka kamu da cuta.
- 1 Sarakuna 15:24kusan 914 K.H.
Sai Asa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a birnin kakansa Dawuda. Sai Yehoshafat ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
- 1 Sarakuna 15:25kusan 954 K.H.
Nadab ɗan Yerobowam ya zama sarkin Isra’ila a shekara ta biyu ta Asa sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila shekara biyu.
- 1 Sarakuna 15:26kusan 954 K.H.
Ya yi mugunta a gaban Ubangiji, yana tafiya a hanyoyin mahaifinsa da kuma cikin zunubinsa, wanda ya sa Isra’ila suka yi.
- 1 Sarakuna 15:27kusan 954 K.H.
Ba’asha ɗan Ahiya na gidan Issakar ya yi maƙarƙashiya gāba da shi, ya buge shi a Gibbeton, a wani garin Filistiyawa, yayinda Nadab da dukan Isra’ila suke wa garin kwanto.