Tsallake zuwa abun ciki

circa 930–586 BC

The Divided Kingdom

The kingdom splits into Israel and Judah; prophets warn of judgment as both nations slowly drift into idolatry and exile.

1,722 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ka aikata mugunta fiye da dukan waɗanda suka rayu kafin kai. Ka yi wa kanka waɗansu alloli, gumakan da aka yi da ƙarfe; ka tsokane ni na yi fushi, ka kuma juye mini baya.

  2. “ ‘Saboda wannan, zan kawo masifa a gidan Yerobowam. Zan yanke kowane ɗa na ƙarshe a Isra’ila, bawa ko ’yantacce. Zan ƙone gidan Yerobowam kamar yadda mutum yakan ƙone juji, sai duk ya ƙone ƙurmus.

  3. Karnuka za su ci waɗanda suka mutu na Yerobowam a cikin birni, kuma tsuntsayen sararin sama za su cinye waɗanda suka mutu a jeji. Ni Ubangiji na faɗa!’

  4. “Ke kuma, ki koma gida. Sa’ad da kika taka ƙafa a birninki, yaron zai mutu.

  5. Dukan Isra’ila kuwa za su yi makoki dominsa. Shi ne kaɗai na Yerobowam wanda za a binne, domin shi ne kaɗai a gidan Yerobowam wanda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya sami wani ɗan abu mai kyau a kansa.

  6. “Ubangiji zai tā da wani sarki wa kansa a bisa Isra’ila wanda zai hallaka iyalin Yerobowam. Ko yanzu ma, wannan zai fara faruwa.

  7. Ubangiji kuma zai bugi Isra’ila, har tă zama kamar kyauro mai girgiza a bakin rafi. Zai tumɓuke Isra’ila daga wannan ƙasa mai kyau da ya ba wa kakanninsu, yă watsar da su gaba da Kogin Yuferites domin sun tsokane Ubangiji har ya yi fushi, ta wurin yin ginshiƙan Ashera.

  8. Zai kuma ba da Isra’ila saboda zunuban da Yerobowam ya yi, da ya kuma sa Isra’ila suka yi.”

  9. Sai matar Yerobowam ta tashi ta tafi, ta kuwa tafi Tirza. Nan da nan da ta taka madogarar ƙofar gidan, sai yaron ya mutu.

  10. Suka binne shi, dukan Isra’ila kuwa suka yi makoki dominsa, yadda Ubangiji ya faɗa ta wurin bawansa annabi Ahiya.

  11. 1 Sarakuna 14:19kusan 975 K.H.

    Sauran ayyukan sarautar Yerobowam, da yaƙe-yaƙensa, da yadda ya yi mulki, ba a rubuce suke a littafin tarihi na sarakunan Isra’ila ba?

  12. 1 Sarakuna 14:20kusan 975 K.H.

    Ya yi mulki shekaru ashirin da biyu, sai ya huta tare da kakanninsa. Sai Nadab ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  13. 1 Sarakuna 14:21kusan 975 K.H.

    Rehobowam ɗan Solomon ya zama sarki a Yahuda. Yana da shekara arba’in da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekaru goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga cikin dukan kabilan Isra’ila don yă sa Sunansa. Sunan mahaifiyarsa Na’ama, ita mutuniyar Ammon ce.

  14. 1 Sarakuna 14:22kusan 975 K.H.

    Yahuda ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Ta wurin zunuban da suka yi, sun tā da fushin kishinsa fiye da yadda kakanninsu suka yi.

  15. 1 Sarakuna 14:23kusan 975 K.H.

    Sun kuma kafa wa kansu masujadai da suke kan tuddai, da a kan keɓaɓɓun duwatsu, suka kuma gina ginshiƙan Ashera a kowane tudu, da kuma a ƙarƙashin kowane duhuwar itace.

  16. 1 Sarakuna 14:24kusan 975 K.H.

    Har ma akwai maza karuwai na masujada. Mutane suka sa kansu ga yin kowane abin ƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora kafin Isra’ilawa.

  17. 1 Sarakuna 14:25kusan 970 K.H.

    A shekara ta biyar ta Sarki Rehobowam, Shishak sarkin Masar ya kai wa Urushalima yaƙi.

  18. 1 Sarakuna 14:26kusan 970 K.H.

    Ya kwashe dukiyar haikalin Ubangiji da kuma dukiyar fadan sarki. Ya ɗauki kome, har da dukan garkuwoyi na zinariya da Solomon ya yi.

  19. 1 Sarakuna 14:27kusan 970 K.H.

    Saboda haka sarki Rehobowam ya yi garkuwoyin tagulla ya mayar da su. Ya kuma naɗa waɗannan shugabannin matsara ya sa su aiki a ƙofar zuwa fadan sarki.

  20. 1 Sarakuna 14:28kusan 970 K.H.

    Duk sa’ad da sarki ya tafi wurin haikalin Ubangiji, matsara sukan riƙe garkuwoyinsu, daga baya kuma sai su mai da su ɗakin tsaro.

  21. 1 Sarakuna 14:29kusan 975 K.H.

    Game da sauran ayyukan mulkin Rehobowam kuwa, da kuma dukan abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.

  22. 1 Sarakuna 14:30kusan 975 K.H.

    Aka ci gaba da yaƙe-yaƙe tsakanin Rehobowam da Yerobowam.

  23. 1 Sarakuna 14:31kusan 958 K.H.

    Sai Rehobowam ya huta da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda. Sunan mahaifiyarsa Na’ama, ita kuwa mutuniyar Ammon ce. Sai Abiyam ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  24. A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yerobowam ɗan Nebat, Abiyam ya zama sarkin Yahuda,

  25. ya kuma yi mulki a Urushalima shekara uku. Sunan mahaifiyarsa Ma’aka ne, ’yar Abisalom.