- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 930–586 BC
The Divided Kingdom
The kingdom splits into Israel and Judah; prophets warn of judgment as both nations slowly drift into idolatry and exile.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Tarihi 11:6kusan 975 K.H.
Betlehem, Etam, Tekowa,
- 2 Tarihi 11:7kusan 975 K.H.
Bet-Zur, Soko, Adullam,
- 2 Tarihi 11:8kusan 975 K.H.
Gat, Maresha, Zif,
- 2 Tarihi 11:9kusan 975 K.H.
Adorayim, Lakish, Azeka,
- 2 Tarihi 11:10kusan 975 K.H.
Zora, Aiyalon da Hebron. Waɗannan su ne garuruwan katanga a cikin Yahuda da Benyamin.
- 2 Tarihi 11:11kusan 975 K.H.
Ya ƙarfafa kāriyarsu ya kuma sa shugabannin mayaƙa a cikinsu, tare da tanadin abinci, man zaitun da kuma ruwan inabi.
- 2 Tarihi 11:12kusan 975 K.H.
Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen, ya kuma sa suka zama da ƙarfi. Saboda haka Yahuda da Benyamin suka zama nasa.
- 2 Tarihi 11:13kusan 974 K.H.
Firistoci da Lawiyawa daga dukan yankuna ko’ina a Isra’ila suka haɗa kai da shi.
- 2 Tarihi 11:14kusan 974 K.H.
Lawiyawa suka ma bar makiyayansu da mallakarsu, suka zo Yahuda da Urushalima domin Yerobowam da ’ya’yansa maza sun ƙi su a matsayin firistocin Ubangiji.
- 2 Tarihi 11:15kusan 974 K.H.
Yerobowam ya naɗa firistocinsa domin masujadan kan tudu da kuma domin gumakan nan na akuya da maraƙin da ya yi.
- 2 Tarihi 11:16kusan 974 K.H.
Waɗanda suke daga kowane kabilar Isra’ila waɗanda suka sa zuciya a kan neman Ubangiji, Allah na Isra’ila, suka bi Lawiyawa zuwa Urushalima don su miƙa hadayu ga Ubangiji Allah na kakanninsu.
- 2 Tarihi 11:17kusan 975 K.H.
Suka ƙarfafa mulkin Yahuda suka kuma goyi bayan Rehobowam ɗan Solomon shekaru uku, suna tafiya a hanyoyin Dawuda da Solomon a wannan lokaci.
- 2 Tarihi 11:18kusan 975 K.H.
Rehobowam ya auri Mahalat, ’yar Yerimot ɗan Dawuda wadda Abihayil ’yar Eliyab ɗan Yesse ta haifa.
- 2 Tarihi 11:19kusan 975 K.H.
Ta haifa masa ’ya’ya maza. Yewush, Shemariya da Zaham.
- 2 Tarihi 11:20kusan 975 K.H.
Sa’an nan ya auri Ma’aka ’yar Absalom, wadda ta haifa masa Abiya, Attai, Ziza da kuma Shelomit.
- 2 Tarihi 11:21kusan 975 K.H.
Rehobowam ya ƙaunaci Ma’aka ’yar Absalom fiye da sauran matansa da ƙwarƙwaransa. Duka-duka dai ya auri mata goma sha takwas da ƙwarƙwarai sittin, yana da ’ya’ya maza ashirin da takwas da ’ya’ya mata sittin.
- 2 Tarihi 11:22kusan 975 K.H.
Rehobowam ya naɗa Abiya ɗan Ma’aka yă zama babba yerima a cikin ’yan’uwansa, don dai yă naɗa shi sarki.
- 2 Tarihi 11:23kusan 975 K.H.
Ya yi hikima, ya watsar da waɗansu ’ya’yansa a dukan yankunan Yahuda da Benyamin, da kuma a dukan birane masu katanga. Ya ba su tanadi mai yawa ya kuma aurar musu mata masu yawa.
- 2 Tarihi 12:1kusan 972 K.H.
Bayan mulkin Rehobowam ya kahu kamar sarki ya kuma yi ƙarfi, shi da dukan Isra’ila suka yi biris da dokar Ubangiji.
- 2 Tarihi 12:2kusan 970 K.H.
Domin sun yi rashin biyayya ga Ubangiji, saboda haka Shishak sarkin Masar ya yaƙi Urushalima a shekara ta biyar ta Sarki Rehobowam.
- 2 Tarihi 12:3kusan 970 K.H.
Da kekunan yaƙi dubu ɗaya da ɗari biyu da kuma mahayan dawakai dubu haɗe da mayaƙan Libiyawa, Sukkatawa da kuma Kushawa waɗanda suka wuce ƙidaya suka zo tare da shi daga Masar,
- 2 Tarihi 12:4kusan 970 K.H.
ya ci biranen katanga na Yahuda har zuwa Urushalima.
- 2 Tarihi 12:5kusan 970 K.H.
Sai annabi Shemahiya ya zo wurin Rehobowam da kuma wajen shugabannin Yahuda waɗanda suka taru a Urushalima don tsoron Shishak, ya kuma faɗa musu, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Kun yi biris da ni; saboda haka, yanzu na bashe ku ga Shishak.’ ”
- 2 Tarihi 12:6kusan 970 K.H.
Shugabannin Isra’ila da sarki suka ƙasƙantar da kansu suka ce, “Ubangiji mai adalci ne.”
- 2 Tarihi 12:7kusan 970 K.H.
Sa’ad da Ubangiji ya ga sun ƙasƙantar da kansu, sai wannan maganar Ubangiji ta zo wa Shemahiya, “Tun da yake sun ƙasƙantar da kansu, to, ba zan hallaka su ba, amma zan cece su, ba zan kwararo fushina ta hannun Shishak a kan Urushalima ba.