- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 930–586 BC
The Divided Kingdom
The kingdom splits into Israel and Judah; prophets warn of judgment as both nations slowly drift into idolatry and exile.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Tarihi 13:17kusan 958 K.H.
Abiya da mutanensa suka kashe su sosai, har mutum dubu ɗari biyar suka mutu a cikin jarumawan Isra’ila.
- 2 Tarihi 13:18kusan 958 K.H.
Aka cinye mutanen Isra’ila a wannan lokaci, mutanen Yahuda kuwa suka yi nasara domin sun dogara ga Ubangiji Allah na kakanninsu.
- 2 Tarihi 13:19kusan 958 K.H.
Abiya ya kori Yerobowam ya kuma ƙwace garuruwan Betel, Yeshana da Efron, tare da ƙauyukan da suke kewaye daga gare shi.
- 2 Tarihi 13:20kusan 958 K.H.
Yerobowam bai sāke yin ƙarfi a zamanin Abiya ba. Ubangiji ya buge shi ya kuma mutu.
- 2 Tarihi 13:21kusan 958 K.H.
Amma Abiya ya ƙara ƙarfi. Ya auri mata goma sha huɗu, ya kuma kasance da ’ya’ya maza ashirin da biyu da kuma ’ya’ya mata goma sha shida.
- 2 Tarihi 13:22kusan 958 K.H.
Sauran ayyukan sauratar Abiya, abin da ya yi da abin da ya faɗa, a rubuce suke a cikin rubuce-rubucen annabi Iddo.
- 2 Tarihi 14:1kusan 955 K.H.
Abiya kuwa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Asa ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki, a zamaninsa kuma ƙasar ta zauna lafiya na shekara goma.
- 2 Tarihi 14:2kusan 941 K.H.
Asa ya yi abin da yake da kyau da kuma daidai a gaban Ubangiji Allahnsa.
- 2 Tarihi 14:3kusan 941 K.H.
Ya kawar da baƙin bagade da masujadai bisa tudu, ya farfashe keɓaɓɓun duwatsu, ya kuma sassare ginshiƙan Ashera.
- 2 Tarihi 14:4kusan 941 K.H.
Ya umarci Yahuda su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, su kuma yi biyayya da dokoki da kuma umarnansa.
- 2 Tarihi 14:5kusan 941 K.H.
Ya kawar da masujadan kan tudu da bagadan turare a kowane gari a Yahuda, masarautar kuwa ta zauna lafiya a ƙarƙashinsa.
- 2 Tarihi 14:6kusan 941 K.H.
Ya gina biranen katanga na Yahuda, da yake ƙasar tana zaman lafiya. Babu wanda yake yaƙi da shi a waɗannan shekaru, gama Ubangiji ya ba shi hutu.
- 2 Tarihi 14:7kusan 941 K.H.
Ya ce wa Yahuda, “Bari mu gina waɗannan garuruwa mu sa katanga kewaye da su, da hasumiyoyi, ƙofofi da ƙyamare. Ƙasar har yanzu tamu ce domin mun nemi Ubangiji Allahnmu, mun neme shi ya kuwa ba mu hutu a kowane gefe.” Saboda haka suka gina suka kuma yi nasara.
- 2 Tarihi 14:8kusan 941 K.H.
Asa ya kasance da mayaƙa dubu ɗari uku daga Yahuda, kintsatse da manyan garkuwoyi da māsu, da kuma mayaƙa dubu ɗari biyu da dubu tamanin daga Benyamin, riƙe da ƙananan garkuwoyi da kuma baka. Dukan waɗannan jarumawa ne ƙwarai.
- 2 Tarihi 14:9kusan 941 K.H.
Zera mutumin Kush ya taka ya fita don yă yaƙe su da babban runduna da kuma kekunan yaƙi ɗari uku, ya kuma zo har Maresha.
- 2 Tarihi 14:10kusan 941 K.H.
Asa ya fita don yă ƙara da shi, suka ja dāgā yaƙi a Kwarin Zefata kusa da Maresha.
- 2 Tarihi 14:11kusan 941 K.H.
Sai Asa ya kira ga Ubangiji Allahnsa ya ce, “Ubangiji, babu wani kamar ka da zai taimaki marar ƙarfi a kan mai ƙarfi. Ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama mun dogara a gare ka, kuma a cikin sunanka muka fito don mu yaƙi wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu; kada ka bar mutum yă yi nasara a kanka.”
- 2 Tarihi 14:12kusan 941 K.H.
Ubangiji fa ya bugi mutanen Kush a gaban Asa da Yahuda. Mutanen Kush suka gudu,
- 2 Tarihi 14:13kusan 941 K.H.
Asa kuwa da mayaƙansa suka bi su har Gerar. Mutanen Kush suka mutu a ranan nan har ba a iya ƙidaya, aka buge su a gaban Ubangiji da rundunansa. Mutanen Yahuda suka kwashi ganima sosai.
- 2 Tarihi 14:14kusan 941 K.H.
Suka hallaka dukan ƙauyukan kewaye da Gerar, gama tsoron Ubangiji ya kama su. Suka kwashi ganima na dukan ƙauyukan nan, da yake akwai ganima sosai a can.
- 2 Tarihi 14:15kusan 941 K.H.
Suka kuma yaƙi sansanin makiyaya suka kwashe tumaki da awaki da raƙuma. Suka koma Urushalima.
Sai Ruhun Allah ya sauko a kan Azariya ɗan Oded.
Ya fita ya je ya sadu da Asa ya kuma faɗa masa, “Ka saurare ni, Asa da kuma dukan Yahuda da Benyamin. Ubangiji yana tare da ku sa’ad da kuke tare da shi. In kuka neme shi, za ku same shi, amma in kuka yashe shi, zai yashe ku.
Tun da daɗewa Isra’ila ba su da Allah na gaskiya, babu firist da zai koyar, kuma babu doka.
Amma cikin wahalarsu suka juya ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, suka kuma neme shi, suka kuwa same shi.