Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wine

175 ayoyi · 83 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai ya ce musu, “Wannan jinina ne na alkawari, wanda aka zubar da shi saboda mutane da yawa.

  2. Sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, don yă rage zafi, amma bai sha ba.

  3. gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa.

  4. Kuma ba wanda yakan so shan sabon ruwan inabi bayan ya sha tsohon, don yakan ce, ‘Ai, tsohon ya fi kyau.’ ”

  5. Ya je wurinsa, ya daddaure masa raunukansa, sa’an nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa.

  6. Bayan ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, sai ya ce, “Ku karɓa, ku rarraba wa junanku.

  7. Ina dai gaya muku, ba zan ƙara sha daga ’ya’yan inabi ba, sai mulkin Allah ya zo.”

  8. Sai ya ɗauki burodi ya yi godiya, ya kakkarya ya ba su, da cewa, “Wannan jikina ne, da aka bayar dominku. Ku riƙa yin haka don tunawa da ni.”

  9. Haka kuma, bayan abincin, ya ɗauki kwaf ruwan inabi ya ce, “Wannan kwaf ruwan inabi shi ne, na sabon alkawari cikin jinina, da aka zubar dominku.

  10. Sojoji su ma, suka zo suka yi masa ba’a. Suka miƙa masa ruwan tsami.

  11. Da ruwan inabi ya ƙare, sai mahaifiyar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.”

  12. Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya

  13. ya ce, “Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu.”

  14. Sai Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, sai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba.

  15. Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.

  16. Gama naman jikina abinci ne na gaskiya jinina kuma abin sha ne na gaskiya.

  17. Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana cikina, ni kuma ina cikinsa.

  18. To, akwai wani tulun ruwan tsami ajiye a can, saboda haka suka jiƙa soso da shi, suka soka soson a sandan itacen hizzob, suka kai bakin Yesu.

  19. Ya fi kyau kada ka ci nama ko ka sha ruwan inabi ko kuma ka yi wani abin da zai sa ɗan’uwanka yă fāɗi.

  20. Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu.

  21. Ka daina shan ruwa kaɗai, yi amfani da ruwan inabi kaɗan saboda cikinka da kuma yawan rashin lafiyarka.

  22. Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari.

  23. Da ita ce sarakunan duniya suka yi zina mazaunan duniya kuma suka bugu da ruwan inabin zinace zinacenta.”

  24. Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabin haukan zinace zinacenta. Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita, attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”

  25. kayayyakin sinnamon da kayan yaji, na turaren wuta, mur da turare, na ruwan inabi da man zaitun, na gari mai laushi da alkama; shanu da tumaki; dawakai da kekunan doki, da jikuna da kuma rayukan mutane.