Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wine

175 ayoyi · 83 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Nuhu, mutumin ƙasa, shi ne farko da ya fara yin gonar inabi.

  2. Sa’ad da ya sha ruwan inabin ya kuwa bugu, sai ya kwanta tsirara cikin tentinsa.

  3. Sai Melkizedek sarkin Salem ya kawo burodi da ruwan inabi. Shi firist ne na Allah Mafi Ɗaukaka,

  4. Sa’an nan ya ce, “Ɗana, kawo mini naman da ka farauto in ci, domin in sa maka albarka.” Yaƙub ya kawo masa ya kuwa ci; ya kuma kawo masa ruwan inabi ya kuma sha.

  5. Allah yă ba ka daga raɓar sama da kuma yalwar ƙasa, yalwar hatsi da sabon ruwan inabi.

  6. Ishaku ya amsa wa Isuwa, “Na mai da shi shugaba a kanka, na sa dukan dangoginsa su zama bayinsa, na kuma ba shi hatsi da sabon ruwan inabi. Saboda haka me kuma zan yi maka ɗana?”

  7. Kwaf Fir’auna kuwa yana a hannuna, na kuma ɗiba inabin na matse su cikin kwaf Fir’auna, na kuma sa kwaf ɗin a hannunsa.”

  8. “Yahuda, ’yan’uwanka za su yabe ka; hannuwanka za su kasance a wuyan abokan gābanka, ’ya’yan mahaifinka maza za su rusuna maka.

  9. Zai daure jakinsa a kuringa, aholakinsa a rassa mafi kyau; zai wanke tufafinsa cikin ruwan inabi rigunansa cikin inabi ja wur kamar jini.

  10. Idanunsa za su duhunce fiye da ruwan inabi, haƙorarsa farare kamar madara.

  11. Haɗe da ɗan rago na farkon, ka miƙa mudun gari mai laushi wanda an gauraye da kwalaba ɗaya na tataccen mai zaitun, da kwalaba ɗaya na ruwan inabi don hadaya ta sha.

  12. “Kai da ’ya’yanka maza, ba za ku sha ruwan inabi ko wani abu mai sa jiri ba a duk sa’ad da za ku shiga cikin Tentin Sujada, in ba haka ba za ku mutu. Wannan dawwammamiyar farilla ce wa tsararraki masu zuwa.

  13. tare da hadaya ta gari mai laushi, humushi biyu haɗe da mai, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji, mai daɗin ƙanshi, da kuma abin sha kwalaba ɗaya na ruwan inabi.

  14. dole yă keɓe kansa daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye, kada kuma yă sha ruwan tsamin da aka yi daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye. Ba zai sha ruwan ’ya’yan inabi, ko yă ci ’ya’yan inabi ɗanye ko busasshe ba.

  15. sai shi wanda ya kawo hadayar yă miƙa wa Ubangiji hadaya ta gari mai laushi mai kyau, kashi ɗaya bisa goma na efa wanda aka kwaɓa da kwalaba ɗaya na mai.

  16. Da kowane ɗan rago don hadaya ta ƙonawa, a shirya kwalaba ɗaya na ruwan inabi, a matsayin hadaya ta sha.

  17. “ ‘In da rago ne za a miƙa, to, sai a shirya hadaya ta gari mai laushi, garin yă zama kashi biyu bisa goma na efa. A kwaɓa shi da kashi ɗaya bisa uku na garwan mai,

  18. da kashi ɗaya bisa uku na garwan ruwan inabi, a matsayin hadaya ta sha. A miƙa ta abin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

  19. “ ‘Sa’ad da kuka shirya rago don hadaya ta ƙonawa saboda alkawari na musamman, ko hadaya ta salama ga Ubangiji,

  20. sai ku kawo hadaya ta gari tare da bijimi, kashi ɗaya bisa uku na gari mai laushi kwaɓaɓɓe da rabin garwan mai.

  21. A kuma kawo rabin garwan ruwan inabi na hadaya ta sha. Za tă zama hadayar da aka yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

  22. Hadaya ta sha, za tă zama kwalaba ɗaya na ruwan inabi, da ɗan rago guda. Za a kwarara hadaya ta sha ga Ubangiji a wuri mai tsarki.

  23. Da kowane bijimi, za a kasance da hadaya ta sha, na rabin kwalabar ruwan inabi; da rago kuwa, a kasance da kashi ɗaya bisa uku; da kowace tunkiya kuma, a kasance da kashi ɗaya bisa huɗu. Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa don tsayawar kowane sabon wata na shekara.

  24. Yi amfani da kuɗin ku saya duk abin da kuke so, ko shanu, ko tumaki, ko ruwan inabi, ko dai wani abin shan da ya yi tsami, ko kuwa duk abin da kuke so. Sai ku da gidanku, ku ci a can, a gaban Ubangiji Allahnku, ku kuma yi farin ciki.

  25. Za ku ba su nunan fari na hatsinku, da sabon ruwan inabinku, da manku, da kuma gashi na fari daga askin da kuka yi na tumakinku.