Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wine: Moab

5 ayoyi · 83 fannoni

Ayoyi game da Moab

  1. Gonakin Heshbon sun bushe, inabin Sibma ma haka. Masu mulkin al’ummai sun tattake inabi mafi kyau, waɗanda suka taɓa yaɗuwa zuwa Yazer suka bazu ta wajen hamada. Tohonsu sun buɗu suka kai har teku.

  2. Saboda haka na yi kuka, yadda Yazer take kuka, saboda inabin Sibma. Ya Heshbon, ya Eleyale, na cika ku da hawaye! Sowa ta murna a kanku saboda ’ya’yan itatuwanku da suka nuna da kuma girbinku sun ɓace.

  3. An ɗauke farin ciki da murna daga gonakin itatuwa masu ’ya’ya; babu wanda yake rerawa ko yake sowa a cikin gonakin inabi; babu wanda yake matsin ruwan inabi a wuraren matsi, gama na kawo ƙarshen yin sowa.

  4. Zan yi kuka saboda kai, yadda Yazer ya yi kuka Ya kuringar Sibma. Rassanki sun kai har teku; sun kai har tekun Yazer. Mai hallakarwa ya fāɗo a kan ’ya’yan itatuwanku da kuma inabinku da suka nuna.

  5. Farin ciki da murna su ɓace daga lambunan itatuwa da kuma gonakin Mowab. Na dakatar da malalar ruwan inabi daga wurin matsi; ba wanda zai matse su da ihun farin ciki. Ko da yake akwai sowa sowar ba ta farin ciki ba ce.