Skip to content

Jonadab

9 ayoyi · 1 ɗan gida

An kuma san shi da: Jehonadab

Ayoyin da suka ambaci Jonadab

  1. Bayan ya bar wurin, sai ya gamu da Yehonadab ɗan Rekab wanda yake kan hanyarsa don yă sadu da shi. Sai Yehu ya gaishe shi, ya ce, “Ka amince da ni yadda na amince da kai?” Yehonadab ya ce, “I.” Yehu ya ce, “To, in haka ne ka ba ni hannunka.” Sai ya miƙa masa, Yehu kuwa ya ja shi cikin keken yaƙin.

  2. Sa’an nan Yehu da Yehonadab ɗan Rekab, suka shiga haikalin Ba’al. Yehu ya ce wa masu yi wa Ba’al sujada, “Ku dudduba ku tabbatar cewa babu wani bawan Ubangiji a nan tare da ku, sai masu hidimar Ba’al kawai.”

  3. Amma sai suka amsa suka ce, “Ba ma shan ruwan inabi, domin kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu cewa, ‘Ko ku, ko zuriyarku kada ku sha ruwan inabi.

  4. Mun yi biyayya da kome da kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu. Mu ko matanmu ko ’ya’yanmu maza da mata ba mu taɓa shan ruwan inabi ba

  5. Mun yi rayuwarmu a cikin tentuna mun kuma yi biyayya ƙwarai da kowane abin da kakanmu Yehonadab ya umarce mu.

  6. ‘Yehonadab ɗan Rekab ya umarci ’ya’yansa maza kada su sha ruwan inabi sun kuma kiyaye wannan umarni. Har yă zuwa yau ba sa shan ruwan inabi, domin sun yi biyayya da umarnin kakansu. Amma na yi muku magana sau da sau, duk da haka ba ku yi biyayya ba.

  7. Zuriyar Yehonadab ɗan Rekab sun yi biyayya da umarnin da kakansu ya ba su, amma waɗannan mutane ba su yi mini biyayya ba.’

  8. Sai Irmiya ya ce wa iyalin Rekabawa, “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kun yi biyayya da umarnin kakanku Yehonadab kuka kuma kiyaye dukan umarnansa kuka yi kome bisa ga tsari.’

  9. Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Yehonadab ɗan Rekab ba zai taɓa rasa mutumin da zai yi mini hidima ba.’ ”