Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wine: Fermented

8 ayoyi · 83 fannoni

Ayoyi game da Fermented

  1. “Kai da ’ya’yanka maza, ba za ku sha ruwan inabi ko wani abu mai sa jiri ba a duk sa’ad da za ku shiga cikin Tentin Sujada, in ba haka ba za ku mutu. Wannan dawwammamiyar farilla ce wa tsararraki masu zuwa.

  2. dole yă keɓe kansa daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye, kada kuma yă sha ruwan tsamin da aka yi daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye. Ba zai sha ruwan ’ya’yan inabi, ko yă ci ’ya’yan inabi ɗanye ko busasshe ba.

  3. Hadaya ta sha, za tă zama kwalaba ɗaya na ruwan inabi, da ɗan rago guda. Za a kwarara hadaya ta sha ga Ubangiji a wuri mai tsarki.

  4. Yi amfani da kuɗin ku saya duk abin da kuke so, ko shanu, ko tumaki, ko ruwan inabi, ko dai wani abin shan da ya yi tsami, ko kuwa duk abin da kuke so. Sai ku da gidanku, ku ci a can, a gaban Ubangiji Allahnku, ku kuma yi farin ciki.

  5. Ba ku ci burodi ba, ba ku kuwa sha ruwan inabi, ko wani abu mai sa jiri ba. Ya yi haka don ku san cewa shi ne Ubangiji Allahnku.

  6. Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja, sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya, sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro!

  7. A ƙarshe yana sara kamar maciji da kuma dafi kamar gamsheƙa.

  8. Ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ya yi haka, ruwan inabin zai farfashe salkunan, yă yi hasarar ruwan inabin, salkunan kuma su lalace. A’a, yakan zuba sabon ruwan inabin a sababbin salkuna.”