Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wine: Generally made by treading the grapes in a press
Ayoyi game da Generally made by treading the grapes in a press
A waɗannan kwanaki, na ga mutane a Yahuda suna matse ruwan inabi a ranar Asabbaci suna kuma kawo hatsi suna labta su a kan jakuna, tare da ruwan inabi, ’ya’yan inabi, ɓaure da kaya iri-iri. Suna kuma kawowa dukan wannan cikin Urushalima a ranar Asabbaci. Saboda haka na gargaɗe su a kan sayar da abinci a wannan rana.
Me ya sa rigunanka suka yi ja, sai ka ce na wanda yake tattaka ’ya’yan inabi?
“Na tattake ’ya’yan inabi ni kaɗai; cikin al’ummai kuma babu wani tare da ni. Na tattake su cikin fushina Na matse su cikin hasalata; jininsu ya fantsamar wa rigunana, na kuma ɓata dukan tufafina.