Skip to content

Jazer

12 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Jaazer

31.9400, 35.7200 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Jazer

  1. Sai Musa ya aika ’yan leƙen asiri zuwa Yazer. Daga baya, sai Isra’ilawa suka ci ƙauyukan da suke kewaye, suka kuma kori Amoriyawa da suke zaune a can.

  2. Mutanen Ruben da mutanen Gad, da suke da garken shanu da kuma garke tumaki masu yawa, suka ga cewa ƙasashen Yazer da Gileyad wurare ne masu kyau don kiwon shanu da tumaki.

  3. “Atarot, Dibon, Yazer, Nimra, Heshbon, Eleyale, Sebam, Nebo da Beyon,

  4. Atrot Shofan, Yazer, Yogbeha,

  5. Yankin ƙasarsu ya ƙunshi Yazer, da dukan garuruwan Gileyad, da rabin ƙasar Ammonawa har zuwa Arower kusa da Rabba,

  6. Heshbon da kuma Yazer, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan.

  7. Bayan suka ƙetare Urdun, sai suka yi sansani kusa da Arower, kudu da garin da yake cikin kwari, sa’an nan suka ratsa ta wajen Gad, suka ci gaba zuwa Yazer.

  8. Heshbon da Yazer, tare da wuraren kiwonsu.

  9. Game da zuriyar Hebron kuwa, Yeriya ne babba bisa ga tarihin zuriyar iyalansu. A shekara ta arba’in ta sarautar Dawuda, sai aka yi binciken tarihi, aka tarar jarumawa cikin zuriyar Hebron suna zama a Yazer cikin Gileyad ne.

  10. Gonakin Heshbon sun bushe, inabin Sibma ma haka. Masu mulkin al’ummai sun tattake inabi mafi kyau, waɗanda suka taɓa yaɗuwa zuwa Yazer suka bazu ta wajen hamada. Tohonsu sun buɗu suka kai har teku.

  11. Saboda haka na yi kuka, yadda Yazer take kuka, saboda inabin Sibma. Ya Heshbon, ya Eleyale, na cika ku da hawaye! Sowa ta murna a kanku saboda ’ya’yan itatuwanku da suka nuna da kuma girbinku sun ɓace.

  12. Zan yi kuka saboda kai, yadda Yazer ya yi kuka Ya kuringar Sibma. Rassanki sun kai har teku; sun kai har tekun Yazer. Mai hallakarwa ya fāɗo a kan ’ya’yan itatuwanku da kuma inabinku da suka nuna.