Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Heshbon

18 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Isra’ila suka ci dukan biranen Amoriyawa, suka kuma zauna a cikinsu, haɗe da babban birnin Heshbon da dukan ƙauyukanta.

  2. Sihon sarkin Amoriyawa ya yi mulkin Heshbon, bayan ya ci sarkin Mowab na dā da yaƙi, ya kuma ƙwace dukan ƙasarsa har zuwa arewancin kogin Arnon.

  3. Shi ya sa Amoriyawa suka rubuta wannan waƙa game da Heshbon suka ce, “Ku zo mu sāke gina Heshbon, birnin Sihon.

  4. “Mayaƙansa sun fito kamar harshen wuta suka ƙone birnin Ar na Mowab suna hallaka ’yan ƙasar tuddan Arnon.

  5. Kaitonki, Mowab! Gunkinki Kemosh ya yashe mutanenki; aka kuma kama su, aka kai su bauta wajen Sihon sarkin Amoriyawa.

  6. “Amma mun tumɓuke su, mun hallaka garuruwan Heshbon har zuwa Dibon. Mun ragargaza su har zuwa Nofa wanda ya miƙe zuwa Medeba.”

  7. Ta haka Isra’ila suka zauna a ƙasar Amoriyawa.

  8. Sai Musa ya aika ’yan leƙen asiri zuwa Yazer. Daga baya, sai Isra’ilawa suka ci ƙauyukan da suke kewaye, suka kuma kori Amoriyawa da suke zaune a can.

  9. Sai suka juya suka haura kan hanya ta zuwa Bashan, inda Og yake sarauta, ya kuwa fito tare da dukan sojojinsa suka yi yaƙi da Isra’ila a Edireyi.

  10. Ubangiji ya ce wa Musa, “Kada ka ji tsoronsa, gama na ba da shi a gare ka, da dukan sojojinsa da kuma ƙasarsa. Ka yi da shi yadda ka yi da Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon.”

  11. Ta haka suka kashe shi, tare da ’ya’yansa maza da kuma dukan sojojinsa, ba wanda ya ragu. Suka kuma mamaye ƙasarsa.

  12. daga kabilar Gad kuwa aka ba su, Ramot Gileyad (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), Mahanayim,

  13. Heshbon da kuma Yazer, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan.

  14. “Muryar kukansu na tashi daga Heshbon zuwa Eleyale da Yahaz, daga Zowar har zuwa Horonayim da Eglat Shelishiya, gama har ruwan Nimrim ma sun bushe.

  15. A Mowab zan kawo ƙarshen waɗanda suke miƙa hadayu a masujadan kan tudu suna kuma ƙone turare ga allolinsu,” in ji Ubangiji.

  16. Game da Ammonawa. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Isra’ila ba shi da ’ya’ya maza ne? Ba shi da magāda ne? To, me ya sa Molek ya mallaki Gad? Me ya sa mutanensa suka zama a garuruwansa?

  17. Amma kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan yi kirarin yaƙi a kan Rabba ta Ammonawa; zai zama tarin juji, za a sa wuta a ƙauyukan da suke kewayenta. Sa’an nan Isra’ila zai kori waɗanda suka kore shi,” in ji Ubangiji.

  18. “Ki yi kuka, ya Heshbon, gama an hallaka Ai! Ku tā da murya ku yi kuka, ya mazaunan Rabba! Ku sa tufafin makoki; ku ruga nan da can a cikin katanga, gama Molek zai tafi bauta, tare da firistocinsa da kuma fadawansa.