Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Warfare of Saints

107 ayoyi · 73 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Zan fanshe su daga ikon kabari; zan cece su daga mutuwa. Ina annobanki, ya mutuwa? Ina hallakarka, ya kabari? “Ba zan ji tausayi ba,

  2. Gama ɗa yakan ce wannan ba mahaifinsa ba ne, diya kuma takan tayar wa mahaifiyarta, matar ɗa takan yi gāba da uwar mijinta, abokan gāban mutum su ne iyalin cikin gidansa.

  3. Kada ku yi farin ciki, ku maƙiyana! Ko da yake na fāɗi, zan tashi. Ko da yake na zauna a cikin duhu, Ubangiji zai zama haskena.

  4. Tare za su zama kamar mutane masu ƙarfi suna tattake lakar tituna a cikin yaƙi. Domin Ubangiji yana tare da su, za su yi faɗa su kuma yi nasara a kan masu yaƙi a kan dawakai.

  5. Gama na zo ne in sa, “ ‘gāba tsakanin mutum da mahaifinsa, ’ya da mahaifiyarta, matar ɗa da surukarta,

  6. abokan gāban mutum, za su zama mutanen gidansa ne.’

  7. “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”

  8. amma ina ganin wata doka tana aiki a gaɓoɓin jikina, tana yaƙi da dokar hankalina, tana kuma sa in zama ɗaurarren dokar zunubin da take aiki a gaɓoɓin jikina.

  9. Kaitona! Wane ne zai cece ni daga wannan jiki mai mutuwa?

  10. Godiya ga Allah ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu! Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi.

  11. A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu.

  12. Dare fa ya kusan ƙarewa; gari kuma yana gab da wayewa. Saboda haka bari mu kawar da ayyukan duhu mu kuma yafa kayan yaƙi na haske.

  13. Allah na salama zai tattake Shaiɗan ba da daɗewa ba yă kuma sa shi a ƙarƙashin sawunku. Alherin Ubangijinmu Yesu kuma yă kasance tare da ku.

  14. Duk ’yan wasan gasa sukan hori kansu sosai. Sukan yi haka domin su sami rawanin da ba zai daɗe ba. Amma mu muna yi ne domin mu sami rawanin da zai dawwama.

  15. To, ni fa ba gudu nake yi kamar mai gudu ba wurin zuwa ba. Dambena kuma ba naushin iska nake yi ba.

  16. A’a, ina horon jikina in mai da shi bawana, saboda bayan na yi wa waɗansu wa’azi, ni kaina kada in kāsa cancantar samun lada.

  17. Abokin gāba na ƙarshen da za a hallaka kuwa, shi ne mutuwa.

  18. Gama ya “sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” To, da aka ce an sa “kome” a ƙarƙashinsa, a fili yake cewa ba a haɗa da Allah a ciki ba, shi wannan da ya sa kome a ƙarƙashin Kiristi.

  19. Sa’ad da mai ruɓan nan ya maye marar ruɓan nan, mai mutuwa kuma ya maye marar mutuwan nan, sa’an nan ne karin maganar da yake a rubuce zai zama gaskiya cewa, “An haɗiye mutuwa cikin nasara.”

  20. “Ya ke mutuwa, ina nasararki? Ya ke mutuwa, ina dafinki?”

  21. Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.

  22. Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi.

  23. don kada Shaiɗan yă rinjaye mu. Da yake muna sane da dabarunsa.

  24. Amma godiya ga Allah, wanda kullum yake bi da mu da nasara cikin Kiristi, kuma ta wurinmu, yana baza ƙanshin nan na sanin Kiristi a ko’ina.

  25. da cikin magana mai gaskiya, da kuma cikin ikon Allah. Muna riƙe da makaman adalci dama da hagu,