Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Warfare of Saints: With prayer

4 ayoyi · 73 fannoni

Ayoyi game da With prayer

  1. Ta Dawuda. Yi hamayya, ya Ubangiji, da waɗanda suke hamayya da ni; yi faɗa da waɗanda suke faɗa da ni.

  2. Ka ɗauki garkuwa da kuma makami; ka tashi ka taimake ni.

  3. Ka ɗaga māshi da kuma abin da ake jefa a kan waɗanda suke fafarata. Ka ce wa raina, “Ni ne cetonka.”

  4. A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a.