Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Warfare of Saints

107 ayoyi · 73 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Zan kuma sa ƙiyayya tsakaninka da macen, tsakanin zuriyarka da zuriyarta. Zai ragargaje kanka, kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”

  2. Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarki yă kuma ba ka gudummawa daga Sihiyona.

  3. Ta Dawuda. Ubangiji ne haskena da cetona, wa zan ji tsoro? Ubangiji ne mafakar raina, wane ne zan ji tsoro?

  4. Sa’ad da mugaye suka tasar mini don su cinye ni, sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari, sun yi tuntuɓe suka fāɗi.

  5. Ko da yake mayaƙa sun kewaye ni, zuciyata ba za tă ji tsoro ba; ko da yake ya ɓarke a kaina, duk da haka zan ƙarfafa.

  6. Ka dogara ga Ubangiji, ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya ka kuma dogara ga Ubangiji.

  7. Ta Dawuda. Yi hamayya, ya Ubangiji, da waɗanda suke hamayya da ni; yi faɗa da waɗanda suke faɗa da ni.

  8. Ka ɗauki garkuwa da kuma makami; ka tashi ka taimake ni.

  9. Ka ɗaga māshi da kuma abin da ake jefa a kan waɗanda suke fafarata. Ka ce wa raina, “Ni ne cetonka.”

  10. Da yawa ne masu gāba da ni da ƙarfi; waɗanda suke kina ba dalili sun yi yawa.

  11. Masu ɓata sunana suna bina dukan yini; da yawa suna kai mini hari cikin fariyarsu.

  12. Duba yadda suka kwanta suna jirana! Mugaye suna ƙulle-ƙullen gāba da ni ba saboda wani dalili ko na yi wa wani zunubi ba, ya Ubangiji.

  13. Amma ga waɗanda suke tsoronka, ka ɗaga tuta don a buɗe gāba da baka. Sela

  14. An ture ni baya na kusa fāɗuwa, amma Ubangiji ya taimake ni.

  15. Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mai fansana mai ƙarfi, wanda yake garkuwoyin kaina a ranar yaƙi.

  16. Kowane takalmin jarumin da aka yi amfani da shi a yaƙi da kuma kowane rigar da ka naɗe cikin jini zai kasance an ƙone shi zai kuma zama abin hura wuta.

  17. zai haɗiye mutuwa har abada. Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye daga dukan fuskoki; zai kawar da kunyar mutanensa daga dukan duniya. Ubangiji ne ya faɗa.

  18. Amma matattunka za su rayu; jikunansu za su tashi. Ku da kuke zama a ƙura, ku farka ku kuma yi sowa don farin ciki. Raɓarka kamar raɓar safiya ce; duniya za tă haifi matattunta.

  19. Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai; kada ka karai, gama ni ne Allahnka. Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka; zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.

  20. “Duk wanda ya yi fushi da kai tabbatacce zai sha kunya da ƙasƙanci; waɗanda suka yi hamayya da kai za su zama kamar ba kome ba su kuma hallaka.

  21. Ko ka nemi abokan gābanka, ba za ka same su ba. Waɗanda suke yaƙi da kai za su zama kamar ba kome ba.

  22. Gama ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya riƙe ka da hannun damana ya kuma ce maka, Kada ka ji tsoro; zan taimake ka.

  23. Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub marar ƙarfi, ya ƙaramin Isra’ila, gama ni kaina zan taimake ka,” in ji Ubangiji, Mai Fansarka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

  24. “Ni kaɗai ne na ta’azantar da ku. Wane ne ku da kuke tsoron mutane masu mutuwa, ’ya’yan mutane waɗanda suke ciyawa ne kawai,

  25. “Sun tanƙwasa harshensu kamar baka, don su harba ƙarya; ba da gaskiya ba ne suke nasara a cikin ƙasar. Sukan tashi daga wannan zunubi zuwa wancan; ba su san ni ba,” in ji Ubangiji.